Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 62

Masifa A Gidan Dauda

Masifa A Gidan Dauda

BAYAN da Dauda ya fara sarauta a Urushalima, Jehobah ya ba sojojinsa nasarori masu yawa bisa abokan gabansu. Jehobah ya yi alkawari zai ba wa Isra’ilawa ƙasar Kan’ana. Kuma yanzu, da taimakon Jehobah, duka ƙasar da aka yi musu alkawari ta zama nasu.

Dauda sarki ne mai kirki. Kuma yana ƙaunar Jehobah. Abu da ya yi da farko shi ne ya kawo sunduƙin alkawari zuwa Urushalima. Kuma yana so ya gina haikali da zai saka shi a ciki.

Sa’ad da Dauda ya manyanta ya yi mummuna kuskure. Dauda ya sani cewa bai dace ba mutum ya ɗauki abin wani. Amma wata rana da yamma yana bisa bene na fadarsa, ya dubi ƙasa ya ga wata kyakkyawar mace tana wanka. Sunanta Bathsheba, kuma mijinta sojansa ne sunansa Uriah.

Dauda ya yi sha’awar Bathsheba sosai da ya sa aka kawo ta fadarsa. Mijinta kullum yana bakin daga. Dauda ya kwana da ita daga baya ta ga cewa tana da jiki. Dauda ya damu ƙwarai ya aika da saƙo ga shugaban sojojinsa Joab ya tura Uriah gaba a yaƙi inda za a kashe shi. Sa’ad da Uriah ya mutu, Dauda ya auri matarsa Bathsheba.

Jehobah ya yi fushi ƙwarai da Dauda. Sai ya aiki bawansa Nathan ya gaya masa game da zunubinsa. Ka ga Nathan a nan yana yi wa Dauda magana. Dauda ya tuba daga abin da ya yi, saboda haka Jehobah bai kashe shi ba. Amma Jehobah ya ce: ‘Domin ka yi wannan mugun abun, za ka ga masifa da yawa a gidanka.’ Wace masifa ce Dauda ya gani!

Da farko, ɗan Bathsheba ya mutu. Sai kuma ɗan farin Dauda Amnon ya tilasta wa ’yar’uwarsa Tamar ya kwana da ita. Ɗan Dauda Absalom ya yi fushi ƙwarai domin wannan ya kashe Amnon. Daga baya, Absalom ya sami tagomashin mutane da yawa, kuma ya naɗa kansa sarki. A ƙarshe, Dauda ya yi nasara a yaƙinsa da Absalom, wanda aka kashe. Hakika, Dauda ya ga masifa mai yawa.

Tsakanin duka waɗannan, Bathsheba ta haifi ɗa mai suna Sulemanu. Sa’ad da Dauda ya tsufa kuma ba shi da lafiya, ɗansa Adonijah ya yi ƙoƙari ya naɗa kansa Sarki. Sai Dauda ya sa wani firist mai suna Zadok ya zuba mai a kan Sulemanu ya nuna cewa Sulemanu ne zai zama sarki. Ba da daɗewa ba Dauda ya mutu yana da shekara 70 da haihuwa. Ya yi sarauta na shekara 40, amma yanzu Sulemanu ne sarkin Isra’ila.

2 Samuila 11:1-27; 12:1-18; 1 Sarakuna 1:1-48.