Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 101

An Kashe Yesu

An Kashe Yesu

DUBI irin muguntar da ake yi a nan! Ana kashe Yesu. An rataye shi a kan gungume. An buga masa kusa a hannayensa da ƙafafunsa. Me ya sa wani zai so ya yi wa Yesu haka?

Domin wasu mutane ba sa son shi ne. Ka san ko su waye ne? Ɗaya daga cikinsu shi ne mugun mala’ika Shaiɗan Iblis. Shi ne ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi wa Jehobah rashin biyayya. Kuma Shaiɗan ne ya sa abokan gaban Yesu suka yi wannan mugun abin.

Kafin ma su buga Yesu a kan gungume, abokan gabansa suka yi masa wasu miyagun abubuwa. Ka tuna yadda suka je gadinar Jathsaimani suka kama shi? Su waye ne waɗannan abokan gabansa? Shugabannin addini ne. Bari mu ga abin da ya faru a gaba.

Sa’ad da shugabannin addinai suka kama Yesu, manzanninsa suka gudu. Suka ƙyale Yesu shi kaɗai da abokan gabansa domin sun tsorata. Amma manzo Bitrus da Yohanna ba su yi nisa ba. Suka bi su su ga abin da zai faru da Yesu.

Firistoci suka kai Yesu wurin tsoho Annas wanda dā shi ne babban firist. Jama’ar ba su ɓata lokacin a nan ba. Sai suka kai Yesu gidan Kayafa, wanda shi ne babban firist na yanzu. Shugabannin addini da yawa sun riga sun taru a gidansa.

A nan gidan Kayafa suka tuhume shi. Aka kawo mutane su yi ƙarya game da Yesu. Dukan shugabannin addini suka ce: ‘A kashe Yesu.’ Sai suka tofa masa yau a fuska, kuma suka naushe shi.

Sa’ad da suke yin wannan duka, Bitrus yana waje a filin gida. Da akwai sanyi saboda haka mutanen suka hura wuta. Sa’ad da suke ɗuma kansu da wutar, wata baiwa ta dubi Bitrus ta ce: ‘Wannan mutumin ma yana tare da Yesu.’

‘A’a, ba ni ba ne!’ in ji Bitrus.

Sau uku mutane suka ce wa Bitrus yana tare da Yesu. Amma sai ya ce ba gaskiya ba ne. Da Bitrus ya faɗi na ukun, sai Yesu ya juya ya kalle shi. Bitrus ya yi baƙin ciki domin wannan ƙarya da ya yi, ya fita waje ya yi ta kuka.

Da rana ta fara fitowa a ranar Jumma’a, firistoci suka kai Yesu wajen da suke babban taronsu, wato Majalisa. A nan suka tattauna game da abin da za su yi da shi. Suka kai shi wurin Bilatus Babunti, wanda yake sarautar gundumar Yahudiya.

‘Wannan mugun mutum ne,’ firistoci suka gaya wa Bilatus. ‘Ya kamata a kashe shi.’ Bayan ya yi wa Yesu tambaya, Bilatus ya ce: ‘Ni ban ga laifi da ya yi ba.’ Sai Bilatus ya tura Yesu wajen Hirudus Antibas. Hirudus shi ke sarautar Galili, amma yana zama a Urushalima. Hirudus bai ga laifin da Yesu ya yi ba, sai ya tura shi wurin Bilatus kuma.

Bilatus yana so ya ƙyale Yesu. Amma abokan gabansa suna so a ƙyale wani wanda yake kurkuku maimakonsa. Wannan mutumin ɗan fashi ne Barabbas. Sa’ad da Bilatus ya fito da Yesu waje rana ta riga ta yi tsaka. Ya ce wa mutanen: ‘Dubi Sarkinku!’ Amma sai babban firist ya yi ihu: ‘A kashe shi! A kashe shi! Saboda haka, Bilatus ya ƙyale Barabbas, suka tafi da Yesu inda za su kashe shi.

Ranar Jumma’a da rana aka rataye Yesu a kan gungume. Ba za ka iya ganinsu ba a hoto, amma a kowane gefen Yesu da mai laifi ɗaya da aka kashe a kan gungume. Kafin Yesu ya mutu, ɗaya cikin waɗannan masu laifi ya ce masa: ‘Ka tuna da ni sa’ad da ka shiga cikin mulkinka.’ Yesu ya amsa: ‘Na yi maka alkawari za ka kasance tare da ni cikin Aljanna.’

Wannan ba alkawari ba ne mai ban sha’awa? Ka san ko wace aljanna ce Yesu yake maganarta? A ina ne aljannar da Allah ya yi da farko take? Hakika, a duniya ne. Sa’ad da Yesu ya fara sarauta a sama, zai ta da wannan mutumin ya more sabuwar Aljanna a duniya. Bai kamata ba ne mu yi farin ciki?

Matta 26:57-75; 27:1-50; Luka 22:54-71; 23:1-49; Yohanna 18:12-40; 19:1-30.