Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 59

Dalilin Da Ya Sa Dole Dauda Ya Gudu

Dalilin Da Ya Sa Dole Dauda Ya Gudu

BAYAN da Dauda ya kashe Goliath, shugaban sojojin Isra’ila Abner ya kai shi wurin Saul. Saul ya yi farin ciki da Dauda. Ya mai da shi shugaban sojojinsa kuma ya koma da zama gidan sarki.

Daga baya, da sojojin suka dawo daga yaƙi da Filistiyawa, mata suka yi waƙa: Saul ya kashe mana dubbai kuma Dauda nasa dubbai goma.’ Wannan ya sa Saul ya fara kishi, domin an ba Dauda girma fiye da shi. Amma Jonathan ɗan Saul bai yi kishi ba. Yana ƙaunar Dauda sosai, kuma Dauda ma yana ƙaunar Jonathan. Sai suka yi wa juna alkawarin cewa za su kasance abokai ko da yaushe.

Dauda gwani ne wajen kaɗa garaya, kuma Saul yana son waƙar da yake yi. Amma wata rana kishin da Saul yake yi ya sa ya yi mugun abu. Sa’ad da Dauda yake kaɗa garaya, Sau ya jefa masa māshi, ya ce: ‘Zan kafa Dauda da bango!’ Amma Dauda ya kauce, māshi bai same shi ba. Daga baya Saul ya sake jifansa da bai same shi ba. Dauda ya fahimci cewa yanzu dole ne ya mai da hankali.

Ka tuna da alkawarin da Saul ya yi? Ya ce zai ba duk mutumin da ya kashe Goliath ’yarsa ya aura . A ƙarshe Saul ya gaya wa Dauda zai ba shi ’yarsa Michal, amma sai ya kashe abokan gabansu Filistiyawa 100. Ka yi tunanin wannan! Saul yana so ne Filistiyawa su kashe Dauda. Amma ba su kashe shi ba saboda haka Saul ya aura wa Dauda ’yarsa.

Wata rana Saul ya gaya wa Jonathan da kuma dukan bayinsa cewa yana so ya kashe Dauda. Amma Jonathan ya gaya wa babansa: ‘Kada ka taɓa Dauda. Bai taɓa yi maka laifi ba. Maimakon haka, dukan abin da ya yi babban taimako ne a gareka. Ya ɗauki kasada sa’ad da ya kashe Goliath, kuma sa’ad da ka ga haka, ka yi farin ciki.’

Saul ya saurari ɗansa kuma ya yi alkawari cewa ba zai taɓa Dauda ba. Aka mai da Dauda gidan sarki, kuma ya je yana yi wa Saul hidima kamar dā. Amma wata rana, da Dauda yake kiɗa, Saul ya sake jifansa da māshi. Dauda ya kauce, māshin ya caƙi bango. Wannan na uku ke nan! Dauda ya fahimci cewa dole ne ya gudu!

A cikin daren Dauda ya koma gida. Amma Saul ya aiki mutane su kashe shi. Michal ta san abin da babbanta yake so ya yi. Saboda haka, ta gaya wa mijinta: ‘Idan ba ka gudu ba cikin daren nan, washegari kai macacce ne.’ Cikin wannan daren Michal ta taimaki Dauda ya gudu ta taga. Shekara bakwai Dauda yana ɓuya daga wuri zuwa wuri domin kada Saul ya same shi.

1 Samuila 18:1-30; 19:1-18.