Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 75

Yara Huɗu A Babila

Yara Huɗu A Babila

SARKI Nebuchadnezzar ya kwashi dukan Isra’ilawa masu ilimi zuwa Babila. Daga baya sarkin ya zaɓi kyawawan samari masu basira a tsakaninsu. Huɗu daga cikin waɗannan su ne kake gani a nan. Ɗayan nan Daniel ne, saura ukun kuma Babiloniyawa suna kiransu Shadrach, Meshach da Abednego.

Nebuchadnezzar ya shirya ya koyar da waɗannan samari domin su yi hidima a fadarsa. Bayan koyarwa ta shekara uku zai zaɓi waɗanda suka fi basira domin warware matsala. Sarkin yana so yaran su kasance masu ƙarfi masu lafiya sa’ad da ake koyar da su. Saboda haka ya ba da umurni cewa bayinsa su ba su abinci mai kyau da giya a cikin wanda shi da iyalinsa suke ci da sha.

Dubi saurayi Daniel. Ka san abin da yake gaya wa babban bawan Nebuchadnezzar Ashpenaz? Daniel yana gaya masa cewa ba ya so ya ci abinci mai kyau na gidan sarki. Amma Ashpenaz ya damu. ‘Sarki ya riga ya ba da abin da za ku ci ku sha,’ ya ce. ‘Kuma idan ba ku kasance da koshin lafiya ba kamar sauran yaran zai kashe ni.’

Saboda haka Daniel ya tafi wajen wanda Ashpenaz ya saka su a hannunsa. Ya ce: “Don Allah ka gwada mu ka gani na kwana 10. Ka ba mu mabunƙusa ƙasa mu ci da kuma ruwa mu sha. Sa’an nan ka gwada mu da yaran da suke cin abincin sarki ka ga waye suka fi ƙoshi.’

Mai kula da su ya yarda ya yi haka. Da kwanaki 10 suka cika, Daniel da abokanansa uku suka fi dukan sauran yaran ƙoshi. Saboda haka mai kula da su ya ƙyale su suka ci gaba da cikin mabunƙusa ƙasa maimakon abincin da sarki ya yi masu tanadi.

Bayan shekara uku aka kai dukan yaran ga Nebuchadnezzar. Bayan ya dube su duka, sarki ya ga cewa Daniel da abokanansa uku suka fi basira. Saboda haka ya ɗauke su su taimake shi a fada. Kuma dukan lokaci da sarki ya yi wa Daniel, Shadrach, da Meshach da Abednego tambaya ko kuma ya ba su wata matsala mai wuya su warware, suna nuna fahimi da ya ninka na firistocinsa da masu basiransa sau 10.

Daniel 1:1-21.