Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 80

Mutanen Allah Suna Fitowa Daga Babila

Mutanen Allah Suna Fitowa Daga Babila

KUSAN shekara biyu ta shige tun da mutanen Mediya da Farisa suka kama Babila. Ka dubi abin da yake faruwa a yanzu! Hakika, Isra’ilawa suna fitowa daga Babila. Ta yaya suka sami ’yanci? Waye ya ƙyale su su tafi?

Cyrus ne sarkin Farisa. Da daɗewa kafin a haifi Cyrus, Jehobah ya sa annabinsa Ishaya ya rubuta game da Cyrus: ‘Za ka yi abin da nake so. Za a bar maka ƙofa a buɗe domin ka kama birnin.’ Kuma Cyrus ya yi ja-gora wajen kama Babila. Mutanen Mediya da Farisa suka shiga cikin birnin ta ƙofar da aka bari a buɗe.

Amma kuma annabin Jehobah Ishaya ya ce Cyrus zai ba da umurnin a sake gina Urushalima da kuma haikalinta. Shin Cyrus ya ba da wannan umurni kuwa? Hakika, ya bayar. Ga abin da Cyrus ya cewa Isra’ilawa: ‘Ku tafi Urushalima kuma ku sake gina haikalin Jehobah, Allahnku.’ Abin da Isra’ilawan suke kan hanyar zuwa yi ke nan.

Amma ba dukan Isra’ilawa ba ne za su iya yin doguwar tafiyar zuwa Urushalima ba. Doguwar tafiya ce ta kusan mil 500 kuma da yawa sun tsufa ko kuma ba su da lafiya saboda haka ba za su iya tafiya mai nisa ba. Akwai kuma wasu dalilai da ya sa wasu mutane ba su tafi ba. Amma Cyrus ya gaya wa waɗanda ba za su iya zuwa ba: ‘Ku ba da zinariya da azurfa da kuma wasu kyauta ga mutanen da za su tafi su gina Urushalima da haikalinta.’

Saboda haka, aka ba da kyauta mai yawa ga waɗanda suke kan hanyarsu ta zuwa Urushalima. Kuma Cyrus ya ba su kwanuka da kofina da Nebuchadnezzar ya kwashe daga haikalin Jehobah sa’ad da ya halaka Urushalima. Mutane suka sami kayayyaki da yawa da za su kwashe zuwa Urushalima.

Bayan sun yi kamar wata huɗu suna tafiya, Isra’ila saka isa Urushalima a kan lokaci. Shekara 70 ke nan daidai da halaka birnin, kuma ƙasar ta kasance babu kowa. Amma ko da yake Isra’ilawa sun koma ƙasarsu za su fuskanci wahala, kamar yadda za mu koya a gaba.

Ishaya 44:28; 45:1-4; Ezra 1:1-11.