Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 3

“Mai-Tsarki, Mai-Tsarki, Mai-Tsarki ne, Ubangiji”

“Mai-Tsarki, Mai-Tsarki, Mai-Tsarki ne, Ubangiji”

1, 2. Wane wahayi ne annabi Ishaya ya gani, kuma menene yake koya mana game da Jehovah?

ISHAYA ya cika da mamaki, da daukaka, da tsoron Allah domin abin da ya gani a gabansa—wahayi daga Allah. Kamar a zahiri! Daga baya Ishaya ya rubuta cewa da gaske ya “ga Ubangiji” a zaune a kan kursiyi. Sitirar Jehovah ta cika haikali na Urushalima.—Ishaya 6:1, 2.

2 Ishaya kuma ya cika da tsoro domin abin da ya ji—waka mai karfi ta cika haikali har sai da tushen ya girgiza. Wakar tana fitowa ne daga mala’iku masu babban matsayi, halittu na ruhu. Muryoyinsu ya furta kalmomin daukaka: “Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki ne, Ubangiji mai-runduna: dukan duniya cike ta ke da daukakarsa.” (Ishaya 6:3, 4) Rera “mai-tsarki” sau uku ya ba ta nanaci na musamman da ya dace, domin tsarkaka ta Jehovah ta fi gaban a bayyana. (Ru’ya ta Yohanna 4:8) An nanata tsarkakar Jehovah a dukan cikin Littafi Mai Tsarki. Darurruwan ayoyi sun hada sunansa da kalmar nan “tsarki” da kuma “tsarkaka.”

3. Ta yaya kuskure game da tsarkakar Jehovah take sa mutane su guji Allah maimakon su yi kusa da shi?

3 Don haka, daya daga cikin abubuwa na farko da Jehovah yake so mu fahimta shi ne cewa shi mai tsarki ne. Duk da haka, da yawa a yau wannan yana koransu. Wasu mutane cikin kuskure suna hada tsarkaka da adalcin kai ko kuma tsarkaka ta karya. Mutane da suke kokawa da jin ba su da daraja, tsarkakar Allah za ta rika tsoratar da su maimakon rinjayarsu. Za su tsorata cewa ba za su taba cancanta su kusaci wannan Allah mai-tsarki ba. Saboda haka, da yawa suna guje wa Allah domin tsarkakarsa. Wannan abin bakin ciki ne, domin tsarkakar Allah da gaske ita ce dalilin matsowa kusa da shi. Me ya sa? Kafin mu amsa wannan tambayar, bari mu tattauna abin da tsarkaka ta gaskiya take nufi.

Mecece Tsarkaka?

4, 5. (a) Mecece tsarkaka take nufi, kuma mecece ba ta nufa ba? (b) A wadanne hanyoyi biyu ne masu muhimmanci Jehovah ya kasance “kebabbe”?

4 Domin Allah mai tsarki ne ba ya nufin cewa ya gamsu da kansa kawai, mai fahariya ne, ko kuma mai ba’a ne ga wasu. Maimakon haka, yana kyamar wadannan halaye. (Misalai 16:5; Yakub 4:6) To, menene ainihi kalmar nan “tsarki” take nufi? A Ibrananci na Littafi Mai Tsarki, kalmar an samo ta ne daga furci da take nufin “kebabbe.” A bauta, “tsarki” yana nufin abin da aka kebe daga amfani na yau da kullum, ko kuma da aka rike don bauta. Tsarkaka kuma na ba da ma’ana sosai ta tsabta. Ta yaya wannan kalmar take ga Jehovah? Tana nufi ne cewa “kebabbe” ne da nesa daga gare mu ajizai?

5 Ba haka ba ne. “Mai-tsarki na Isra’ila,” Jehovah ya kwatanta kansa cewa yana ‘tsakiyar’ mutanensa, ko da yake masu zunubi ne su. (Ishaya 12:6; Hosea 11:9) Saboda haka tsarkakarsa ba ta sa ya yi nisa ba. To, ta yaya ne yake “kebabbe”? A hanyoyi biyu masu muhimmanci. Na daya, kebabbe ne daga dukan halittu saboda shi kadai ne Madaukaki Duka. Tsabtarsa cikakkiya ce ba ta da iyaka. (Zabura 40:5; 83:18) Na biyu, Jehovah kebabbe ne gabaki daya daga zunubi, kuma wannan abin karfafa ne. Me ya sa?

6. Me ya sa za mu sami karfafa daga kebewar Jehovah gabaki daya daga zunubi?

6 Muna rayuwa ne a duniya da ake rashin tsarki na gaske. Kome na jama’a da suke a ware daga Allah, ya gurbata a wata hanya, zunubi ya lalata shi da kuma ajizanci. Dukanmu muna bukatar mu yaki zunubi da ke cikinmu. Kuma dukanmu muna cikin hadarin da zunubi zai iya nasara a kanmu idan muka sake. (Romawa 7:15-25; 1 Korinthiyawa 10:12) Jehovah ba ya cikin irin wannan hadarin. Tun da kebabbe ne daga zunubi, digon zunubi ba zai taba taba shi ba. Wannan ya sake tabbatar mana cewa Jehovah Uba ne nagari, domin yana nufin cewa matabbaci ne kwarai. Ba kamar ubanni ba na mutane masu zunubi, Jehovah ba zai taba zama marar gaskiya ba, marar kamewa, ko kuma azzalumi. Tsarkakarsa ta sa irin wannan abin ba zai taba yiwuwa ba. A wasu lokatai Jehovah ya yi rantsuwa da tsarkakarsa, wannan ya sa rantsuwar abin dogara. (Amos 4:2) Wannan ba tabbaci ba ne?

7. Me ya sa za a iya cewa tsarkaka yanayi ne na Jehovah?

7 Tsarkaka yanayin Jehovah ne. Me wannan yake nufi? Alal misali: Ka lura da kalmomin nan “dan Adam” da kuma “ajizi.” Ba za ka iya kwatanta na farkon ba, ba tare da amfani da na biyun ba. Ajizanci ya cika mu kuma yana rinjayar dukan abin da muke yi. Yanzu ka lura da wannan kalmomi biyun masu bambanci—“Jehovah” da “tsarki.” Tsarkaka ta cika Jehovah. Kome game da shi mai tsabta ne, mai kyau, kuma nagari. Ba za mu zo ga ainihin sanin Jehovah ba idan ba tare da fahimtar wannan muhimmiyar kalmar ba—“tsarki.”

“Mai-Tsarki ga Ubangiji”

8, 9. Menene ya nuna cewa Jehovah yana taimakon mutane ajizai su zama masu tsarki a karamar hanya?

8 Tun da Jehovah yana rike da halin tsarki, za a iya cewa shi ne tushen tsarkaka. Bai boye wannan halin ba cikin son kai; ya ba wa wasu, kuma ya yi hakan hannu sake. Sa’ad da Allah ya yi magana da Musa ta wajen mala’ika a kurmi mai ci da wuta, har kasar wajen ta tsarkaka domin nasabarta da Jehovah!—Fitowa 3:5.

9 Mutane ajizai za su iya zama masu tsarki da taimakon Jehovah? Hakika, a karamar hanya. Allah ya ba wa mutanensa Isra’ila damar zama “al’umma mai-tsarki.” (Fitowa 19:6) Ya albarkaci wannan al’ummar da tsarin bauta mai tsarki, mai tsabta, kuma mai kyau. Tsarki ne jigon da ya bayyana sau da yawa cikin Dokar Musa. Hakika, babban firist yana sanye da allo na sahihiyar zinariya a gaban rawaninsa, inda ko waye zai ga walkiyarta. Kuma an zana rubutu irin ta hatimi a kansa: “Mai-tsarki na Ubangiji.” (Fitowa 28:36) Saboda haka mizani mai girma na tsabta zai bambance bautarsu, hakika, hanyar rayuwarsu. Jehovah ya gaya musu: “Sai ku zama masu-tsarki: gama ni Ubangiji Allahnku mai-tsarki ne.” (Leviticus 19:2) Muddin Isra’ilawa suna raye bisa gargadin Allah iyakar abin da zai yiwu ga mutane ajizai, masu tsarki ne a karamar hanya.

10. Idan ya zo ga tsarkaka, wane bambanci ne yake tsakanin Isra’ila ta dā da kuma al’ummai da suka kewaye su?

10 Wannan nanaci a kan tsarkaka bambanci ne kwarai da bautar wasu al’ummai da suka kewaye Isra’ila. Wadannan al’umman arna suna bauta wa alloli wadanda wanzuwarsu ma karya ce da rudu, alloli da aka kwatanta su masu nuna karfi ne, ’yan hadama, kuma karuwai. Ba su da tsarki ta kowacce hanya. Bautar irin wadannan alloli tana sa mutane su zama marasa tsarki. Saboda haka, Jehovah ya yi wa mutanensa kashedi su ware kansu daga bautar arna da kuma ayyukan addinansu marasa tsabta.—Leviticus 18:24-28; 1 Sarakuna 11:1, 2.

11. Ta yaya tsarkakar kungiyar Jehovah ta samaniya ta bayyana (a) a mala’iku? (b) a mala’iku seraf? (c) a Yesu?

11 Har a yanayi mafi kyau ma, al’umma da Jehovah ya zaba ta Isra’ila ta dā ta nuna tsarkaka kadan ne kawai na kungiyar Allah ta samaniya. Miliyoyin ruhohi wadanda suke bauta wa Allah da aminci an kira su “rundunan tsarkakansa.” (Yahuda 14) Suna nuna hasken, kyakkyawar tsarkakar Allah. Ka tuna kuma da mala’iku seraf da Ishaya ya gani a wahayi. Abin da suke fada a wakarsu ta nuna cewa wadannan halittu na ruhu masu girma suna muhimmin aiki wajen sanar da tsarkakar Jehovah a dukan sararin samaniya. Wani halittar ruhu, da ya fi dukan wadannan—shi ne makadaici Dan Allah. Yesu shi ne mafi girma wajen nuna tsarkakar Jehovah. Daidai ne, an san shi da “Mai-tsarki na Allah.”—Yohanna 6:68, 69.

Suna Mai Tsarki, Ruhu Mai Tsarki

12, 13. (a) Me ya sa aka kwatanta sunan Allah daidai da tsarki? (b) Me ya sa dole ne a tsarkake sunan Allah?

12 To, sunan Allah fa? Kamar yadda muka gani a Babi na 1, sunan ba lakabi ba ne ko kuma lamba. Yana wakiltan Jehovah Allah, ya kunshi dukan halayensa. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “sunansa Tsarki ne.” (Ishaya 57:15) A Dokar Musa babban zunubi ne a saba wa sunan Allah. (Leviticus 24:16) Ka lura da abin da Yesu ya sa farko a cikin addu’a: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) A tsarkake abu yana nufin a kebe shi domin ibada, a rika daukarsa da tsarki. Amma me ya sa abin da yanayinsa ma mai tsabta ne kamar sunan Allah zai bukaci a tsarkake shi?

13 An tuhumi sunan Allah mai tsarki, an lalata sunan da karya da tsegumi. A Adnin, Shaidan ya yi karya game da Jehovah wanda ya nuna cewa Jehovah ba Mamallaki ba ne mai gaskiya. (Farawa 3:1-5) Tun daga lokacin, Shaidan—mai mulkin wannan duniyar, marar tsarki—ya tabbata cewa wannan karya game da Allah ta yadu. (Yohanna 8:44; 12:31; Ru’ya ta Yohanna 12:9) Addinai suna kwatanta Allah cewa mugun sarki ne, yana nesa, kuma azzalumi ne. Suna da’awar suna da goyon bayansa cikin zubar da jini a yake-yakensu. Sau da yawa ana bai wa ra’i na bayyanau darajar ayyukan halitta da Allah ya yi. Hakika, an bata sunan Allah kwarai da gaske. Dole ne a tsarkake shi; dole ne a mai da masa da darajarsa. Muna da muradin a tsarkake sunan Allah kuma a kunita mallakarsa, muna farin ciki a ko menene za mu yi a wannan kuduri mai girma.

14. Me ya sa ake kiran ruhun Allah mai tsarki, kuma me ya sa sabo ga ruhu mai tsarki yana da hadari?

14 Da akwai abin da yake da nasaba sosai da Jehovah da a kan iya kira mai tsarki—ruhunsa, ko kuma ikon aiki. (Farawa 1:2) Jehovah ya yi amfani da karfinsa da ya fi kome ya kammala nufe-nufensa. Dukan abin da Allah ya yi, yana yi ne a hanya mai tsarki, mai kyau, mai tsabta, daidai ne aka kira ikon aikinsa ruhu mai tsarki ko kuma ruhun tsarkaka. (Luka 11:13; Romawa 1:4) Yi wa ruhu mai tsarki sabo, wanda ya kunshi saba wa nufin Jehovah da gangan, yana nufin zunubi da ba a gafartawa.—Markus 3:29.

Abin da Ya Sa Tsarkakar Jehovah Take Jawo Mu Gare Shi

15. Me ya sa kasancewa da tsoro irin na ibada amsa ce da ta dace da tsarkakar Jehovah, kuma menene irin wannan tsoron ya kunsa?

15 Ba shi da wuya a fahimci abin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi dangantaka tsakanin tsarkakar Allah da kuma tsoro na ibada daga mutum. Alal misali, Zabura 99:3 ta ce: “Bari su yi yabon sunanka mai-girma mai-ban razana: Mai-tsarki ne shi.” Wannan razana kuwa, ba firgita ba ce. Maimakon haka, tsoro ne na ibada, daraja ce a babbar matsayinta. Daidai ne mu ji hakan, tun da tsarkakar Jehovah ta fi nesa da mu. Tsabtacce mai haskaka, mai daukaka. Duk da haka, bai kamata mu guje shi ba. Maimakon haka, daukaka tsarkakar Allah yadda ta dace za ta jawo mu kusa da shi. Me ya sa?

Kyau yana rinjayarmu, haka ma ya kamata tsarkaka ta yi

16. (a) Ta yaya tsarkaka take da alaka da kyau? Ka ba da misali. (b) Ta yaya kwatanci na wahayi na Jehovah ya nanata tsabta, kyau da kuma haske?

16 Abu daya shi ne, Littafi Mai Tsarki ya dangana tsarkaka da kyau. A Zabura 96:6, mun karanta game da wuri mai tsarki na Allah “karfi da jamali suna cikin tsatsarkan wurinsa.” Jamali yana rinjaya. Alal misali, dubi hoto da yake shafi na 33. Wannan yanayin bai rinjaye ka ba? Me ya sa yake da ban sha’awa? Ka lura da yadda ruwan yake da kyau. Har iskar ma dole ne ta kasance da tsabta, kuma gajimare yana da kyau kuma haske yana haskakawa. A yanzu, idan aka lalata wannan yanayi—tabkin ya cika da juji, itatuwa da duwatsu an bata su da rubuce-rubuce, iskar kuma ta cika da hayaki—ba zai rinjaye mu ba kuma; za mu guje shi. Muna danganta kyau da tsabta da kuma haske. Wadannan kalmomin za a iya amfani da su wajen kwatanta tsarkakar Jehovah. Ba mamaki da kwatancin Jehovah na wahayi yake rinjayarmu! Yana haskakawa, yana walkiya kamar duwatsu masu daraja, yana haske kamar wuta ko kuma karafa masu tamani—haka kyan Allah mai tsarki yake.—Ezekiel 1:25-28; Ru’ya ta Yohanna 4:2, 3.

17, 18. (a) Ta yaya wahayin Ishaya ya taba shi da farko? (b) Yaya Jehovah ya yi amfani da mala’ika seraf ya karfafa Ishaya, kuma menene muhimmancin abin da mala’ikan ya yi?

17 Amma, ya kamata tsarkaka ta Allah ta sa mu ji muna kasa da shi ne? Hakika, amsar E, ce. Tun da, muna kasa da Jehovah—wannan ma rage magana ce kwarai. Sanin wannan ya kamata ne ya ware mu daga gare shi? Ka dubi yadda Ishaya ya ji, da jin seraf suka sanar da tsarkakar Jehovah. “Sa’annan na ce, Kaitona! gama na lalace; da shi ke ni mutum mai-lebuna marasa-tsarki ne, ina kuwa zaune a tsakiyar mutane masu-lebuna marasa-tsarki: gama idanuna suna ga Sarki mai runduna.” (Ishaya 6:5) Hakika, tsarkakar Jehovah da ba ta da iyaka ta nuna wa Ishaya yadda yake mai zunubi kuma ajizi. Da farko, wannan amintaccen mutumin ya razana. Amma Jehovah bai kyale shi a wannan yanayin ba.

18 Mala’ika seraf ya karfafa annabin. Ta yaya? Wannan ruhu mai daukaka ya yi firiya zuwa bagadi, ya dauko garwashi, kuma ya taba lebunan Ishaya da shi. Wannan za ka ji yana da zafi maimakon karfafawa. Amma, ka tuna cewa wannan wahayi ne, da yake cike da ma’ana ta alama. Ishaya, Bayahude mai aminci ya san cewa ana yin hadaya kowacce rana a bagadi na haikali domin a nemi gafarar zunubi. Kuma mala’ikan ya tunasar da annabin cewa ko da yake shi ajizi ne, “mai-lebuna marasa-tsarki,” zai iya kasancewa da tsarki a gaban Allah. * Jehovah yana shirye ya dauki ajizi, mutum mai zunubi da tsarki—akalla a karamar hanya.—Ishaya 6:6, 7.

19. Ta yaya za mu iya zama masu tsarki a karamar hanya, ko da yake muna ajizai?

19 Haka yake a yau. Dukan wadancan hadayu da aka mika a kan bagadi na Urushalima hoto ne na abu babba da ke zuwa—hadaya daya kamiltacciya, da Yesu Kristi ya mika a shekara ta 33 A.Z. (Ibraniyawa 9:11-14) Idan da gaske mun tuba daga zunubanmu, mun gyara hanyarmu da ba ta dace ba, kuma muka ba da gaskiya a wannan hadayar, an gafarta mana. (1 Yohanna 2:2) Mu ma za mu iya kasancewa da tsabta a gaban Allah. Saboda haka, manzo Bitrus ya tunasar da mu: “An rubuta, Ku za ku zama masu-tsarki; gama ni mai-tsarki ne.” (1 Bitrus 1:16) Ka lura da cewa Jehovah bai ce dole mu zama masu tsarki kamarsa ba. Bai taba bukatar abin da ba zai yiwu ba a gare mu. (Zabura 103:13, 14) Maimako, Jehovah ya ce mana mu zama masu tsarki domin shi ma mai tsarki ne. Tun da mu “ ’ya’ya kaunatattu” ne, muna kokarin mu yi koyi da shi iyakar gwargwadon iyawarmu mu mutane ajizai. (Afisawa 5:1) Saboda haka, iya zama tsarkaka aba ce da za a ci gaba da yi. Yayin da muke girma a ruhaniya, muna kokarin “kāmala tsarki” kowacce rana.—2 Korinthiyawa 7:1.

20. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu fahimci cewa za mu iya kasancewa da tsabta a idanun Allahnmu mai tsarki? (b) Yaya ya taba Ishaya da ya fahimci cewa an gafarta masa zunubansa?

20 Jehovah, Allah mai tsarki, yana kaunar abin da yake nagari kuma mai tsabta. Yana kyamar zunubi. (Habakkuk 1:13) Amma ba ya kyamarmu. Idan muka dauki zunubi kamar yadda ya dauke shi—muna kin abin da ke munana, muna kaunar abin da ke mai kyau—kuma mu yi kokari mu bi kamiltaccen sawun Kristi Yesu, Jehovah zai gafarta mana zunubanmu. (Amos 5:15; 1 Bitrus 2:21) Sa’ad da muka fahimci cewa za mu iya kasancewa da tsabta a idanun Allahnmu mai tsarki, zai iya taba mu kwarai. Ka tuna cewa, tsarkakar Jehovah da farko ta tunasar da Ishaya rashin tsarkinsa. Ya yi kuka: “Kaitona!” Amma da ya fahimci cewa an gafarta masa zunubansa, ra’ayinsa ya canja. Da Jehovah ya nemi wanda zai ba da kai ya aika, Ishaya ya amsa ba tare da bata lokaci ba, ko da yake bai san abin da zai kunsa ba. Ya daga murya: “Ga ni; ka aike ni.”—Ishaya 6:5-8.

21. Menene tushen tabbacinmu cewa za mu iya gina halaye na tsarkaka?

21 An halicce mu a kamanin Allah mai tsarki, an ba mu dabi’a da kuma fahimtar abubuwa na ruhaniya. (Farawa 1:26) Dukanmu muna da iyawa na zama tsarkaku. Yayin da muke kokari mu koyi tsarkaka, Jehovah zai yi farin ciki ya taimaka mana. A wannan hanyar za mu kusaci Allahnmu mai tsarki. Bugu da kari, yayin da muka bincika halayen Jehovah a babobi da suke gaba, za mu ga cewa da akwai dalilai masu karfi da yawa na kusantarsa!

^ sakin layi na 18 Furcin nan “mai-lebuna marasa-tsarki” ya dace, domin lebuna sau da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki a hanya ta alama na nufin magana ko kuma yare. A dukan ajizancin mutane, yawancin zunubanmu za a iya samunsu a yadda muke amfani da furci ne.—Misalai 10:19; Yakub 3:2, 6.