Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 97

Yesu Ya Shigo Kamar Sarki

Yesu Ya Shigo Kamar Sarki

BA DA daɗewa ba bayan ya warkar da makafi biyu masu bara, Yesu ya isa wani ƙaramin ƙauye kusa da Urushalima. Ya gaya wa almajiransa biyu: ‘Ku shiga cikin ƙauyen za ku sami ɗan jaki. Ku kwance shi ku kawo mini.’

Da suka kawo masa jakin sai Yesu ya hau. Sai ya shiga cikin Urushalima da ba ta da nisa sosai. Da ya yi kusa da birnin, taron jama’a suka fito su tare shi. Yawancinsu suka tuɓe rigunansu suka shimfiɗa a kan hanya. Wasu suka yanko ganyayen dabino. Suka shimfiɗa wannan ma a kan hanya, suka yi ihu: ‘Mai albarka ne sarkin mai zuwa cikin sunan Jehobah!’

Da daɗewa a Isra’ila sababbin sarakuna za su hau jaki zuwa cikin Urushalima domin su nuna kansu ga mutanen. Abin da Yesu yake yi ke nan. Kuma waɗannan mutane suna nuna cewa suna so Yesu ya zama sarkinsu. Amma ba dukan mutanen ne suke so ya zama sarkinsu ba. Za mu ga wannan ta abin da ya faru sa’ad da Yesu ya tafi haikali.

A haikali Yesu ya warkar da makafi da guragu. Sa’ad da yara ƙanana suka ga wannan suka yi ta waƙar yabo ga Yesu. Amma hakan ya sa firistoci suka yi fushi, suka gaya wa Yesu: ‘Ka ji abin da yaran nan suka faɗa?’

‘E, na ji,’ Yesu ya amsa musu. ‘Ba ku karanta ba ne a cikin Littafi Mai Tsarki cewa: “Daga bakin yara ƙanana Allah ya kawo yabo?”’ Saboda haka yaran suka ci gaba da yabon sarki na Allah.

Muna so mu zama kamar waɗannan yara, ko ba haka ba? Wasu mutane za su yi ƙoƙari su hana mu yin magana game da mulkin Allah. Amma za mu ci gaba da gaya wa mutane game da abubuwa masu ban sha’awa da Yesu zai yi wa mutane.

Lokaci bai yi da Yesu zai fara sarauta ba sa’ad da yake duniya. Yaushe ne wannan lokaci zai yi? Almajiran Yesu suna so su sani. Za mu karanta game da wannan a gaba.

Matta 21:1-17; Yohanna 12:12-16.