Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 92

Yesu Ya Ta Da Matattu

Yesu Ya Ta Da Matattu

YARINYAR da kake gani a nan shekararta 12. Yesu ya riƙe hannunta, kuma mamarta da babanta suna tsaye a kusa. Ka san abin da ya sa suke farin ciki haka sosai? Bari mu gani.

Baban yarinyar muhimmin mutum ne mai suna Yariyus. Wata rana sai ’yarsa ta yi rashin lafiya, aka kwantar da ita a kan gado. Amma ba ta sami sauƙi ba. Rashin lafiyarta ya ci gaba da yin tsanani. Yariyus da matarsa suka damu ƙwarai, domin kamar dai ’yarsu za ta mutu. Ita ce kawai ’yarsu. Saboda haka Yariyus ya je ya nemi Yesu. Ya sami labarin irin mu’ujizai da Yesu yake yi.

Sa’ad da Yariyus ya sami Yesu, akwai jama’a mai yawa tare da shi. Amma Yariyus ya shiga tsakanin mutane ya je ya faɗi a gaban Yesu. ’yata ba ta da lafiya ƙwarai,’ in ji shi. ‘Don Allah ka zo ka warkar da ita,’ ya roƙi Yesu. Yesu ya ce masa zai bi shi.

Sa’ad da suke tafiya, jama’ar suka ci gaba da matsawa kusa da shi. Farat ɗaya Yesu ya tsaya. ‘Waye ya taɓa ni?’ ya yi tambaya. Yesu ya ji iko ya fita daga jikinsa, saboda haka ya sani cewa da wanda ya taɓa shi. Amma wanene ne? Wata mace ce da ba ta da lafiya na shekara 12. Ta zo ta taɓa rigar Yesu ta warke!

Hakan ya sa Yariyus ya sami ƙarfin zuciya, domin ya ga yadda yake da sauƙi Yesu ya warkar da mutane. Amma sai wani ya zo da saƙo. ‘Kada ka dami Yesu kuma,’ ya gaya wa Yariyus. ‘’yarka ta riga ta mutu.’ Yesu ya ji abin da suka ce sai ya ce wa Yariyus: ‘Kada ka damu, za ta sami lafiya.’

Sa’ad da suka isa gidan Yariyus, mutane suna kuka suna makoki. Amma Yesu ya ce: ‘Kada ku yi kuka. Yarinyar ba ta mutu ba. Barci kawai take yi.’ Amma suka yi dariya suka yi wa Yesu ba’a, domin sun sani ta mutu.

Sai Yesu ya kira baban yarinyar da mamarta da kuma uku daga cikin almajiransa zuwa ɗakin da yarinyar take kwance. Ya riƙe ta a hannu ya ce: ‘Ki tashi!’ Ta tashi kamar yadda kake gani a nan. Ta tashi tsaye kuma ta fara tafiya! Abin da ya sa ke nan babanta da mamarta suke farin ciki ƙwarai.

Wannan ba ita ce na farko da Yesu ya tayar daga matattu ba. Na fari da Littafi Mai Tsarki ya faɗa shi ne ɗan wata gwauruwa da take zama a birnin Na’in. Daga baya kuma Yesu ya ta da Li’azaru, ɗan’uwan Maryamu da Marta daga matattu. Sa’ad da Yesu zai zama sarkin Mulkin Allah, zai ta da mutane da yawa daga matattu. Abin farin ciki ne, ko ba haka ba?

Luka 8:40-56; 7:11-17; Yohanna 11:17-44.