Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 109

Bitrus Ya Ziyarci Karniliyus

Bitrus Ya Ziyarci Karniliyus

MANZO Bitrus ne yake tsaye a nan, waɗanda suke bayansa kuma wasu abokansa ne. Amma me ya sa wannan mutumin ya durƙusa wa Bitrus? Ya kamata ya yi haka kuwa? Ka san ko wanene ne shi?

Sunansa Karniliyus ne. Hafsa ne na sojan Roma. Karniliyus bai san Bitrus ba, amma an gaya masa ya gayyace shi zuwa gidansa. Bari mu ga yadda haka ya faru.

Mabiyan Yesu na farko Yahudawa ne, amma Karniliyus ba Bayahude ba ne. Duk da haka yana ƙaunar Allah, yana yi masa addu’a, kuma yana yin wa mutane da yawa kirki. To, wata rana mala’ika ya bayyana masa ya ce: ‘Allah ya yi farin ciki da kai, kuma zai amsa addu’o’inka. Ka aiki mutane su kira wani mutum mai suna Bitrus. Yana can Yafa a bakin teku a gidan Siman.’

Ba tare da wani ɓata lokaci ba, Karniliyus ya aiki mutane su nemi Bitrus. Washegari, sa’ad da mutanen suka yi kusa da Yafa, Bitrus yana zaune a kan daɓen rufin gidan Siman. A nan Allah ya sa Bitrus ya yi tunanin cewa ya ga yadi yana saukowa daga sama. Yadin kuma yana ɗauke da dabbobi iri iri. A cikin dokar Allah, waɗannan dabbobin ba su da tsabta domin abinci, duk da haka wata murya ta ce masa: ‘Ka tashi Bitrus. Ka yanka ka ci.’

‘A’a!’ in ji Bitrus. ‘Ban taɓa cin abin da ke marar tsabta ba.’ Sai muryar ta ce wa Bitrus: ‘Ka dena kiran abin da Allah ya tsabtace marar tsabta.’ Haka ya faru wajen sau uku. Sa’ad da Bitrus yake mamakin ma’anar wannan duka sai mutane da Karniliyus ya aika suka isa gidan suka nemi Bitrus.

Bitrus ya sauka ƙasa ya ce: ‘Ni kuke nema. Me ya kawo ku?’ Sa’ad da mutanen suka ce mala’ika ya gaya wa Karniliyus ya gayyaci Bitrus zuwa gidansa, Bitrus ya yarda ya bi su. Washegari Bitrus da abokansa suka tafi su ziyarci Karniliyus a Kaisariya.

Karniliyus ya tara danginsa da kuma abokansa. Sa’ad da Bitrus ya isa, Karniliyus ya tare shi. Ya durƙusa a gaban Bitrus, kamar yadda kake gani a nan. Amma Bitrus ya ce: ‘Ka tashi, ni mutum ne kamarka.’ Hakika, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ba daidai ba ne mutum ya durƙusa ya yi wa mutum bauta. Jehobah kaɗai ya kamata mu bauta wa.Sai Bitrus ya yi wa mutanen da suka taru wa’azi. ‘Na ga cewa Allah ya yarda da dukan mutane da suke so su bauta masa,’ in ji Bitrus. Kuma sa’ad da yake magana, Allah ya aiko da ruhunsa mai tsarki mutanen suka fara magana da yare dabam dabam. Wannan ya ba wa almajiran Yahudawa da suka bi Bitrus mamaki, domin suna tsammanin Yahudawa kawai ne Allah ya yi wa tagomashi. Wannan ya nuna masu cewa Allah ba ya ɗaukan wata ƙabila da muhimmanci fiye da wata. Wannan abu ne mai kyau da ya kamata mu tuna, ko ba haka ba?

Ayukan Manzanni 10:1-48; 11:1-18; Ru’ya ta Yohanna 19:10.