Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 81

Dogara Ga Taimakon Allah

Dogara Ga Taimakon Allah

KUSAN mutane 50,000 ne suka yi doguwar tafiya daga Babila zuwa Urushalima. Amma sa’ad da suka isa, Urushalima kango ce kawai. Babu wanda yake zaune a cikin ta. Dole ne Isra’ilawa su sake gina kome.

Ɗaya daga cikin abubuwa na farko da suka gina shi ne bagadi. Wannan wuri ne da za su ba da hadayar dabbobi ga Jehobah. Bayan ’yan watanni Isra’ilawan suka fara gina Haikali. Amma abokan gaba da suke zaune a kusa da su ba sa son Isra’ilawa su yi ginin. Saboda haka suka fara yi musu barazana domin su daina. A ƙarshe, waɗannan abokanan gaba, suka sa sabon sarkin Farisa ya hana yin ginin.

Shekaru suka shige. Yanzu an yi shekara 17 da fitowar Isra’ilawa daga Babila. Jehobah ya aiki annabawansa Haggai da Zechariah su gaya wa mutanen su fara ginin. Mutanen suka dogara ga taimakon Allah, suka yi wa annabawan biyayya. Suka fara ginin kuma, ko da yake doka ta ce kada su yi ginin.

Sai wani ma’aikacin Farisa mai suna Tattenai ya zo ya tambayi Isra’ilawan wa ya ba su izinin su gina haikalin. Isra’ilawan suka gaya masa cewa sa’ad da suke Babila, Sarki Cyrus ya gaya masu: ‘Ku tafi ku gina Urushalima da kuma haikalin Allahnku.’

Tattenai ya aika da wasiƙa zuwa Babila ya yi tambaya ko Cyrus da ya riga ya mutu, da gaske ya faɗi haka. Ba da daɗewa ba ya sami wasiƙa daga wurin sabon sarkin Farisa. Wasiƙar ta ce da gaske Cyrus ya faɗi haka. Saboda haka sarkin ya rubuta: ‘Ka ƙyale Isra’ilawan su gina haikalin Allahnsu. Kuma na umurce ka ka taimake su.’ A cikin shekara huɗu aka gama gina haikalin, Isra’ilawa suka yi farin ciki ƙwarai.

Shekaru da yawa suka shige. Yanzu kusa shekara 48 ne tun da aka gama gina haikalin. Mutanen da suke Urushalima talakawa ne, kuma birnin da kuma haikalin Allah ba su da kyau sosai. A can Babila, Ba’isra’ile Ezra ya sami labari cewa haikalin Allah yana bukatar gyara. Ka san abin da ya yi?

Ezra ya tafi wurin Artaxerxes, sarkin Farisa, kuma wannan sarkin kirkin ya ba wa Ezra kyauta mai yawa ya tafi da su Urushalima. Ezra ya ce wa Isra’ilawa da suke Babila su taimake shi su kwashi waɗannan kyauta zuwa Urushalima. Wajen mutane 6,000 suka ce za su tafi. Suka dauƙi zinariya da azurfa da wasu kayayyaki masu kyau da za su kwashe zuwa Urushalima.

Ezra ya damu domin da miyagun mutane a kan hanya. Waɗannan mutane za su kwace musu zinariya da azurfarsu kuma su kashe su. Saboda haka Ezra ya tara mutanen, kamar yadda kake gani a wannan hoto. Sai suka yi addu’a Jehobah ya kāre su a doguwar tafiyarsu zuwa Urushalima.

Jehobah kuwa ya kāre su. Bayan wata huɗu na tafiya suka isa Urushalima lafiya lau. Wannan bai nuna ba ne cewa Jehobah zai iya kāre waɗanda suka dogara a gare shi?

Ezra sura 2 zuwa 8.