Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 65

An Raba Mulkin

An Raba Mulkin

KA SAN abin da ya sa wannan mutumin yake yayyaga rigarsa? Jehobah ne ya gaya masa ya yi haka. Wannan mutumin annabin Allah ne Ahijah. Ka san ko wanene annabi? Annabi mutum ne wanda Allah yake gaya masa abin da zai faru kafin ya faru.

A nan Ahijah yana yin magana da Jeroboam. Jeroboam mutum ne wanda Sulemanu ya ba shi shugabancin wasu ayyukan gininsa. Sa’ad da Ahijah ya sadu da Jeroboam a kan hanya, Ahijah ya yi wani abin mamaki. Ya tuɓe sabuwar rigar da take jikinsa ya yayyaga ta gida 12. Ya gaya wa Jeroboam: ‘Ka ɗauki 10.’ Ka san abin da ya sa Ahijah ya ba wa Jehoboam kashi 10?

Ahijah ya yi masa bayani cewa Jehobah zai ƙwace mulkin daga hannun Sulemanu. Ya ce Jehobah zai ba Jeroboam ƙabilu goma. Wannan ya nuna cewa ƙabilu biyu ne kawai za su rage wa ɗan Sulemanu Rehoboam.

Da Sulemanu ya ji abin da Ahijah ya gaya wa Jeroboam sai ya yi fushi sosai. Ya yi ƙoƙari ya kashe Jeroboam. Amma Jeroboam ya gudu zuwa ƙasar Masar. Bayan ɗan lokaci Sulemanu ya mutu. Ya yi sarauta na shekara 40, aka naɗa ɗansa Rehoboam ya zama sarki. A can ƙasar Masar, Jeroboam ya sami labarin cewa Sulemanu ya mutu, sai ya koma Isra’ila.

Rehoboam ba sarkin kirki ba ne. Ya zalunci mutane fiye da yadda babansa Sulemanu ya yi. Jeroboam da wasu manyan mutane suka je wajen Sarki Rehoboam suka roƙe shi ya kyautata wa mutanen. Amma Rehoboam ya ƙi ya saurare su. Maimakon haka, sai ya daɗa musu azaba fiye da dā. Saboda haka mutanen suka naɗa Jeroboam ya zama sarkin ƙabilu goma, amma ƙabilu biyu na Benjamin da na Judah suka riƙe Rehoboam ya zama sarkinsu.

Jeroboam ba ya son mutanensa su tafi Urushalima su bauta wa Jehobah. Saboda haka ya kafa gumakan ’yan maraƙi biyu ya sa mutanen masarautar ƙabilu 10 su bauta musu. Ba da daɗewa ba ƙasar ta cika da yin laifi da mugunta.

Akwai matsala kuma a masarautar ƙabilu biyun. Bai kai shekara biyar ba bayan Rehoboam ya zama sarki, sarkin Masar ya zo ya yaƙi Urushalima. Ya kwashi abubuwa masu tamani da yawa daga haikalin Jehobah. Haikalin ya kasance na ɗan lokaci ne kamar yadda aka gina shi.

1 Sarakuna 11:26-43; 12:1-33; 14:21-31.