Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 57

Allah Ya Zaɓi Dauda

Allah Ya Zaɓi Dauda

KA GA abin da ya faru? Yaron nan ya ceci wannan ɗan rago daga dabbar daji. Dabbar dajin ta zo ta kama wannan ɗan ragon za ta je ta cinye shi. Amma yaron ya bi ta ya ceci ɗan ragon daga bakinta. Da dabbar ta taso masa ya kama ta ya kashe ta! A wani lokaci kuma ya ceci ɗaya daga cikin tumakin daga hannun zaki. Yaro ne marar tsoro. Ka san ko wanene wannan yaron?

Wannan Dauda ne yana yaro. Yana zama a garin Bethlehem. Obed ne kakansa, ɗan Ruth da Boaz. Ka tuna da su? Kuma sunan baban Dauda Jesse. Dauda yana kiwon tumakin babansa. An haifi Dauda shekara 10 bayan Jehobah ya zaɓi Saul ya zama sarki.

Lokaci ya yi da Jehobah ya ce wa Sama’ila: ‘Ka ɗauki mai na musamman ka je gidan Jesse a Bethlehem. Na zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa ya zama sarki.’ Da Sama’ila ya ga ɗan farin Jesse mai suna Eliab, ya ce wa kansa: ‘Hakika wannan ne Jehobah ya zaɓa.’ Amma Jehobah ya gaya masa: ‘Kada ka dubi yadda yake da tsawo ko kuma kyau. Ban zaɓe shi ya zama sarki ba.’

Sai Jesse ya kira ɗansa Abinadab ya kai sa wurin Sama’ila. Amma Sama’ila ya ce: ‘A’a, Jehobah bai zaɓe shi ba.’ Sai Jesse ya kai ɗan sa Shammah. Sama’ila ya ce: ‘A’a, Jehobah bai zaɓe shi ba.’ . Jesse ya kawo ’ya’yansa maza bakwai ga Sama’ila, amma Jehobah bai zaɓi ko ɗaya daga cikinsu ba. Sama’ila ya yi tambaya: ‘Su ke nan mazan?’.

Jesse ya ce: ‘Sai dai autansu.’ . ‘Amma ya fita kiwon tumaki.’ Da suka kawo Dauda, Sama’ila ya ga cewa kyakkyawan yaro ne. Jehobah ya ce masa, ‘Shi ne wannan.’ ‘Zuba masa man a kai.’ Haka ne Sama’ila ya yi. Lokaci yana zuwa da Dauda zai zama sarki.

1 Samuila 17:34, 35; 16:1-13.