Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 2

Za Ka Iya ‘Kusantar Allah’ da Gaske Kuwa?

Za Ka Iya ‘Kusantar Allah’ da Gaske Kuwa?

1, 2. (a) Me mutane da yawa za su ji ba zai yiwu ba, amma menene Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana? (b) Wace dangantaka ce ta kusa aka ba wa Ibrahim, kuma me ya sa?

YAYA za ka ji idan Mahaliccin sama da kasa ya ce game da kai, “Wannan abokina ne”? Ga mutane da yawa, wannan zai kasance abu ne da ba zai yiwu ba. Yaya kuwa taliki zai kulla abota da Jehovah Allah? Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da gaske cewa za mu iya kusantar Allah.

2 Ibrahim na zamanin dā, ya more irin wannan kusanci. Jehovah ya ce game da wannan kakan, “abokina.” (Ishaya 41:8, NW ) Hakika, Jehovah ya dauki Ibrahim abokinsa ne. An ba wa Ibrahim wannan dangantaka ta kusa ne domin “Ibrahim ya gaskata Allah.” (Yakub 2:23) A yau ma, Jehovah yana neman zarafi ya “manne” wa wadanda suke bauta masa domin kauna. (Kubawar Shari’a 10:15, NW ) Kalmarsa ta aririta: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.” (Yakub 4:8) A wadannan kalmomi mun ga gayyata da kuma alkawari.

3. Wace gayyata Jehovah ya gayyace mu, kuma ta hada da wane alkawari?

3 Jehovah ya gayyace mu mu matso kusa da shi. Yana shirye ya karbe mu mu zama abokanansa. A wannan lokacin kuma ya yi alkawarin cewa idan muka yi kokarin matsowa kusa da shi, shi ma zai yi haka. Zai kusace mu. Da haka za mu sa hannu a abu mai tamani—za mu san “asirin Ubangiji.” * (Zabura 25:14) Maganar ‘asiri’ muna yi da aboki na musamman ne.

4. Ta yaya za ka kwatanta aboki na kusa, kuma a wace hanya ce Jehovah ya tabbatar shi irin wannan aboki ne ga wadanda suka kusace shi?

4 Kana da aboki na kusa da za ka gaya wa asirinka? Irin wannan aboki ne da ya damu da kai. Ka amince da shi, domin ya tabbatar shi amini ne. Farin cikinka zai karu idan ka gaya masa batunka. Kunnensa mai tausayi yana rage zafin bakin cikinka. Har a lokacin da kamar ba wanda yake fahimtarka, shi yana yi. Hakanan, sa’ad da ka kusaci Allah, za ka zo ga samun Aboki na musamman wanda yake ganinka da tamani da gaske, wanda ya damu da kai da gaske, kuma ya fahimce ka sosai. (Zabura 103:14; 1 Bitrus 5:7) Ka dogara a gare shi sosai, domin ka sani cewa amini ne ga wadanda suka amince da shi. (Zabura 18:25) Duk da haka, wannan gatar kasancewa kusa da Allah ta yiwu ne domin shi ya sa ta yiwu.

Jehovah Ya Bude Hanya

5. Menene Jehovah ya yi domin ya sa ya yiwu mu kusace shi?

5 Idan aka bar mu, mu masu zunubi ba za mu taba kusantar Allah ba. (Zabura 5:4) Manzo Bulus ya rubuta: “Amma Allah yana shaidar kaunatasa garemu, da shi ke, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Romawa 5:8) Hakika, Jehovah ya shirya Yesu ya “bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Matta 20:28) Bangaskiyarmu ga hadayar fansa ta sa ya yiwu mu kusaci Allah. Tun da Allah ya “fara kaunacemu,” ya kafa mana tushen shiga dangantaka da shi.—1 Yohanna 4:19.

6, 7. (a) Ta yaya muka sani cewa Jehovah ba Allah ba ne boyayye kuma wanda ba za a san shi ba? (b) A wadanne hanyoyi ne Jehovah ya bayyana kansa?

6 Jehovah ya sake wani kokari: Ya bayyana mana kansa. A kowacce dangantaka, kusanta ta dangana ne bisa sanin mutumin da kuma son halayensa da hanyoyinsa. Idan Jehovah Allah ne da yake boye, wanda ba za a iya saninsa ba, ba za mu taba kusantarsa ba. Duk da haka, bai boye kansa ba, yana so mu san shi. (Ishaya 45:19) Bugu da kari, abin da ya bayyana game da kansa yana samuwa ga kowa, har ga mu wadanda ba a dauke mu kome ba a duniya.—Matta 11:25.

Jehovah ya bayyana kansa ta wajen abin da ya halitta da kuma rubutacciyar Kalmarsa

7 Ta yaya Jehovah ya bayyana kansa gare mu? Abin da ya halitta sun nuna wasu bangaren mutuntakarsa—yawan ikonsa, zurfin hikimarsa, yawaitar kaunarsa. (Romawa 1:20) Amma bayyana kansa da Jehovah ya yi bai tsaya daga abin da ya halitta ba. Babban Mai Magana, ya yi tanadin rubutaccen wahayi game da kansa a cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki.

Ganin “Jamalin Ubangiji”

8. Me ya sa za a iya cewa Littafi Mai Tsarki kansa tabbaci ne na kaunar Jehovah gare mu?

8 Littafi Mai Tsarki kansa tabbaci ne na kaunar Jehovah gare mu. A cikin Kalmarsa, ya bayyana kansa a kalmomin da za mu fahimta—ya tabbatar da cewa ba kawai yana kaunarmu ba amma yana so mu san shi kuma mu kaunace shi. Abin da muka karanta a wannan littafi mai tamani ya taimake mu mu ga “jamalin Ubangiji” kuma ya motsa mu mu kusace shi. (Zabura 90:17) Bari mu tattauna wasu hanyoyi masu dadada zuciya da Jehovah ya bayyana kansa a cikin Kalmarsa.

9. Wadanne ne wasu misalai na furci na kai tsaye a cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna halayen Allah?

9 Nassosi suna dauke da furci da yawa na kai tsaye da suke lissafa halayen Allah. Ka lura da wasu misalai. “Ubangiji yana son shari’a.” (Zabura 37:28) Allah “mafifici ne shi cikin iko.” (Ayuba 37:23) “Allah mai-aminci.” (Kubawar Shari’a 7:9) “Yana da hikima a zuciya.” (Ayuba 9:4 ) “Ubangiji ya gibta a gabansa, ya furta kuma, Ubangiji, Ubangiji, Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinkai da gaskiya.” (Fitowa 34:6) “Nagari ne kai, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa kuwa.” (Zabura 86:5) Kuma, kamar yadda aka fada a babi na baya, hali daya ya fi shahara: “Allah kauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Yayin da kake bimbini bisa wadannan halaye, ba ka sha’awar kusantar wannan Allah da ba shi da na biyunsa?

Littafi Mai Tsarki yana taimaka mana mu kusaci Jehovah

10, 11. (a) Don ya taimake mu mu ga mutuntakarsa sosai, menene Jehovah ya hada cikin Kalmarsa? (b) Wane misali ne na Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu kaga ikon Allah yana aiki?

10 Kari ga gaya mana halayensa, Jehovah cikin kauna ya hada cikin Kalmarsa takamammun misalai na wadannan halaye. Irin wannan labaran suna zana hoton zuci da suke taimaka mana mu ga bangarori na mutuntakarsa sosai. Wannan kuma yana sa mu kusace shi. Ga wani misali.

11 Wani abu ne ka karanta cewa Allah “mai-karfi ne cikin iko.” (Ishaya 40:26) Wani ne kuma dabam ka karanta game da yadda ya ceci Isra’ilawa a Jar Teku kuma ya ciyar da al’ummar a daji na shekara 40. Za ka iya zana hoton zuci na mafadacin ruwa yana tsagewa biyu. Za ka iya tunanin al’ummar—watakila duka 3,000,000—suna tafiya a kan busashiyar kasa a daben tekun, daskararren ruwa yana tsaye kamar ganuwa a gefen hagu da na dama. (Fitowa 14:21; 15:8) Za ka ga tabbacin kāriyar Allah a cikin daji. Ruwa ya tumbatso daga dutse. Abinci, da ya yi kama da fararen iri suka bayyana a kasa. (Fitowa 16:31; Litafin Lissafi 20:11) A nan Jehovah bai nuna kawai cewa yana da iko ba amma yana amfani da shi domin mutanensa. Ba karfafa ba ce mu sani cewa addu’o’inmu suna zuwa wajen Allah mai iko wanda “mafakanmu ne da karfinmu, taimako ne na kusa-kusa cikin wahala”?—Zabura 46:1.

12. Ta yaya Jehovah yake taimaka mana mu “fahimce” shi a kalmomin da za mu iya fahimta?

12 Jehovah, wanda ruhu ne, ya taimaka mana sosai mu san shi. Da yake mutane ne, iyakarmu duniya ta zahiri ne saboda ba ma iya ganin duniya ta ruhaniya. Don haka idan Allah zai kwatanta mana kansa a kalmomi na ruhu zai kasance ne kamar kana kokari ne ka kwatanta siffarka, kamar su launin idanunka ko kuma tawadar Allah ga wanda aka haife shi makaho. Maimakon haka, Jehovah ya taimaka mana mu “fahimce” shi a kalmomin da za mu fahimta. A wasu lokatai, ya yi amfani da misalai da kuma kwatanci, ya kwatanta kansa da abubuwa da muka sani. Ya kwatanta kansa ma kamar yana da wasu gabobi na mutane. *

13. Wane hoton zuci ne Ishaya 40:11 ta zana, kuma ta yaya wannan ya shafe ka?

13 Ka lura da kwatancin Jehovah da ke cikin Ishaya 40:11: “Za ya yi kiwon garkensa kamar makiyayi, za ya tattara ’ya’yan tumaki a hannunsa, ya dauke su a cikin kirjinsa.” A nan an kwatanta Jehovah da makiyayi wanda yake daukan ’ya’yan tumaki da “hannunsa.” Wannan ya nuna iyawar Jehovah ya kāre kuma ya tallafa wa mutanensa, har da marasa karfi. Za mu samu kwanciyar rai cikin hannunsa mai karfi, idan muna da aminci a gare sa, ba zai taba yasar da mu ba. (Romawa 8:38, 39) Makiyayi Mafi Girma yana daukan dan rago a “kirjinsa”—furci da yake nufin wata kalmasa da ke kwancewa a saman riga, inda wani lokaci makiyayi yake daukan dan rago sabon haihuwa. Saboda haka an tabbatar mana cewa Jehovah yana kaunarmu kuma ya damu da mu. Daidai ne mu so mu kusace shi.

“Dan Ya Ke Nufa Shi Bayyana Masa”

14. Me ya sa za a iya cewa Jehovah ya bayyana asirinsa sosai ta wajen Yesu?

14 A cikin Kalmarsa, Jehovah ya bayyana asirinsa sosai ta wajen Dansa da yake kauna, Yesu. Babu wani wanda zai nuna tunanin Allah da kuma yadda yake ji sosai ko kuma ya bayyana Shi fiye da yadda Yesu ya yi. Ban da haka, Dan farin yana tare da Ubansa kafin a halicci wasu halittun ruhu da na sararin samaniya da ake gani. (Kolossiyawa 1:15) Yesu ya san Jehovah kwarai. Shi ya sa ya ce: “Ba wanda ya sansance ko wanene Dan, sai Uban; ba kuwa wanda ya sansance ko wanene Uban, sai Dan, da dukan wanda Dan ya ke nufa shi bayyana masa.” (Luka 10:22) Lokacin da yake duniya, shi mutum, Yesu ya bayyana Ubansa a hanyoyi biyu masu muhimmanci.

15, 16. A wadanne hanyoyi ne Yesu ya bayyana Ubansa?

15 Na farko, koyarwar Yesu ta taimake mu mu san Ubansa. Yesu ya kwatanta Jehovah a kalmomin da za su taba zukatanmu. Alal misali, wajen bayyana Allah mai jinkai wanda yake marabtar masu zunubi da suka tuba, Yesu ya kwatanta Jehovah da uba mai gafartawa wanda ya motsa da ganin dansa almubazzari yana komowa sai ya sheka da gudu, ya fadā masa a wuya, ya yi ta yi masa sumba. (Luka 15:11-24) Yesu kuma ya kwatanta Jehovah cewa Allah ne wanda yake “jawo” mutane masu zukatan kirki domin yana kaunar kowannensu. (Yohanna 6:44) Ya sani idan karamin gwarare ya fadi kasa. Yesu ya yi bayani: “Kada ku ji tsoro fa; kun fi gwarare masu-yawa daraja.” (Matta 10:29, 31) Babu shakka muna da tabbacin muna so mu kusaci irin wannan Allah mai kula.

16 Na biyu, misalin Yesu ya nuna yadda Jehovah yake. Yesu ya yi koyi da Ubansa sarai har ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yohanna 14:9) Saboda haka, sa’ad da muke karatun Linjila game da Yesu—juyayin da ya yi da kuma hanyar da ya bi da wasu—a wata hanya muna ganin hoto ne mai rai na Ubansa. Babu yadda Jehovah zai bayyana mana halayensa fiye da haka kuma. Me ya sa?

17. Ka ba da misalin abin da Jehovah ya yi domin ya taimake mu mu fahimci yadda yake.

17 Alal misali: A ce kana so ka bayyana abin da kirki yake nufi. Za ka iya bayyana shi da kalmomi. Amma idan za ka iya nuna wani yana yin abin kirki kuma ka ce, “Wannan shi ne misalin abin kirki,” sai kalmar “kirki” ta kara ma’ana kuma ta kasance da saukin fahimta. Jehovah ya yi abu kusan haka ya taimake mu mu fahimci yadda yake. Hade da bayyana kansa cikin kalmomi, ya yi mana tanadin rayayyen misali na Dansa. A wurin Yesu, ana ganin halayen Allah sosai. Ta cikin kwatancin Yesu na Lingila, Jehovah yana cewa ne: “Wannan haka nake.” Yaya hurarren tarihi ya kwatanta Yesu lokacin da yake duniya?

18. Ta yaya Yesu ya nuna iko, shari’a, da kuma hikima?

18 Halaye hudu na musamman na Allah, Yesu ya nuna su da kyau. Yana da iko bisa cututtuka, yunwa, har da mutuwa. Duk da haka, ba kamar mutane ba masu son kai wadanda suke barna da ikonsu, shi bai taba yin amfani da ikonsa na yin mu’ujiza domin kansa ba ko kuma domin ya cuci wasu. (Matta 4:2-4) Yana kaunar shari’a. Zuciyarsa ta cika da fushi da ya ga ’yan kasuwa suna yi wa mutane ha’inci. (Matta 21:12, 13) Ya bi da matalauta da kuma wadanda ake wahalar da su babu wariya, ya taimaki wadannan su sami “hutawa” ga ransu. (Matta 11:4, 5, 28-30) A koyarwar Yesu ‘wanda ya fi Sulemanu girma’ da akwai hikima wadda babu irin ta. (Matta 12:42) Amma Yesu bai taba fahariya ba domin hikimarsa. Kalmominsa sun taba zukatan talakawa, domin koyarwarsa a bayyane take, tana da sauki, kuma tana yiwuwa.

19, 20. (a) Ta yaya Yesu misali ne mafi kyau na kauna? (b) Yayin da muke karatu, muke bimbini game da misalin Yesu, me za mu tuna da shi?

19 Yesu fitaccen misali ne na kauna. A cikin dukan hidimarsa, ya nuna kauna a hanyarta dabam dabam, hade da juyayi da kuma tausayi. Ba ya kallon wahalar wasu, ba tare da ya tausaya musu ba. Sau da yawa, wannan tausayin ya motsa shi ga aikatawa. (Matta 14:14) Ko da yake ya warkar da marasa lafiya kuma ya ciyar da mayunwata, Yesu ya nuna tausayi a hanya mafi muhimmanci. Ya taimake wasu su kaunaci gaskiyar Mulkin Allah, kuma su karbe ta, wadda za ta kawo wa ’yan Adam albarka ta dindindin. (Markus 6:34; Luka 4:43) Fiye da kome, Yesu ya nuna kauna ta sadaukar da kai ta wajen ba da kansa da son rai domin wasu.—Yohanna 15:13.

20 Abin mamaki ne cewa mutane na dukan tsararraki da kuma kowacce kabila suna so su matso kusa da wannan mutum wanda yake da kauna da kuma juyayi? (Markus 10:13-16) Ko da yake, yayin da muke karatu game da shi kuma muke yin bimbini a kan misalin Yesu, bari mu rike a zuciyarmu cewa a cikin Dansa muna ganin kamanin Ubansa sosai.—Ibraniyawa 1:3.

Abin Taimako Wajen Nazari

21, 22. Menene yake kunshe cikin neman Jehovah, kuma menene wannan abin taimako wajen nazari ya kunsa don ya taimake mu wajen yin haka?

21 Ta wajen bayyana kansa sosai a cikin Kalmarsa, Jehovah ya nuna mana cewa yana so mu kusace shi. Amma, bai tilasta mana mu bidi yardajjiyar dangantaka da shi ba. Hakkinmu ne mu nemi Jehovah “tun yana samuwa.” (Ishaya 55:6) Neman Jehovah ya kunshi sanin halayensa da kuma hanyoyinsa kamar yadda aka bayyana su cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan abin taimako wajen nazari da kake karantawa an shirya ne domin ya taimake ka wajen yin haka.

22 Za ka lura cewa wannan littafin an raba shi kashi kashi da suka yi daidai da halaye hudu na musamman na Jehovah: iko, shari’a, hikima, da kuma kauna. Kowanne kashi ya fara ne da takaitaccen bayani game da wannan halin. Babobi na gaba sun tattauna yadda Jehovah ya nuna wadannan halaye a bangarori dabam dabam. Kowanne sashe yana dauke da babi da yake nuna yadda Yesu ya ba da misalin wannan halin, da wani babi kuma wanda yake bincika yadda mu za mu nuna wannan halin a rayuwarmu.

23, 24. (a) Ka ba da bayani bisa fasali na musamman “Tambayoyi don Bimbini.” (b) Ta yaya bimbini yake taimaka mana mu kusaci Allah?

23 Daga wannan babin, akwai fasali na musamman da ke da jigo “Tambayoyi don Bimbini.” Alal misali, ka duba akwati da ke shafi na 24. Nassosin da kuma tambayoyin ba a tsara su domin maimaita abin da ke cikin babin ba. Maimakon haka, manufarsu shi ne su taimake ka ka yi bimbini a kan wasu abubuwa masu muhimmanci na wannan batu. Ta yaya za ka yi amfani da wannan da kyau? Ka dubi kowanne cikin ayoyin da aka rubuta, kuma ka karanta ayoyin a hankali. Sa’an nan ka bincika tambaya da take kan kowacce aya. Ka yi bimbini a kan amsoshin. Kana iya kara bincike. Ka yi wa kanka karin tambayoyi: ‘Menene wannan yake gaya mini game da Jehovah? Ta yaya ya shafi rayuwata? Ta yaya zan yi amfani da shi in taimake wasu?’

24 Irin wannan bimbinin zai taimake mu mu kusaci Jehovah sosai. Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya hada bimbini da zuciya. (Zabura 19:14) Sa’ad da muka yi bimbini a nuna godiya ga abin da muka koya game da Allah, sanin zai shiga zuciyarmu ta alama, a inda zai taba tunaninmu, ya motsa mu, kuma a karshe ya motsa mu ga aikatawa. Kaunarmu ga Allah za ta karu, kuma wannan kaunar za ta motsa mu mu so yin abin da zai faranta masa rai tun da Abokinmu ne da muke kauna. (1 Yohanna 5:3) Don mu shiga irin wannan dangantakar, dole ne mu san halayen Jehovah da kuma hanyoyinsa. Da farko, bari mu tattauna bangaren mutuntakar Allah da ya ba da dalili wanda zai sa mu kusace shi—tsarkakarsa.

^ sakin layi na 3 Kalmar Ibrananci da aka yi amfani da ita a nan tana cikin Amos 3:7 ma, wadda ta ce Ubangiji Jehovah na bayyana “asirinsa” ga bayinsa, yana sanar da su a kan lokaci abin da yake da niyyar yi.

^ sakin layi na 12 Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar fuskar Allah, idanunsa, kunnuwansa, hancinsa, bakinsa, hannunsa, da kuma kafafuwansa. (Zabura 18:15; 27:8; 44:3; Ishaya 60:13; Matta 4:4; 1 Bitrus 3:12) Irin wannan furci na kwatanci kada a dauke shi a zahiri, kamar yadda ba za mu dauki kwatanta Jehovah da “dutse” ko kuma “garkuwa” a zahiri ba.—Kubawar Shari’a 32:4, NW; Zabura 84:11.