Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 98

A Kan Dutsen Zaitun

A Kan Dutsen Zaitun

WANNAN Yesu ne a kan Dutsen Zaitun. Mutane huɗu da suke tare da shi manzanninsa ne. Andarawus ne da Bitrus ’yan’uwan juna da kuma Yakub da Yohanna ’yan’uwan juna. Haikalin Jehobah ne a Urushalima kake gani a can nesa.

Kwana biyu ke nan tun da Yesu ya shigo Urushalima a kan ɗan jaki. Yanzu ranar Talata ne. Da farko Yesu yana haikali. A nan firistoci suna so su kama Yesu su kashe shi. Amma suna tsoron su yi haka domin mutanen suna ƙaunarsa.

Yesu ya kira shugabannin addinan: ‘Macizai ’ya’yan macizai!’. Yesu kuma ya ce Allah zai yi musu horo domin dukan muguntar da suke yi. Bayan haka Yesu ya hau Dutsen Zaitun, sai waɗannan manzanni huɗu suka fara yi masa tambayoyi. Ka san abin da suke tambayar Yesu?

Manzannin suna tambaya game da abubuwa ne da suke gaba. Sun sani cewa Yesu zai kawo ƙarshen dukan mugunta a duniya. Amma ba su san lokacin da wannan zai faru ba. Yaushe ne Yesu zai sake zuwa ya zama Sarki ya yi sarauta?

Yesu ya sani cewa mabiyansa a duniya ba za su iya ganinsa ba sa’ad da ya zo. Domin zai kasance a sama, kuma ba za su iya ganinsa ba a can. Saboda haka Yesu ya gaya wa manzanninsa wasu abubuwa da za su faru a duniya sa’ad da ya fara sarauta a sama. Waɗanne ne wasu a cikin waɗannan abubuwa?

Yesu ya ce za a yi yaƙe-yaƙe, mutane da yawa za su yi rashin lafiya da kuma yunwa, yin laifi zai daɗa muni, kuma za a yi manyan girgizan ƙasa. Yesu kuma ya ce za a yi wa’azi game da mulkin Allah a ko’ina a duniya. Muna ganin wannan abubuwa suna faruwa a zamaninmu? Hakika kuwa! Saboda haka za mu tabbata cewa Yesu yana sarauta a sama. Ba da daɗewa ba zai kawo ƙarshen dukan mugunta a duniya.

Matta 21:46; 23:1-39; 24:1-14; Markus 13:3-10.