Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 76

An Halaka Urushalima

An Halaka Urushalima

FIYE da shekara 10 ya shige tun da Nebuchadnezzar ya kwashi Isra’ilawa masu ilimi zuwa Babila. Kuma yanzu dubi abin da yake faruwa! Yana ƙona Urushalima. Kuma Isra’ilawa da ba a kashe ba an kwashe su zuwa Urushalima.

Ka tuna abin da annabawan Jehobah ya gaya wa mutane ke nan zai same su idan ba su sake miyagun halayensu ba. Amma Isra’ilawan ba su saurari annabin ba. Suka ci gaba da bauta wa allolin ƙarya maimakon Jehobah. Saboda haka mutane sun cancanci a yi musu hukunci. Mun san wannan domin annabin Allah Ezekiel ya gaya mana game da miyagun abubuwa da Isra’ilawan suke yi.

Ka san ko wanene Ezekiel? Yana ɗaya daga cikin samarin da Sarki Nebuchadnezzar ya kwasa zuwa Babila shakaru 10 kafin a halaka Urushalima. Daniel da abokanansa uku, Shadrach, Meshach da kuma Abednego, su ma an kwashe su zuwa Babila a lokaci guda.

Sa’ad da Ezekiel yana Babila, Jehobah ya nuna masa miyagun abubuwa da suke faruwa a haikali a Urushalima. Jehobah ya yi haka ne ta wajen mu’ujiza. Ezekiel yana Babila, amma Jehobah ya sa ya ga dukan abubuwa da suke faruwa a haikali. Kuma abin da Ezekiel ya gani abin mamaki ne!

‘Dubi abin ƙyama da mutanen suke yi a cikin haikali,’ Jehobah ya gaya wa Ezekiel. ‘Dubi sun rufe bango da hoton macizai da wasu dabbobi. Kuma dubi Isra’ilawan suna bauta masu!’ Ezekiel yana ganin waɗannan abubuwa kuma ya rubuta abubuwan da suke faruwa.

Jehobah ya tambayi Ezekiel: ‘Ka ga abin da shugabannin Isra’ilawa suke yi a ɓoye?’ Hakika, ya ga wannan ma. Da mutane 70 kuma dukansu suna bauta wa allolin ƙarya. Suna cewa: ‘Jehobah ba ya ganinmu. Ya riga ya bar ƙasar.’

Sai kuma Jehobah ya nuna wa Ezekiel wasu mata a ƙofar arewa ta haikali. Suna zaune a wurin suna bauta wa allahn ƙarya Tam’muz. Ka kuma dubi waɗannan mutane a ƙofar haikali! Su wajen 25. Ezekiel ya gan su. Suna rusuna wa ga gabas suna bauta wa rana!

Jehobah ya ce: ‘Waɗannan mutane ba su daraja ni ba. Ba miyagun abubuwa kawai suke yi ba, amma har cikin haikali na suke zuwa su yi su!’ Saboda haka, Jehobah ya yi alkawari: ‘Za su ga fushi na. Kuma ba zan ji tausayinsu ba sa’ad da ake halaka su.’

Shekara uku kawai bayan Jehobah ya nuna wa Ezekiel waɗannan abubuwa Isra’ilawa suka yi wa Sarki Nebuchadnezzar tawaye. Saboda haka ya je ya yaƙe su. Bayan kamar shekara ɗaya da rabi Babiloniyawa suka fasa ganuwar Urushalima suka ƙona birnin kurmus. Yawancin mutanen aka kashe su ko kuma aka kwashe su zuwa bauta a Babila.

Me ya sa Jehobah ya ƙyale wannan halaka ta sami Isra’ilawa? Hakika, domin ba su saurari Jehobah ba kuma ba su yi wa dokokinsa biyayya ba. Wannan ya nuna yadda yake da muhimmanci mu yi abin da Allah ya ce.

Da farko an ƙyale mutane kaɗan su zauna a ƙasar Isra’ila. Sarki Nebuchadnezzar ya ɗaura wa wani Bayahude mai suna Gediliah aikin kula da mutanen. Wasu Isra’ilawa suka kashe Gedaliah. Mutanen suka ji tsoro cewa Babiloniyawa za su zo su halaka su duka domin wannan mugun abin da ya faru. Suka tilasta wa Irmiya ya bi su, suka gudu zuwa ƙasar Masar.

Wannan ya sa babu kowa a ƙasar Isra’ila. Shekara 70 babu wanda ya zauna a ƙasar. Ɗungum babu kowa. Amma Jehobah ya yi alkawarin cewa zai dawo da mutanensa zuwa ƙasarsu bayan shekara 70. Amma a yanzu me yake faruwa da mutanen Allah a ƙasar Babila inda aka kai su? Bari mu gani.

2 Sarakuna 25:1-26; Irmiya 29:10; Ezekiel 1:1-3; 8:1-18.