Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 83

Ganuwar Urushalima

Ganuwar Urushalima

KA DUBI aikin da ake yi a nan. Isra’ilawa sun shagala suna gina ganuwar Urushalima. Sa’ad da Nebuchadnezzar ya halaka Urushalima wajen shekara 152 da suka shige, ya rurrushe ganuwar kuma ya ƙone ƙofar garin. Isra’ilawa ba su gina ganuwar ba sa’ad da suka komo daga Babila.

Yaya kake tsammani mutanen suka ji a dukan waɗannan shekaru da suke zaune a birnin da ba shi da ganuwa? Ba su da kwanciyar hankali. Domin abokan gabansu za su iya kawo musu hari cikin sauƙi. Amma yanzu wannan mutumin Nehemiah yana taimaka wa mutanen su sake gina ganuwar. Ka san ko wanene Nehemiah?

Nehemiah Ba’isra’ile ne da ya fito daga birnin Shushan, inda Mordekai da Esther suke da zama. Nehemiah yana aiki a fadan sarki, saboda haka abokin Mordekai da kuma sarauniya Esther. Amma Littafi Mai Tsarki bai ce Nehemiah yana yi wa Sarki Ahasuerus mijin Esther aiki ba. Ya yi wa sarkin da ya gaje shi ne aiki, Sarki Artaxerxes.

Ka tuna, Artaxerxes sarkin kirki ne wanda ya bai wa Ezra kuɗi ya kyawanta haikalin Jehobah. Amma Ezra bai gina ganuwar da ta rushe ba na birnin. Bari mu ga yadda Nehemiah ya yi wannan aikin.

An yi shekara 13 tun da Artaxerxes ya bai wa Ezra kuɗi ya gyara haikalin. Yanzu Nehemiah ne shugaban shayarwa na Sarki Artaxerxes. Aikinsa shi ne ya bai wa sarki giya, kuma yana tabbata cewa babu wanda yake ƙoƙarin ya kashe shi da guba. Aiki ne mai muhimmanci.

To, wata rana sai ɗan’uwan Nehemiah Hanani da wasu mutane daga ƙasar Isra’ila suka zo su ziyarci Nehemiah. Suka gaya masa matsalolin da Isra’ilawan suke fuskanta, da kuma yadda ganuwar Urushalima har yanzu take rushe. Wannan ya sa Nehemiah ya yi baƙin ciki ƙwarai kuma ya gaya wa Jehobah game da shi.

Wata rana sarki ya lura cewa Nehemiah yana baƙin ciki, sai ya tambaye shi: ‘Me ya sa kake baƙin ciki?’ Nehemiah ya gaya masa cewa domin yanayin Urushalima ba shi da kyau kuma ganuwarta tana rushe. ‘To me kake so in yi maka?’ sarki ya yi tambaya.

Nehemiah ya ce: ‘Ka bari in je Urushalima, domin in gina ganuwar.’ Sarki Artaxerxes yana da kirki. Ya ce wa Nehemiah ya tafi, kuma ya taimake shi da katakai domin ginin. Da ya isa Urushalima, ya gaya wa mutanen shirinsa. Suka so ra’ayinsa suka ce: ‘Mu fara ginin.’

Da abokan gaban Isra’ila suka ga ganuwar ta fara yin tsawo, sai suka ce: ‘Mu je mu kashe su, mu hana ginin.’ Da Nehemiah ya ji haka sai ya ba wa masu aiki māsu da takubba. Kuma ya ce musu: ‘Kada ku ji tsoron abokan gabanku. Ku yi yaƙi domin ’yan’uwanku, da ’ya’yanku, da matanku, da kuma gidajenku.’

Mutanen suka yi gaba gaɗi. Suka kasance a shirye da makamansu dare da rana, suka ci gaba da ginin. A cikin kwanaki 52 suka gama ginin. Yanzu mutanen saka sami kwanciyar hankali cikin birnin. Nehemiah da Ezra suka koyar da mutanen dokokin Allah, kuma mutanen suka yi farin ciki.

Amma har yanzu abubuwa ba su kasance kamar yadda suke ba kafin a kwashi mutanen zuwa bauta a Babila. Mutanen yanzu suna ƙarƙashin sarkin Farisa kuma dole su miƙa kai. Amma Jehobah ya yi alkawari cewa zai aiko da wani sabon sarki, kuma sarkin zai kawo salama ga mutanen. Wanene ne wannan sarkin? Ta yaya zai kawo salama ga duniya? Har sai bayan shekaru 450 kafin aka sami bayani game da wannan. A lokacin ne aka haifi ɗa mafi muhimmanci. Amma wannan wani labari ne daban.

Nehemiah sura 1 zuwa 6.