Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 66

Jezebel, Muguwar Sarauniya

Jezebel, Muguwar Sarauniya

BAYAN mutuwar Sarki Jeroboam , duk wani sarki da ya yi sarautar bisa ƙabilu 10 mugu ne. Sarki Ahab ne ya fi dukansu mugunta. Ka san abin da ya sa? Wani babban dalili shi ne matarsa, muguwar Sarauniya Jezebel ce.

Jezebel ba Ba’isra’iliya ba ce. Ita ’yar sarkin Sidon ce. Tana bauta wa allahn ƙarya Ba’al, kuma ta sa Ahab da kuma Isra’ilawa da yawa suka fara bauta wa Ba’al. Jezebel ba ta son Jehobah kuma ta kashe annabawansa da yawa. Wasu suka fara ɓuya cikin ƙogo domin kada a kashe su. Idan Jezebel tana son abu, tana iya kashe mutum domin ta samu abin da take so.

Wata rana Sarki Ahab ya yi baƙin ciki. Sai Jezebel ta tambaye shi: ‘Me ya sa kake baƙin ciki haka?’

‘Domin abin da Naboth ya gaya mini,’ Ahab ya amsa mata. ‘Ina so in sayi gonarsa. Amma ya ce mini ba zai sayar mini ba.’

Jezebel ta ce: ‘Kada ka damu,’ . ‘Zan samo maka.’

Sai Jezebel ta rubuta wasiƙa zuwa ga wasu manyan mutane a cikin birni da wannan mutumin Naboth yake da zama. Ta gaya musu ‘Ku sami wasu mutanen banza su ce Naboth ya zagi Allah da kuma Sarki.’ ‘Sai su fita da Naboth bayan gari su jefe shi su kashe shi.’

Da Jezebel ta sami labarin cewa Naboth ya mutu, sai ta ce wa Ahab: ‘Ka tafi ka karɓi gonarsa.’ Kana ganin bai kamata a yi wa Jezebel horo domin wannan mugun abin da ta yi ba?

Saboda haka daga baya Jehobah ya aiki Jehu ya yi mata horo. Sa’ad da Jezebel ta ji cewa Jehu yana zuwa, ta saka tozali ta yi ƙwalliya domin ta yi kyau. Amma da Jehu ya isa ya ga Jezebel a taga, ya ce wa mutanen da suke fada: ‘Ku jefo ta!’ Mutanen suka yi biyayya kamar yadda kake gani a wannan hoton. Suka jefa ta ƙasa, ta faɗi ta mutu. Haka muguwar Sarauniya Jezebel ta ƙarasa.

1 Sarakuna 16:29-33; 18:1-4; 21:1-16; 2 Sarakuna 9:30-37.