Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 67

Jehoshaphat Ya Dogara Ga Jehobah

Jehoshaphat Ya Dogara Ga Jehobah

KA SAN ko su wanene waɗannan mutane da kuma abin da suke yi? Yaƙi za su je, kuma mutanen da suke gaba suna waƙa. Wataƙila ka yi tambaya: ‘Me ya sa mawaƙan ba su da takubba da masu da za su yi yaƙi da su?’ Bari mu ga abin da ya sa.

Jehoshaphat sarki ne na masarautar ƙabilu biyu na Isra’ila. Ya yi rayuwa a zamani ɗaya da Ahab da Jezebel na masarautar ƙabilu goma. Amma Jehoshaphat sarkin kirki ne, kuma babansa Asa ma sarkin kirki ne. Domin haka mutanen ƙabilu biyu na masarautar kudu sun more rayuwa mai kyau.

Amma yanzu wani abu ya faru da ya tsorata mutanen. ’Yan saƙo, sun ba wa Jehoshaphat rahoto cewa: ‘Sojoji masu yawa daga ƙasashen Moab da Ammon da Dutse Seir suna zuwa su kawo maka hari.’ Isra’ilawa da yawa suntaru a Urushalima domin su roƙi taimakon Jehobah. Suka je haikali, a nan Jehoshaphat ya yi addu’a: ‘Ya Jehobah Allahnmu, ba mu san abin da za mu yi ba. Ba mu da ƙarfi a gaban waɗannan sojoji masu yawa. Muna bukatar taimakonka.’

Jehobah ya saurara, ya sa ɗaya daga cikin bayinsa ya gaya wa mutanen cewa: ‘Yaƙin ba naku ba ne, na Allah ne. Ba za ku yi yaƙi ba. Ku tsaya kawai ku yi kallo, ku ga yadda Jehobah zai cece ku.’

Washegari Jehoshaphat ya gaya wa mutanen: ‘Ku dogara ga Jehobah!’ Sai ya saka mawaƙa a gaban sojojinsa, da suke tafiya suna waƙa ga Jehobah. Ka san abin da ya faru sa’ad da suka yi kusa da bakin daga? Jehobah ya sa sojojin abokan gabansu suka fara yaƙi da junansu. Kuma sa’ad da Isra’ilawa suka isa wurin, dukan sojojin abokan gabansu sun mutu!

Shin Jehoshaphat ba mai hikima ba ne da ya dogara ga Jehobah? Za mu kasance masu hikima idan muka dogara a gare shi.

1 Sarakuna 22:41-53; 2 Labarbaru 20:1-30.