Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 86

Masu Bin Taurari

Masu Bin Taurari

KA GA wannan tauraro mai haske da wannan mutumin yake nunawa? Sa’ad da suka bar Urushalima, tauraro ya bayyana. Waɗannan mutane masu nazarin taurari daga gabas suke. Sun gaskata cewa wannan sabon tauraro zai kai su ga mutum mai muhimmanci.

Sa’ad da mutanen suka isa Urushalima, suka yi tambaya: ‘Ina yaron da zai zama sarkin Yahudawa?’ “Yahudawa” wani suna ne na Isra’ilawa. Mutanen suka ce: ‘Mun ga tauraron yaron ne da farko sa’ad da muke gabas, kuma mun zo ne mu bauta masa.’

Sa’ad da Hirudus, wanda yake sarautar Urushalima ya sami labarin sai abin ya ba shi haushi. Ba ya son wani sarki ya gaje shi. Saboda haka Hirudus ya aike babban firist ya tambaye shi: ‘A ina ne za a haifi sarkin da aka yi alkawarinsa?’ Suka amsa: ‘Littafi Mai Tsarki ya ce a Baitalami.’

Saboda haka Hirudus ya kira mutanen da suka fito daga gabas, ya ce musu: ‘Ku je ku nemi yaron. Idan kun same shi, ku gaya mini. Ni ma ina so in je in bauta masa.’ Amma, ainihi Hirudus yana so ne ya sami yaron ya kashe shi!

Sai tauraron ya ci gaba ya ja-goranci mutanen zuwa Baitalami, ya tsaya a kan gidan da yaron yake. Sa’ad da mutanen suka shiga cikin gidan, suka sami Maryamu da Yesu jariri. Suka yi wa Yesu kyauta. Amma daga baya Jehobah ya yi wa mutanen gargaɗi ta mafarki cewa kada su koma wurin Hirudus. Saboda haka suka koma ƙasarsu ta wata hanya.

Sa’ad da Hirudus ya sami labari cewa mutane da suka fito daga gabas sun koma ƙasarsu, sai ya yi fushi sosai. Saboda haka ya ba da umurnin cewa a kashe dukan yara ƙanana da suke Baitalami daga mai shekara biyu zuwa ƙasa. Amma Jehobah ya riga ya yi wa Yusufu gargaɗi cikin mafarki a kan lokaci, Yusufu ya kwashi iyalinsa zuwa ƙasar Masar. Daga baya da Yusufu ya sami labari cewa Hirudus ya mutu, sai ya koma gidansu a Nazare tare da Maryamu da Yesu. A nan ne Yesu ya girma.

Wanene kake tsammani ya sa sabon tauraron ya haskaka? Ka tuna cewa mutanen da farko sai da suka je Urushalima bayan sun ga tauraron. Shaiɗan Iblis yana so ne ya kashe Ɗan Allah, kuma ya sani cewa sarki Hirudus na Urushalima zai so ya kashe shi. Hakika Shaiɗan ne ya sa wannan tauraro ya haskaka.

Matta 2:1-23; Mikah 5:2.