Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 69

Yarinya Ta Taimaki Jarumi

Yarinya Ta Taimaki Jarumi

KA SAN abin da wannan yarinyar take faɗa? Tana gaya wa wannan matar game da Elisha ne da kuma abubuwan ban al’ajabi da Jehobah yake taimakonsa ya yi. Matar ba ta san Jehobah ba domin ita ba Ba’isra’iliya ba ce. Bari mu ga abin da ya sa yarinyar take gidan matar.

Matar Basuriya ce. Mijinta sunansa Na’aman, shugaban sojojin Suriya. Suriyawa suka kama wannan ƙaramar yarinya kuma suka kawo ta wurin matar Na’aman domin ta zama baiwarta.

Na’aman yana da mugun cuta da ake kira kuturta. Wannan cutar tana cin jikin mutane. Ga abin da yarinyar take gaya wa matar Na’aman: ‘Da a ce Ubangijina ya je wajen annabin Jehobah a Isra’ila. Zai warkar masa da wannan cutar.’ Daga baya aka gaya wa mijin matar.

Na’aman yana so ya warke; saboda haka ya shawarta ya tafi Isra’ila. Da ya isa can, ya tafi gidan Elisha. Elisha ya aiki bawansa ya gaya wa Na’aman ya je ya yi wanka cikin Kogin Urdun sau bakwai. Wannan ya sa Na’aman ya yi fushi sosai, ya ce: ‘Kogunan garinmu sun fi na Isra’ila!’ Bayan ya faɗi haka sai Na’aman ya tafi.

Amma ɗaya daga cikin bayinsa ya gaya masa: ‘Ubangiji, da a ce Elisha ya gaya maka ka yi wani abu mai wuya, da ka yi. Me ya sa ba za ka yi wanka ba kamar yadda ya ce?’ Na’aman ya saurari bawansa kuma ya je ya nitse cikin Kogin Urdun sau bakwai. Da ya gama jikinsa ya sami lafiya!

Na’aman ya yi farin ciki sosai. Ya koma wurin Elisha ya ce masa: ‘Yanzu na tabbata cewa Allahn da yake Isra’ila shi ne Allah na gaskiya a dukan duniya. Saboda haka, don Allah ka karɓi wannan kyauta daga gare ni.’ Amma Elisha ya amsa: ‘A’a, ba zan karɓa ba.’ Elisha ya sani cewa ba daidai ba ne ya karɓi kyautar, domin Jehobah ne ya warkar da Na’aman. Amma bawan Elisha Gehazi yana son kyautar.

Saboda haka ga abin da Gehazi ya yi: Bayan da Na’aman ya tafi, Gehazi ya bi shi ya sha kansa. ‘Elisha ya gaya mini in gaya maka cewa yana bukatar wasu daga cikin kyautar domin abokansa sun zo yanzu yanzun nan su ziyarce shi, In ji Gehazi. Amma ƙarya yake yi. Amma Na’aman bai san cewa ƙarya ba ne: saboda haka ya ba Gehazi wasu cikin abubuwan.

Sa’ad da Gehazi ya koma gida, Elisha ya san abin da ya yi. Jehobah ya gaya masa. Saboda haka ya ce: ‘Domin ka yi wannan mugun abu, kuturtar Na’aman za ta dawo kanka.’ Kuma ba da ɓata lokaci ba ta koma kansa!

Menene za mu koya daga wannan? Na farko, ya kamata mu zama kamar yarinyar mu riƙa magana game da Jehobah. Zai yi amfani da yawa. Na biyu, kada mu zama masu fahariya kamar yadda Na’aman ya yi da farko, amma mu yi wa bayin Allah biyayya. Na uku, kada mu yi ƙarya kamar yadda Gehazi ya yi. Za mu koyi abubuwa da yawa daga karatun Littafi Mai Tsarki.

2 Sarakuna 5:1-27.