Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 96

Yesu Ya Warkar Da Marasa Lafiya

Yesu Ya Warkar Da Marasa Lafiya

SA’AD da Yesu ya yi tafiye tafiye a cikin duka ƙasar, ya warkar da marasa lafiya. An ba da labarin mu’ujizar da ya yi a ƙauyuka da birane. Saboda haka mutane suka kawo masa guragu da makafi da kurame da kuma wasu marasa lafiya. Kuma Yesu ya warkar da su duka.

Yanzu fiye da shekara uku ke nan tun da Yohanna ya yi wa Yesu baftisma. Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa ba da daɗewa ba za shi Urushalima, kuma za a kashe shi, bayan haka zai tashi daga matattu. Amma a yanzu Yesu ya ci gaba da warkar da mutane.

A wata ranar Asabar Yesu yana koyarwa. Asabar ranar hutu ne ga Yahudawa. Matar da kake gani a nan ba ta da lafiya sosai. Shekara 18 ba ta miƙe ba domin ba ta iya miƙewa. Saboda haka Yesu ya taɓa ta, ta fara miƙewa. Ta warke!

Hakan ya sa shugaban addini suka yi fushi. ‘Muna da kwanaki shida na aiki,’ waninsu ya faɗa da babbar murya daga cikin jama’a. ‘Waɗannan ne ranar da ya kamata ka zo domin warkar da mutane, ba a ranar Asabar ba!’

Amma Yesu ya amsa ya ce: ‘Ku mugayen mutane. Kuna kwance jakinku ku je ku ba su ruwa a ranar Asabar. Saboda haka bai kamata a warkar da wannan mata da ba ta da lafiya na shekara 18 a ranar Asabar ba?’ Amsar Yesu ya sa mutanen suka ji kunya.

Daga baya Yesu da manzanninsa suka ci gaba da tafiya zuwa Urushalima. Da suka kusa shiga garin Jericho, makafi biyu masu bara suka sami labarin cewa Yesu yana wucewa. Sai suka fara ihu: ‘Yesu, ka taimake mu!’

Yesu ya kira makafin ya tambaye su: ‘Me kuke so in yi muku?’ Suka ce: ‘Ubangiji, muna so idanunmu su buɗe.’ Yesu ya taɓa idanunsu nan take idanunsu suka buɗe! Ka san abin da ya sa Yesu ya yi duka waɗannan mu’ujizai masu ban mamaki? Domin yana ƙaunar mutanen kuma yana so su ba da gaskiya a gare shi. Saboda haka mun tabbata cewa sa’ad da ya zama Sarki babu wanda zai sake yin rashin lafiya a duniya.

Matta 15:30, 31; Luka 13:10-17; Matta 20:29-34.