Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 73

Sarkin Kirki Na Ƙarshe A Isra’ila

Sarkin Kirki Na Ƙarshe A Isra’ila

JOSIAH yana ɗan shekara takwas ya zama sarkin ƙabilu biyu na Isra’ila. Ya yi ƙarami sosai ya zama sarki. Da farko wasu manya suka taimake shi wajen sarautar ƙasar.

Sa’ad da Josiah ya yi sarauta na shekara bakwai ya fara neman Jehobah. Ya bi misalin sarakunan kirki kamar su Dauda, Jehoshaphat da Hezekiah. Har ila sa’ad da yake saurayi Josiah ya nuna bajinta.

Da yawa cikin Isra’ila sun daɗe suna aika mugunta. Suna bauta wa allolin ƙarya. Suna yi wa gumaka sujada. Saboda haka Josiah ya fita da mutane suka fara kawar da allolin ƙarya daga ƙasar. Wannan babban aiki ne domin mutane da yawa suna bauta wa allolin ƙarya. Ga Josiah nan da mutanensa suna farfasa gumaka.

Bayan haka, Josiah ya ba wa mutane uku aikin kula da gyaran haikalin Jehobah. Ana karɓan kuɗi daga mutane ana ba waɗannan mutane uku domin su biya kuɗin ayyuka da za a yi. Sa’ad da suke gyaran haikalin babban firist Hilkiah ya sami wani abu mai muhimmanci a nan. Littafin Dokoki ne da Jehobah ya sa Musa ya rubuta da daɗewa. Ya ɓata da daɗewa.

Aka kai wa Josiah littafin, ya ce a karanta ya saurara. Sa’ad da yake saurara ya ga cewa mutanen ba sa kiyaye dokokin Jehobah. Ya yi baƙin ciki game da wannan, saboda haka ya yaga rigarsa, kamar yadda kake gani a nan. Ya ce: ‘Jehobah ya yi fushi da mu, domin kakanninmu ba su kiyaye dokokin da suke rubuce ba a wannan littafin.’

Josiah ya umurci babban firist Hilkiah ya bincika ya gani menene Jehobah zai yi musu. Hilkiah ya tafi wajen wata mace mai suna Huldah, ita annabiya ce, ya tambaye ta. Ta ba shi wannan saƙon daga Jehobah ya gaya wa Josiah: ‘Urushalima da dukan mutanenta za a hukunta su domin sun bauta wa allolin ƙarya kuma ƙasar ta cika da mugunta. Amma domin kai Josiah ka yi abin kirki wannan hukunci ba zai zo ba har sai bayan ka mutu.’

2 Labarbaru 34:1-28.