Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 115

Sabuwar Aljanna A Duniya

Sabuwar Aljanna A Duniya

KA DUBI dukan waɗannan dogayen itatuwa, kyawawan furanni da kuma duwatsu. Wannan wajen yana da kyau, ko ba haka ba? Dubi barewa tana cin abinci a hannun wannan yaron. Dubi zaki da kuma dawakai da suke tsaye a wancan wuri mai ciyayi. Ba za ka so ba ne ka zauna a gidan da yake irin wannan wurin?

Allah yana so ka rayu har abada a duniya cikin aljanna. Kuma ba ya so ka yi ciwo da mutane suke yi a yau. Wannan shi ne alkawari da Littafi Mai Tsarki ya yi ga waɗanda za su zauna a sabuwar aljanna: ‘Allah zai kasance tare da su. Ba za a sake mutuwa ba ko kuka ko azaba. Abubuwa na dā sun riga sun shuɗe.’

Yesu zai tabbata cewa dukan waɗannan abubuwa sun tabbata. Ka san ko yaushe ne? Hakika, bayan ya kawar da dukan mugunta da kuma miyagun mutane daga duniya. Ka tuna cewa, sa’ad da Yesu yake duniya ya warkar da mutane daga dukan ire-iren cututtuka, kuma ya ta da mutane daga matattu. Yesu ya yi wannan ya nuna abin da zai yi a dukan duniya sa’ad da ya zama Sarkin mulkin Allah.

Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance da daɗi a sabuwar aljanna a duniya! Yesu tare da waɗanda ya zaɓa za su yi sarauta a sama. Waɗannan masarauta za su kula da kowa a duniya kuma su tabbata cewa mutanen suna farin ciki. Bari mu ga abin da ya kamata mu yi domin Allah ya ba mu rai madawwami a sabuwar aljanna.

Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4; 5:9, 10; 14:1-3.