Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 78

Rubutun Hannu A Bango

Rubutun Hannu A Bango

MENENE yake faruwa a nan? Mutanen nan suna babbar liyafa. Sarkin Babila ya gayyaci manyan baƙi wajen dubu ɗaya. Suna yin amfani da kofinan zinariya da na azurfa da kuma kwanukan da aka kwaso daga haikalin Jehobah a Urushalima. Amma farat ɗaya, yatsar mutum ta bayyana ta fara rubutu a jikin bango. Kowa ya tsorata.

Belshazzar, jikan Nebuchadnezzar shi ne sarki a yanzu. Ya yi ihu a kawo masa masu hikimarsa. ‘Duk wanda zai iya karanta wannan rubutu kuma ya gaya mini ma’anarsa, zan ba shi kyauta kuma zan mai da shi na uku wajen muhimmanci a wannan masarautar,’ in ji sarkin. Amma babu mai hikimar da zai iya karanta wannan rubutu a jikin garu, babu wanda zai iya faɗin ma’anarsa.

Mamar sarkin ta ji surutun da ake yi ta shiga cikin babban ɗakin na cin abinci. ‘Kada ka ji tsoro sosai haka,’ ta gaya wa sarkin. ‘Akwai wani mutum a masarautar ka da ya san alloli masu tsarki. Sa’ad da kakanka Nebuchadnezzar yake sarauta ya naɗa shi shugaban dukan masu hikima. Sunansa Daniel. Ka aika a kira shi, shi zai gaya maka ma’anar dukan wannan.’

Saboda haka ba tare da ɓata lokaci ba aka shigo da Daniel. Bayan ya ƙi ya karɓi kyauta, Daniel ya faɗi abin da ya sa Jehobah ya taɓa cire kakan Belshazzar Nebuchadnezzar daga sarauta. ‘Yana da girman kai sosai,’ in ji Daniel. ‘Shi ya sa Jehobah ya yi masa horo.’

‘Amma kai,’ Daniel ya gaya wa Belshazzar, ‘ka san dukan abin da ya faru da shi, duk da haka ka kasance da girman kai kamar Nebuchadnezzar. Ka kawo kwafuna da kwanukan da aka kwaso daga haikalin Jehobah ka yi amfani da su. Ka yabi allolin da ka yi da itace da duwatsu, amma ba ka daraja Mahaliccinka Mai girma ba. Abin da ya sa ke nan Allah ya aiko da hannu ya rubuta waɗannan kalmomi.

‘Ga abin da aka rubuta,’ in ji Daniel: ‘ME’NE, ME’NE, TE’KEL DA PAR’SIN.’

‘ME’NE yana nufin Allah ya ƙayyade kwanakin sarautarka kuma ya kawo ƙarshensu. TE’KEL yana nufin an auna ka da ma’auni kuma an ga ba ka da kyau. PAR’SIN yana nufin cewa an ba da sarautarka ga mutanen Mediya da Farisa.’

A lokacin da Daniel yake magana ma, ’yan Mediya da Farisa sun riga sun fara kai wa Babila farmaki. Suka ci birnin a yaƙi kuma suka kashe Belshazzar. Abin da aka rubuta a bango ya faru cikin wannan dare! Amma menene zai faru da Isra’ila yanzu? Za mu sani nan ba da daɗewa ba, amma da farko bari mu ga abin da ya faru da Daniel.

Daniel 5:1-31.