Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 77

Sun Ƙi Yin Sujada

Sun Ƙi Yin Sujada

KA TUNA ka ji game da waɗannan samarin? Hakika, abokan Daniel ne waɗanda suka ƙi cin abincin da bai dace ba gare su. Babiloniyawa suna kiransu, Shadrach, Meshach da Abednego. Amma dube su yanzu. Me ya sa suka ƙi yin sujada ga wannan babban gunki kamar dukan sauran mutanen? Bari mu gani.

Ka tuna da dokokin da Jehobah da kansa ya rubuta da ake kira Dokoki Goma? Na farko ita ce: ‘Kada ku bauta wa wani allah sai ni.’ Waɗannan samari suna yin biyayya ne ga wannan doka ko da yake yin haka ba shi da sauƙi.

Nebuchadnezzar sarkin Babila ya kira mutane masu girma su daraja gunkinsa da ya kafa. Bai daɗe ba da gaya wa mutanen: ‘Idan kun ji karar ƙaho, da garaya da sauran kayakin kiɗa, sai ku yi sujada ku bauta wa wannan gunkin zinariya. Duk wanda bai yi sujada ya yi bauta ba za a jefa shi cikin wuta ba tare da ɓata lokaci ba.’

Sa’ad da Nebuchadnezzar ya ji cewa Shadrach, Meshach da Abednego ba su yi sujada ba, ya yi fushi sosai. Ya sa aka kawo su wurinsa. Ya sake ba su zarafin su yi sujada. Amma samarin suka dogara ga Jehobah. ‘Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu,’ suka gaya wa Nebuchadnezzar. ‘Amma idan ma bai cece mu ba, ba za mu yi sujada ga gunkinka na zinariya ba.’

Da ya ji haka, Nebuchadnezzar ya ƙara yin fushi sosai. Da tanderu a kusa ya ba da umurni: ‘Ku ƙara zafin wutar tanderun ya fi dā sau bakwai!’ Sai ya sa mutane da suka fi ƙarfi a sojojinsa suka ɗaure Shadrach, Meshach da Abednego suka jefa su cikin tanderun. Tanderun ya yi zafi sosai da zafin wutar ya kashe mutane masu ƙarfin. Amma samarin uku da suka jefa ciki fa?

Sarki ya dubi cikin tanderun, tsoro ya kama shi. ‘Ba mutane uku muka ɗaure muka jefa cikin tanderu ba? Ya yi tambaya.

‘Haka yake,’ in ji bayinsa.

‘Amma na ga mutane huɗu suna yawo cikin wuta,’ in ji shi. ‘Ba a ɗaure suke ba, kuma wutar ba ta ƙone su ba. Kuma na huɗun ya yi kama da allah.’ Sarki ya je kusa da ƙofar tanderun ya yi kira: ‘Shadrach! Meshach! Abednego! Ku fito, ku bayin Allah Maɗaukaki!’

Da suka fito kowa ya ga cewa ba abin da ya same su. Sai sarkin ya ce: ‘A yabi Allahn Shadrach, Meshach da Abednego! Ya aiki mala’ikansa ya cece su domin ba su yi sujada sun bauta wa wani allah ba sai Allahnsu.’

Wannan ba misali ba ne mai kyau na aminci ga Jehobah da ya kamata mu bi?

Fitowa 20:3; Daniel 3:1-30.