Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 84

Mala’ika Ya Ziyarci Maryamu

Mala’ika Ya Ziyarci Maryamu

WANNAN kyakkyawar mace Maryamu ce. Ba’isra’iliya ce da take da zama a garin Nazare. Allah ya sani cewa ita mutumiyar kirki ce. Abin da ya sa ke nan ya aiki mala’ika Jibrailu ya yi magana da ita. Ka san abin da Jibrailu ya zo ya gaya wa Maryamu? Bari mu gani.

‘A gaishe ki, ke da kike mai albarka,’ Jibrailu ya gaishe ta. ‘Jehobah yana tare da ke.’ Maryamu ba ta taɓa ganin wannan mutumin ba a dā. Ta damu domin ba ta san abin da yake nufi ba. Babu ɓata lokaci Jibrailu ya kwantar mata da hankali.

‘Kada ki ji tsoro Maryamu,’ in ji shi. ‘Jehobah ya yi farin ciki da ke ƙwarai. Abin da ya sa ke nan zai yi abin al’ajabi da ke. Ba da daɗewa ba za ki haifi ɗa. Kuma ki sa masa suna Yesu.’

Jibrailu ya ci gaba da bayani: ‘Wannan ɗa zai zama mai girma, kuma za a kira shi ɗan Allah Maɗaukakin Sarki. Jehobah kuma zai ba shi sarauta kamar Dauda. Amma Yesu zai zama sarki har abada, kuma Mulkinsa zai dawwama!’

‘Ta yaya haka zai faru?’ Maryamu ta yi tambaya. ‘Ban yi aure ba ma tukuna. Ban taɓa zama tare da namiji ba, to ta yaya zan haifi ɗan?’

‘Ikon Allah zai sauko bisan ki,’ in ji Jibrailu. ‘Saboda haka za a kira yaron ɗan Allah.’ Saboda da haka ya gaya wa Maryamu: ‘Ki tuna da ’yar’uwarki Elizabatu. Mutane sun ce ta tsufa ta shige haihuwa. Amma ba da daɗewa ba za ta haifi ɗa. To kin gani, ba abin da Allah ba zai iya yi ba.’

A take Maryamu ta ce: ‘Ni baiwar Jehobah ce! Bari ya kasance kamar yadda ka ce.’ Sai mala’ikan ya tafi.

Maryamu ta yi sauri ta ziyarci Elizabatu. Sa’ad da Elizabatu ta ji muryar Maryamu sai jaririn da ke cikin ta ya yi tsalle domin farin ciki. Cike da ruhu mai sarki, Elizabatu ta ce wa Maryamu: ‘Ke mai albarka ce tsakanin mata.’ Maryamu ta zauna tare da Elizabatu na wata uku, sai ta koma gida a Nazare.

Maryamu ta kusa ta auri wani mutum mai suna Yusufu. Amma sa’ad da Yusufu ya ji cewa Maryamu za ta haifi ɗa, yana ganin bai kamata ya aure ta ba. Sai mala’ikan Allah ya ce masa: ‘Kada ka ji tsoron aurar Maryamu. Domin Allah ne ya ba ta ɗa.’ Saboda haka Yusufu ya auri Maryamu, suka jira a haifi Yesu.

Luka 1:26-56; Matta 1:18-25.