Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 6

Haihuwar Yesu Zuwa Mutuwarsa

Haihuwar Yesu Zuwa Mutuwarsa

An aiki mala’ika Jibrailu zuwa wurin wata budurwa kyakkyawa mai suna Maryamu. Ya gaya mata cewa za ta haifi ɗa wanda zai zama sarki ya yi sarauta har abada. An haifi Yesu a gidan tumaki, a nan kuma makiyaya suka ziyarce shi. Daga baya, tauraro ya ja-goranci wasu mutane daga Gabas zuwa wurin yaron. Za mu ga wanda ya sa suka ga tauraron, da kuma yadda aka ceci Yesu daga ƙoƙarin da aka yi don a kashe shi.

Za mu ga Yesu sa’ad da yake ɗan shekara 12, yana magana da malamai a haikali. Bayan shekara goma sha takwas Yesu ya yi baftisma, sai ya fara wa’azin Mulkin da kuma koyarwa da Allah ya aiko shi duniya ya yi. Yesu ya zaɓi mutane 12 ya mai da su manzanninsa domin su taimake shi a aikinsa.

Yesu kuma ya yi mu’ujizai masu yawa. Ya ciyar da mutane dubbai da ƙananan kifaye kaɗan da kuma burodi. Ya warkar da majiyata kuma ya tayar da matattu. A ƙarshe, za mu koyi game da abubuwa da yawa da suka faru da Yesu a kusan ƙarshen rayuwarsa da kuma yadda aka kashe shi. Yesu ya yi wa’azi na kusan shekara uku da rabi, saboda haka SASHE NA 6 ya ba da tarihi ne na shekara 34.