Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 63

Sulemanu Sarki Mai Hikima

Sulemanu Sarki Mai Hikima

SULEMANU bai kai shekara ashirin ba ya zama sarki. Yana ƙaunar Jehobah kuma ya bi shawara mai kyau da babansa Dauda ya ba shi. Jehobah ya yi farin ciki da Sulemanu, saboda haka wata rana cikin dare ya yi magana da shi cikin mafarki: ‘Sulemanu, me kake so in ba ka?’

Sai Sulemanu ya amsa ya ce: ‘Jehobah Allahna, ni yaro ne ƙarami kuma ban san yadda ake sarauta ba. Saboda haka ka ba ni hikima in yi sarauta da kyau.’

Jehobah ya yi farin ciki domin abin da Sulemanu ya tambaya. Saboda haka ya ce: ‘Domin ka bukaci hikima ba tsawon rai ba ko arziki, zan ba ka hikima fiye da dukan wani mutumin da ya taɓa rayuwa. Kuma zan ba ka abin da ba ka tambaya ba, arziki da ɗaukaka.’

Ba da daɗewa ba bayan haka wasu mata biyu suka zo wurin Sulemanu da matsala mai wuya. ‘Ni da wannan matar muna zama gida ɗaya,’ ’yar ta yi bayani. ‘Na haifi yaro, bayan kwana biyu ita ma ta haifi yaro. Sai wata rana daddare ɗanta ya mutu. Ina barci sai ta ajiye mini ɗanta macacce ta ɗauki nawa. Sa’ad da na farka na dubi yaron da ya mutu, na ga cewa ba ɗana ba ne.’

Sai ɗaya macen ta ce: ‘A’a! Yaro mai ran shi ne nawa, wanda ya mutu shi ne nata!’ Mace na farko ta amsa: ‘A’a! Yaron da ya mutu shi ne na ki, mai ran nawa ne!’ Haka matan suka yi ta jayayya. Menene Sulemanu zai yi?

Ya aika a kawo takobi, da aka kawo takobin sai ya ce: ‘Ka raba yaro mai ran gida biyu ka ba kowace mace rabi.’

‘A’a! Ainihin mamar yaron ta yi kuka. ‘Don Allah kada ku kashe yaron. Ku ba ta!’ Amma ɗayar macen ta ce: ‘Kada a ba wa kowannenmu; ka raba yaron gida biyu.’

A ƙarshe Sulemanu ya ce: ‘Kada ka kashe yaron! Ka ba mace na farkon. Ita ce ainihin mamar yaron.’ Sulemanu ya san haka domin ainihin mamar tana ƙaunar yaron sosai saboda haka ta yarda a ba da shi ga wata mace saboda kada a kashe shi. Da mutanen suka ji yadda Sulemanu ya warware matsalar suka yi farin cikin samun sarki mai hikima.

A lokacin sarautar Sulemanu, Allah ya albarkaci mutanen ta wajen sa ƙasa ta ba da amfani na alkama da sha’ir, inabi da ’ya’yan ɓaure da kuma wasu ire-irin abinci. Mutane suka saka kyawawan tufafi suka kuma gina kyawawan gidaje. Kowa ya sami isassun kyawawan abubuwa.

1 Sarakuna 3:3-28; 4:29-34.