Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 54

Sarkin Ƙarfi

Sarkin Ƙarfi

KA SAN sunan mutumin da ya fi kowa ƙarfi da ya taɓa rayuwa? Alƙali ne mai suna Samson. Jehobah ne ya ba Samson ƙarfin da yake da shi. Kafin a haifi Samson ma, Jehobah ya gaya wa mamarsa: ‘Ba da daɗewa ba za ki haifi ɗa. Zai yi ja-gora wajen ceton Isra’ila daga Filistiyawa.’

Filistiyawa miyagun mutane ne da suke da zama a ƙasar Kan’ana. Suna da sojoji da yawa, kuma sun zalunci Isra’ilawa. Wata rana da Samson yana tafiya zuwa inda Filistiyawan suke, zaki ya fito yana ruri zai kama shi. Amma Samson ya kashe zakin da hannunsa. Kuma ya kashe miyagun Filistiyawa ɗarurruwa.

Daga baya Samson ya soma ƙaunar wata mace mai suna Delilah. Dukan shugabannin Filistiyawa suka yi wa Delilah alkawarin cewa za su ba ta azurfa 1,100 idan ta gaya musu abin da yake ba wa Samson ƙarfi. Delilah tana son dukan wannan kuɗin. Ba abokiyar kirki ba ce ga Samson, ko kuma mutanen Allah. Sai ta riƙa tambayar Samson abin da yake ba shi ƙarfi.

A ƙarshe, Delilah ta sa Samson ya gaya mata asirin ƙarfinsa. Ya ce: ‘Ba a taɓa aske mini gashi ba. Tun daga lokacin da aka haife ni Allah ya zaɓe ni in zama bawansa na musamman da ake kira Naziri. Idan aka aske mini gashi, ƙarfi na zai ƙare.’

To, da Delilah ta ji haka, ta sa Samson ya yi barci a kan cinyarta. Sai ta kira wani mutum ya shiga ya aske masa gashinsa. Sa’ad da Samson ya farka, ƙarfinsa ya ƙare. Filistiyawa suka shiga suka kama shi. Suka cire masa idanunsa, suka mayar da shi bawansu.

Wata rana Filistiyawa suka yi wani babban liyafa domin su bauta wa allahnsu Dagon, suka fito da Samson daga kurkuku suna yi masa ba’a. A wannan lokaci, gashinsa ya fito. Samson ya gaya wa yaron da yake masa ja-gora: ‘Bari in taɓa ginshiƙan da ke riƙe wannan ginin.’ Sai Samson ya yi addu’a ga Jehobah domin ya ba shi ƙarfi, kuma ya riƙe ginshiƙan. Ya yi kururuwa: ‘Bari in mutu tare da Filistiyawa.’ Filistiyawa wajen 3000 suka taru a wajen bikin, da Samson ya ture ginshiƙan ginin sai ginin ya rushe ya kashe duka miyagun mutanen.

Alƙalawa sura 13 zuwa 16.