Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 87

Saurayi Yesu A Haikali

Saurayi Yesu A Haikali

DUBI wannan yaron yana magana da tsofaffin mutane. Malamai ne na haikalin Allah a Urushalima. Yaron kuma Yesu ne. Ya ɗan girma a nan. Yanzu yana da shekara 12.

Malaman suna mamaki cewa Yesu yana da sanin Allah da kuma abubuwa da suke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki. Amma me ya sa Yusufu da Maryamu ba sa nan? Ina suke? Bari mu gani.

Kowace shekara Yusufu yana kawo iyalinsa zuwa Urushalima domin biki na musamman da ake kira bikin ƙetarewa. Doguwar tafiya ce daga Nazare zuwa Urushalima. Babu wanda yake da mota, kuma babu jirgin ƙasa. Ba su da waɗannan abubuwa a zamani dā. Yawancin mutane suna tafiya ne da ƙafafunsu, kuma yana ɗaukansu kwana uku su isa Urushalima.

A yanzu Yusufu yana da babban iyali. Suna da ƙannen Yesu maza da mata da suke kula da su. A wannan shekarar Yusufu da Maryamu sun yi doguwar tafiyar da ’ya’yansu zuwa Nazare. Suna tsammani Yesu yana tare da waɗansu da suke tafiya tare. Amma da suka tsaya, bayan sun yi yini suna tafiya, ba su ga Yesu ba. Suka neme shi tsakanin ’yan’uwa da abokai ba su gan shi ba! Saboda haka suka koma Urushalima su neme shi.

A ƙarshe suka sami Yesu a nan tare da malamai. Yana sauraronsu kuma yana yi musu tambayoyi. Kuma dukan mutanen suka yi mamakin hikimarsa. Amma Maryamu ta ce: ‘Ɗana me ya sa ka yi mana haka? Ni da babanka mun damu ƙwarai muna nemanka.’

‘Me ya sa kuke nema na?’ Yesu ya yi tambaya. ‘Ba ku sani ba ne cewa zan kasance a gidan Ubana?’

Hakika, Yesu yana ƙaunar ya kasance a inda zai koyi game da Allah. Ba haka ya kamata mu ji ba mu ma? A garinsu Nazare Yesu yana zuwa taro domin bauta a kowace mako. Domin yana sauraron abin da ake faɗa, ya koyi abubuwa da yawa daga Littafi Mai Tsarki. Ya kamata mu zama kamar Yesu mu yi koyi da misalinsa.

Luka 2:41-52; Matta 13:53-56.