Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 116

Yadda Za Mu Rayu Har Abada

Yadda Za Mu Rayu Har Abada

KA SAN abin da wannan ƙaramar yarinya da abokananta suke karantawa? Hakika, wannan littafin ne da kake karantawa, Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki. Kuma suna karanta labarin da kake karantawa ne, “Yadda Za Mu Rayu Har Abada.”

Ka san abin da suke koya? Da farko, cewa muna bukatar mu koyi game da Jehobah da kuma Ɗansa Yesu idan muna so mu rayu har abada. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Wannan shi ne hanyar rayuwa har abada. Ka koyi game da Allah na gaskiya, da kuma Ɗan da ya aiko duniya, Yesu Kristi.’

Ta yaya za mu koyi game da Jehobah Allah da kuma Ɗansa Yesu? Hanya ɗaya ita ce ta karanta Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki daga farko zuwa ƙarshensa. Ya gaya mana game da Jehobah da kuma Yesu, ko ba haka ba ne? Kuma ya gaya mana game da abubuwa da suka yi da kuma waɗanda za su yi. Amma muna bukatar mu yi wani abu kuma ban da karanta wannan littafin.

Ka ga wannan littafin da yake ajiye a ƙasa? Littafi Mai Tsarki ne. Ka ce wani ya karanta maka inda aka ɗauko waɗannan labarun a Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki ya ba mu cikakken bayani da muke bukata domin mu bauta wa Jehobah a hanyar da take daidai kuma mu sami rai madawwami. Saboda haka ya kamata karatun Littafi Mai Tsarki ya zama jikinmu.

Amma muna bukatar mu yi wani abu kuma ban da koya game da Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi. Za mu iya saninsu sosai amma kuma ba za mu sami rai madawwami ba. Ka san abin da ya kamata mu yi kuma?

Muna bukatar mu yi abubuwa da muka koya. Ka tuna Yahuda Iskariyoti? Yana ɗaya daga cikin manzanni 12 da Yesu ya zaɓa. Yahuda yana da sani sosai game da Jehobah da Yesu. Amma me ya same shi? Bayan ɗan lokaci ya zama mai sonkai, ya bashe da Yesu ga abokanan gabansa domin tsaba 30 na azurfa. Saboda haka Yahuda ba zai sami rai madawwami ba.

Ka tuna Gahazi mutumin da muka koya game da shi a Labari na 69? Yana so ya sami kayaki da kuma kuɗi da ba na shi ba. Saboda haka ya yi ƙarya domin ya sami waɗannan abubuwa. Amma Jehobah ya yi masa horo. Kuma zai yi mana horo idan ba mu bi dokokinsa ba.

Amma da akwai mutanen kirki da suka bauta wa Jehobah da aminci. Muna so mu zama kamarsu, ko ba haka ba? Sama’ila misali ne mai kyau da za mu bi. Ka tuna kamar yadda muka gani a Labari 55, yana ɗan shekara huɗu ko biyar sa’ad da ya fara bauta wa Jehobah a mazauni. Ko nawa shekarunka ba ka yi ƙarami ba sosai ka bauta wa Jehobah.

Hakika, dukanmu muna so mu bi Yesu Kristi. Har sa’ad da yake yaro ma, kamar yadda muka gani a Labari na 87, ya kasance a cikin haikali yana magana da wasu game da Ubansa na samaniya. Ya kamata mu bi misalinsa. Bari mu gaya wa mutane da yawa game da Jehobah Allahnmu da Ɗansa, Yesu Kristi. Idan mun yi waɗannan abubuwa, za mu iya rayuwa har abada cikin sabuwar aljanna ta Allah a duniya.

Yohanna 17:3; Zabura 145:1-21.