Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 112

Jirgi Ya Yi Haɗari A Tsibiri

Jirgi Ya Yi Haɗari A Tsibiri

DUBA! Jirgin yana cikin matsala! Yana farfashewa! Ka ga mutanen da suka faɗa cikin ruwa? Wasu sun riga sun yi kusa da bakin kogin. Wannan Bulus ne a can? Bari mu ga abin da yake faruwa da shi.

Ka tuna Bulus ya yi shekara biyu a kurkuku a Kaisariya. Sai aka saka shi da wasu ’yan kurkuku cikin jirgin ruwa, suka fara tafiya zuwa Roma. Sa’ad da suka bi kusa da tsibirin Karita, guguwa ta same su. Iska ta yi ta busa su har mutanen suka kasa tuka jirgin. Ba su iya ganin rana ba ko kuma taurari da dare. A ƙarshe bayan kwanaki masu yawa, dukan waɗanda suke cikin jirgin suka cire rai cewa za su tsira.

Sai Bulus ya tashi tsaye ya ce: ‘Babu ko ɗayanku da zai rasa ransa; jirgin ne kawai zai hallaka. Domin jiya daddare mala’ikan Allah ya zo mini ya ce: “‘Kada ka ji tsoro, Bulus! Gama dole za ka tsaya a gaban mai mulkin Romawa Kaisar. Kuma Allah za ya ceci dukan musu tafiya tare da kai.’”

Da tsakar daren rana ta 14 tun da aka fara guguwar, matuƙa jirgin suka lura cewa ruwan ba shi da zurfi kuma! Domin ba sa so su je su yi karo da wani dutse a cikin duhu sai suka sauke anka. Washegari sai suka ga gaɓar teku. Suka yi ƙoƙarin tuka jirgin har zuwa gaɓar tekun.

Da suka yi kusa da gaɓar tekun, sai jirgin ya maƙale a cikin yashi. Sai igiyar ruwa ta fara bugun jirgin, jirgin ya farfashe. Hafsan sojoji mai kula da jirgin ya ce: ‘Dukan waɗanda suka iya ruwa su faɗa su yi iyo zuwa gaɓar tekun. Ku sauran ku faɗa kuma ku kama jikin jirgin da ya farfashe ku riƙe.’ Abin da suka yi ke nan. Da haka duka mutane 276 da suke cikin jirgin suka tsira, kamar yadda mala’ikan ya yi alkawari.

Ana kiran tsibirin Malita. Mutanen suna da kirki suka kula da dukan mutanen. Sa’ad da yanayi ya yi kyau, aka saka Bulus cikin wani jirgi aka kai shi Roma.

Ayukan Manzanni 27:1-44; 28:1-14.