Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 74

Mutumin Da Ba Ya Tsoro

Mutumin Da Ba Ya Tsoro

DUBI waɗannan mutane suna yi wa wannan saurayin ba’a. Ka san ko wanene shi? Wannan Irmiya ne. Annabin Allah ne na musamman.

Ba da daɗewa ba bayan Sarki Josiah ya fara halaka gumaka a ƙasar, Jehobah ya gaya wa Irmiya ya zama annabinsa. Amma Irmiya yana ganin cewa shi yaro ne ba zai iya zama annabi ba. Amma Jehobah ya gaya masa cewa zai taimake shi.

Irmiya ya gaya wa Isra’ila su daina yin miyagun abubuwa. Ya ce: ‘Allolin da mutanen al’ummai suka bauta wa allolin ƙarya ne.’ Amma Isra’ilawa da yawa sun gwammace su bauta wa gumaka maimakon Jehobah. Sa’ad da Irmiya ya gaya wa mutane cewa Allah zai yi musu hukunci domin muguntarsu, sai suka yi masa dariya.

Shekaru da yawa suka shige. Josiah ya mutu, kuma bayan watanni uku ɗansa Jehoiakim ya zama sarki. Irmiya ya ci gaba da gaya wa mutanen cewa: ‘Za a halaka Urushalima idan ba su daina miyagun halayensu ba.’ Firist ya kama Irmiya ya yi ihu: ‘Ya kamata a kashe ka domin ka faɗi wannan abin.’ Sai suka faɗa wa shugabanni Isra’ila: ‘Ya kamata a kashe Irmiya domin yana mugun magana game da birninmu.’

Menene Irmiya zai yi yanzu? Bai ji tsoro ba! Ya gaya musu duka: ‘Jehobah ya aiko ni in faɗa muku waɗannan abubuwa. Idan ba ku daina miyagun halayenku ba, Jehobah zai halaka Urushalima. Amma ku tabbata: Idan kuka kashe ni za ku kashe mutum ne da bai yi laifi ba.’

Shugabannin ba su kashe Irmiya ba, amma Isra’ilawan ba su sake miyagun halayensu ba. Daga baya Nebuchadnezzar sarkin Babila ya zo ya yaƙi Urushalima. A ƙarshe, Nebuchadnezzar ya mai da Isra’ilawa suka zama bayinsa. Ya kwashi dubbai zuwa Babila. Ka yi tunanin yadda zai kasance mutanen da ba ka sani ba su ɗauke ka zuwa wata ƙasar da ba ka sani ba!

Irmiya 1:1-8; 10:1-5; 26:1-16; 2 Sarakuna 24:1-17.