Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 100

Yesu A Cikin Gadina

Yesu A Cikin Gadina

BAYAN sun fita daga ɗakin gidan sama, Yesu da manzanninsa suka je gadina na Gathsemane. Sun sha zuwa wannan wurin a dā. Yesu ya ce musu su kasance a faɗake kuma su yi addu’a. Sai ya yi ɗan nisa da su, ya durƙusa ya yi addu’a.

Daga baya Yesu ya koma wurin da almajiransa suke. Me kake tsammanin suke yi? Suna barci! Sau uku Yesu ya gaya masu su kasance a faɗake, amma dukan lokaci da ya komo sai ya same su suna barci. ‘Me ya sa kuke barci a irin wannan lokaci?’ in ji Yesu a zuwansa na ƙarshe. ‘Lokaci ya yi da za a bayar da ni ga abokan gaba na.’

A daidai wannan lokaci sai suka ji surutun jama’a. Duba! Mutanen suna zuwa da takubba da sanduna! Suna riƙe da jiniyoyi domin ya ba su haske. Sa’ad da suka yi kusa, wani ya fito daga cikin jama’ar ya zo wurin Yesu. Ya yi masa sumba kamar yadda kake gani a nan. Mutumin Yahuda Iskariyoti ne! Me ya sa ya yi wa Yesu sumba?

Yesu ya yi tambaya: ‘Yahuda, ka bashe ni ne da sumba?’ Hakika, sumbar alama ce. Ya nuna wa mutanen da suke tare da Yahuda cewa wannan shi ne Yesu, mutumin da suke so. Saboda haka abokan gabansa suka fito suka kama shi. Amma Bitrus ba zai ƙyale su su tafi da Yesu ba tare da faɗa ba. Ya zaro takobi da yake ɗauke da shi ya tsare mutumin da yake kusa da shi. Takobin bai sami wuyar mutumin ba ya tsare kunnensa na dama. Amma Yesu ya taɓa kunnen mutumin ya warke.

Yesu ya gaya wa Bitrus: ‘Ka mai da takobinka. Kana tsammanin ba zan iya roƙon Ubana ya aiko da mala’iku dubbai su ceci ni ba ne?’ Hakika, zai iya! Amma Yesu bai roƙi Allah ya aiko da ko mala’ika ɗaya ba, domin ya sani cewa lokaci ya yi da abokan gabansa za su kama shi. Saboda haka ya ƙyale su suka tafi da shi. Bari mu ga abin da ya faru da Yesu yanzu.

Matta 26:36-56; Luka 22:39-53; Yohanna 18:1-12.