Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 4

“Ubangiji . . . Mai-Girma ne Cikin Iko”

“Ubangiji . . . Mai-Girma ne Cikin Iko”

1, 2. Wadanne abubuwa ne masu ban mamaki Iliya ya gani a rayuwarsa, amma wadanne abubuwa ne mafi ban mamaki ya gani daga kogo a Dutsen Horeb?

ILIYA ya ga abubuwa na ban mamaki a dā. Ya ga hankaka ta kawo masa abinci sau biyu a rana lokacin da yake boye. Ya ga tukunya da ta ba da gari da kurtu da ya ba da mai a lokacin fari, da ba su kare ba na dogon lokaci. Ya ga an amsa addu’arsa da wuta da ta fado daga sama. (1 Sarakuna, surori 17,18) Duk da haka, Iliya bai taba ganin wani abu irin wannan ba.

2 Da ya durkusa a bakin kogo a Dutsen Horeb, ya ga abubuwa masu ban mamaki bi da bi. Ta farko iska ce. Watakila ta yi kara, ta yi gurnani da karfi, domin tana da karfi sosai, ta tsaga dutse kuma ta wargaza tuddai. Na gaba kuma girgizar kasa ce, da karfi mai yawa da ke rufe can cikin kasa. Sai wuta ta biyo baya. Ta share yankin, watakila Iliya ya ji zafin kunarta.—1 Sarakuna 19:8-12.

“Sai ga Ubangiji ya wuce”

3. Iliya ya ga tabbacin wane hali ne na Allah, kuma a ina ne za mu ga tabbacin irin wannan halin?

3 Dukan wadannan abubuwa dabam dabam da Iliya ya gani suna da abu iri daya—nuni ne na iko mai girma na Jehovah. Hakika ba ma bukatar ganin mu’ujiza don mu fahimci cewa Allah yana da iko. Wannan a bayyane yake. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa halitta suna ba da tabbacin ‘ikon Jehovah madawwami da allahntakarsa.’ (Romawa 1:20) Ka yi tunanin haske mai kashe ido na walkiya da kuma tsawa ta aradu, da fadawa na kogi, da kuma yadda sama take da fadi na ban razana! Ba ka ga ikon Allah ba cikin wadannan? Duk da haka, mutane kadan ne kawai a yau suka yarda da ikon Allah. Har ila, mutane kalilan ne suka dauke shi yadda ya dace. Amma fahimtar wannan hali na Allah tana ba mu dalilai na kusantar Jehovah. A wannan sashen, za mu shiga nazari daki-daki na ikon Jehovah da babu kamarsa.

Hali Mai Muhimmanci na Jehovah

4, 5. (a) Wace nasaba ke tsakanin sunan Jehovah da ikonsa? (b) Me ya sa ya dace da Jehovah ya zabi bijimi ya kwatanta ikonsa?

4 Jehovah farda ne wajen iko. Irmiya 10:6 ta ce: “Babu mai-kāma da kai, Ya Ubangiji: mai-girma ne kai, sunanka kuma da girma cikin iko.” Ka lura cewa iko yana hade da sunan Jehovah. Ka tuna cewa, babu shakka, sunansa yana nufin “Yakan Sa Ya Kasance.” Me ya sa ya yiwu Jehovah ya halicci dukan abin da yake so kuma ya sa kansa ya kasance dukan abin da ya zaba? Abu daya shi ne iko. Hakika, iyawar Jehovah ya aikata abu, ya cika nufinsa, ba shi da iyaka. Irin wannan ikon yana daya daga cikin halayensa masu muhimmanci.

5 Domin ba za mu iya samun cikakkiyar fahimtar ikonsa ba, Jehovah ya yi amfani da kwatanci domin ya taimake mu. Kamar yadda muka gani, ya yi amfani da bijimi ya kwatanta ikonsa. (Ezekiel 1:4-10) Zaben nan ya dace, domin bijimi na gida ma yana da girma kuma dabba ne mai karfi. Mutanen Palasdinu na zamanin Littafi Mai Tsarki da kyar, idan ma ke nan sun taba saduwa da abin da ya fi shi karfi. Amma sun san wani bijimi mafi ban tsoro—wani irin bijimin daji, ko kuma bauna, wadanda sun kare da jimawa. (Ayuba 39:9-12) Yuliyas Kaisar Daular Roma ya ce wadannan bijimai da kadan giwa ta dara su. Ya rubuta: “Karfinsu da yawa yake, kuma suna da gudu sosai.” Ka yi tunanin yadda za ka kankance kuma yadda za ka kasala idan kana tsaye kusa da irin wannan dabbar!

6. Me ya sa Jehovah ne kadai ake kira “Mai-iko duka”?

6 Hakanan, mutum ajizi ne marar karfi idan aka gwada shi da Allah mai iko, Jehovah. A gare shi, al’ummai masu girma ma kamar kura mai laushi a bisa mizani suke. (Ishaya 40:15) Ba kamar kowacce halitta ba, ikon Jehovah babu iyaka, domin shi kadai ake kira “Mai-iko duka.” * (Ru’ya ta Yohanna 15:3) Jehovah mai ‘girma ne a ikonsa’ kuma “mai-karfi ne cikin iko.” (Ishaya 40:26) Shi ne tushen iko marar karewa. Bai dogara ba ga wani tushen karfi daga waje, domin “iko ga Allah ya tabbata.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Zabura 62:11) Amma ta wace hanya ce Jehovah yake nuna ikonsa?

Yadda Jehovah Yake Nuna Ikonsa

7. Menene ruhu mai tsarki na Jehovah, kuma mecece kalma ta asali ta harshen take nufi da aka yi amfani da ita a cikin Littafi Mai Tsarki?

7 Jehovah yakan zubo da ruhu mai tsarki babu iyaka. Ikon Allah ne cikin aiki. Hakika, a Farawa 1:2, NW, Littafi Mai Tsarki ya ambace shi da cewa “ikon aiki” na Allah. A kalma ta asalin Ibrananci da kuma Helenanci da aka fassara “ruhu” a wasu wurare, za a iya fassara ta “iska,” “numfashi,” da kuma “guguwa.” In ji mawallafan kamus, kalma ta asali ta yaren tana nufin iko da ba a gani amma yana aiki. Kamar iska, ruhun Allah ba ya ganuwa ga idanunmu, amma ana gani kuma ana fahimtar ayyukansa.

8. A cikin Littafi Mai Tsarki, menene aka kira ruhu mai tsarki a alamance, kuma me ya sa wadannan kwatanci sun dace?

8 Ruhu mai tsarki na Allah mai canzawa ne. Jehovah yana yin amfani da shi ya cika dukan nufin da yake da shi a zuci. Saboda haka ne a cikin Littafi Mai Tsarki aka kira ruhun Allah a alamance ‘yatsa,’ ‘hannunsa mai karfi,’ ko kuma ‘mikakken hannu.’ (Luka 11:20; Kubawar Shari’a 5:15; Zabura 8:3) Kamar yadda mutum zai yi amfani da hannunsa wajen yin ayyuka dabam dabam da suke bukatar karfi da ya bambanta, haka ma Allah yana iya amfani da ruhunsa ya cika kowanne nufinsa—kamar su halittar atam dan mitsitsi ko kuma tsaga Jar Teku ko kuma sa Kiristoci na farko su yi magana a wasu harsuna.

9. Yaya yawan ikon sarauta na Jehovah yake?

9 Jehovah kuma yana nuna ikonsa ta wajen ikonsa na Mamallakin Dukan Halitta. Za ka iya tunanin kana da bayi miliyoyi bisa miliyoyi masu basira da suke a shirye su bi umurninka? Jehovah yana da irin wannan ikon sarauta. Yana da bayi mutane, a cikin Nassosi sau da yawa an kwatanta su da runduna. (Zabura 68:11; 110:3) Mutum halitta ne marar karfi, idan aka gwada shi da mala’ika. Shi ya sa, sa’ad da rundunar Assuriyawa suka kai wa mutanen Allah farmaki, mala’ika guda ya kashe sojoji 185,000 a dare daya! (2 Sarakuna 19:35) Mala’ikun Allah ‘karfafa ne masu iko.’—Zabura 103:19, 20.

10. (a) Me ya sa aka kira Mai Iko Duka, Jehovah mai runduna? (b) Wanene ne mafi girma a dukan halittar Jehovah?

10 Mala’iku nawa ne ake da su? Annabi Daniel ya ga wahayin sama, a ciki ya ga mala’iku fiye da miliyan 100 a gaban kursiyin Jehovah, amma babu alamar cewa ya ga dukan mala’ikun. (Daniel 7:10) Saboda haka, watakila da akwai mala’iku darurruwan miliyoyi. Saboda haka ake kiran Jehovah mai runduna. Wannan lakabi yana kwatanta matsayinsa mai girma na Kwamandan babbar kungiya ta mala’iku masu iko. A kan dukan wadannan ruhohi, ya dora shugaba, Dansa wanda yake kauna, “dan fari ne gaban dukan halitta.” (Kolossiyawa 1:15) Tun da shi ne babban mala’ika—shugaban dukan mala’iku, seraf, da kerub—Yesu shi ne mafi girma a dukan halittar Jehovah.

11, 12. (a) A wadanne hanyoyi ne maganar Allah take iko? (b) Ta yaya Yesu ya yi shaidar yawan ikon Jehovah?

11 Jehovah har yanzu yana da wata hanyar nuna iko. Ibraniyawa 4:12 ta ce: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.” Ka lura da karfin kalmar Allah bisa hankali ko kuma sako da ruhu ya hure, da aka adana yanzu cikin Littafi Mai Tsarki? Zai iya karfafa mu, ya gina bangaskiyarmu, kuma su taimake mu mu yi gyara sosai a rayuwarmu. Manzo Bulus ya gargadi ’yan’uwa masu bi game da mutane da suke dukufa cikin salon rayuwa ta lalata. Sai ya dada cewa: “Wadansu ma a cikinku dā haka ku ke.” (1 Korinthiyawa 6:9-11) Hakika, ‘maganar Allah’ ta yi iko a kan su kuma ta taimake su suka gyaru.

12 Ikon Jehovah da girma yake kuma hanyar nuna shi tana da karfi sosai da babu wanda zai iya hana shi. Yesu ya ce: “Ga Allah dukan abu ya yiwu.” (Matta 19:26) Ga wadanne nufe-nufe ne Jehovah yake amfani da ikonsa?

Iko da Kuduri Ke Ja-Gora

13, 14. (a) Me ya sa za mu iya cewa Jehovah ba tushe ba ne kawai marar rai na karfi? (b) A wadanne hanyoyi ne Jehovah yake amfani da ikonsa?

13 Ruhun Jehovah ya fi dukan wani karfi na zahiri; kuma Jehovah ba karfi ba ne da ba shi da rai, ko kuma kawai wani tushen karfi. Shi Allah ne mai rai wanda yake iko da karfinsa. Amma, me yake motsa shi ya yi amfani da ikonsa?

14 Kamar yadda za mu gani, Allah yana amfani da iko ya halitta, ya halaka, ya kāre, kuma ya yi gyara—kai, ya yi dukan abin da ya dace da kamiltaccen nufe-nufensa. (Ishaya 46:10) A wasu lokatai, Jehovah yana amfani da ikonsa ya bayyana muhimman fannin mutuntakarsa da kuma mizanai. Mafi muhimmanci ma, yana amfani da ikonsa ya cika nufinsa—ya kunita ikon mallakarsa kuma ya tsarkake sunansa mai tsarki ta wajen Mulkin Almasihu. Babu abin da zai iya taka wannan nufin.

15. Jehovah ya yi amfani da ikonsa domin wane nufi ne da ke hade da bayinsa, kuma yaya aka kwatanta wannan a batun Iliya?

15 Jehovah yana amfani da ikonsa ya amfane kowannenmu. Ka lura da abin da 2 Labarbaru 16:9 ta ce: “Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai karfi sabili da wadanda zuciyarsu ta kamilta gareshi.” Wani misali shi ne abin da Iliya ya fuskanta, da aka ambata da farko. Me ya sa Jehovah ya nuna masa wannan iko? Muguwar sarauniya Jezebel ta rantse cewa sai ta sa an kashe Iliya. Annabin ya yi gudun ransa. Ya ji ya kadaita, ya tsorata, kuma ya kasala—kamar dukan aikinsa da kwazo ya zama banza. Don ya karfafa mutumin da yake wahala, Jehovah ya tuna wa Iliya ikonsa. Iskar, da girgizar kasa, da wuta sun nuna cewa Mafi karfi a dukan sararin samaniya yana tare da Iliya. Me zai tsorata daga Jezebel da yake Allah mai iko duka yana tare da shi?—1 Sarakuna 19:1-12. *

16. Me ya sa za mu karfafa ta wajen bimbini bisa iko mai girma na Jehovah?

16 Ko da yake yanzu ba lokacinsa ba ne na yin mu’ujiza, Jehovah bai canja ba tun daga zamanin Iliya. (1 Korinthiyawa 13:8) A yau, yana dokin ya yi amfani da ikonsa domin wadanda suke kaunarsa. Hakika, yana mazaunin ruhu, amma ba shi da nisa daga gare mu. Ikonsa ba shi da iyaka, saboda haka, nisa ba wani abu ba ne. Maimakon haka, “Ubangiji yana kusa da dukan wadanda su ke kira bisa gareshi.” (Zabura 145:18) Wani lokaci da annabi Daniel ya kira bisa Jehovah domin taimako, mala’ika ya bayyana kafin ma ya gama addu’arsa! (Daniel 9:20-23) Babu abin da zai hana Jehovah taimakon wadanda yake kauna kuma ya karfafa su.—Zabura 118:6.

Ikon Allah Ya Sa ba Za a Iya Kusantarsa ba Ne?

17. A wace hanya ce ikon Jehovah yake sa mu tsoro, amma wane irin tsoro ne ba ya kawowa?

17 Ikon Jehovah ya kamata ya sa mu tsorace shi ne? Dole ne mu amsa e, da kuma a’a. E, saboda wannan halin ya ba mu isashen dalilai domin tsoro na ibada, girmamawa da kuma darajawa da muka tattauna a babi na baya. Irin wannan tsoron, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “mafarin hikima ne.” (Zabura 111:10) Za mu kuma ce a’a, domin ikon Allah bai ba mu dalilin razana ba dominsa ko kuma mu guji matsowa kusa da shi.

18. (a) Me ya sa mutane da yawa ba su yarda da mutane masu iko ba? (b) Ta yaya muka sani cewa ikon Jehovah ba zai lalata shi ba?

18 “Iko yana lalatarwa; cikakken iko yana lalatarwa gabaki daya.” Haka dan tarihin Ingilishi Lord Acton ya rubuta a shekara ta 1887. Wannan furcin nasa an maimaita shi sau da yawa, watakila domin mutane da yawa suna ganin gaskiya ce da ba za a yi jayayya da ita ba. Mutane ajizai sau da yawa suna barna da iko, kamar yadda tarihi ya nuna a kai a kai. (Mai-Wa’azi 4:1; 8:9) Domin wannan, mutane da yawa ba sa yarda da masu iko kuma suna janyewa daga gare su. Amma, Jehovah yana da cikakken iko. Akwai hanya ce da ya lalata shi? Hakika babu! Kamar yadda muka gani, mai tsarki ne, ba shi da lalata ko dis. Jehovah ba kamar mutane ajizai ba ne masu iko a wannan lalatacciyar duniya. Bai taba cin zali ba, kuma ba zai taba cin zali ba.

19, 20. (a) Cikin jituwa da wadanne halaye ne Jehovah koyaushe yake nuna ikonsa, kuma me ya sa wannan yana da ban tabbaci? (b) Ta yaya za mu kwatanta kamewa na Jehovah, kuma me ya sa wannan yake da kyau a gare ka?

19 Ka tuna cewa, iko ba shi ne kadai ba halin Jehovah. Har yanzu ba mu yi nazarin shari’arsa ba, hikimarsa, da kuma kaunarsa. Amma bai kamata mu yi tsammanin cewa halayen Jehovah suna bayyana ne kawai daddaya ba, kamar dai a ce daya zai bayyana a lokaci guda. Akasarin haka, za mu gani a babi na gaba cewa koyaushe Jehovah yana nuna ikonsa ne cikin jituwa da shari’arsa, hikimarsa, da kuma kaunarsa. Ka yi tunanin wani hali da Allah yake da shi, wanda ba a samu wurin sarakunan duniya—kamewa.

20 Ka yi tunanin ka sadu da mutum mai kiba kuma ga karfi har ya tsorata ka. Amma, daga baya ka lura cewa yana da kirki. Koyaushe a shirye yake ya yi amfani da karfinsa ya kāre mutane, musamman wadanda ba su da mai kāre su da kuma marasa karfi. Bai taba cin zali ba. Ana zaginsa babu dalili, duk da haka halinsa ga mutane a kafe yake yana kama kai, da daraja, har ma da kirki. Kana mamaki idan za ka iya nuna irin kirki da kuma kamewar nan, musamman ma idan kana da karfinsa! Yayin da ka san wannan mutumin ba za ka fara matsowa kusa da shi ba? Muna da dalili mafi girma na kusantar Jehovah mai iko duka. Ka lura da cikakkiyar jimla da ta ba da jigon wannan babin: Jehovah “mai-jinkirin fushi ne, mai-girma ne cikin iko.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Nahum 1:3) Jehovah ba ya saurin yin amfani da ikonsa gaba da mutane, har ma miyagu. Mai jinkirin fushi ne kuma mai kirki. Ya tabbatar da cewa shi “mai-jinkirin fushi” ne duk da yawan tsokana da ake yi masa.—Zabura 78:37-41.

21. Me ya sa Jehovah yake kame kansa daga tilasta wa mutane su yi nufinsa, kuma menene wannan ya nuna mana game da shi?

21 Ka lura da kamewa na Jehovah a wata hanya dabam. Idan kana da iko babu iyaka, a wasu lokatai, kana tsammanin za ka so ka sa mutane su yi abubuwa yadda kake so? Jehovah, da dukan ikonsa, ba ya tilasta wa mutane su bauta masa. Ko da yake bauta wa Allah shi ne kawai hanyar rai madawwami, Jehovah bai tilasta mana ba mu yi wannan bautar. Maimakon haka, ya daraja kowa da ’yancin zabe. Ya yi gargadi game da sakamakon mummunan zabe kuma ya fadi ladar kyakkyawan zabe. Amma, ya bar mu mu yi zaben kanmu. (Kubawar Shari’a 30:19, 20) Jehovah ba ya son a bauta masa dole ko kuma cikin tsoron ikonsa mai ban tsoro. Yana neman wadanda za su bauta masa da son rai, cikin kauna.—2 Korinthiyawa 9:7.

22, 23. (a) Me ya nuna cewa Jehovah yana farin ciki ya ba wasu iko? (b) Menene za mu bincika a babi na gaba?

22 Bari mu ga dalili na karshe da ya sa bai kamata mu rayu cikin razanar Allah Mai Iko Duka ba. Mutane masu iko suna tsoron ba wa wasu iko. Amma, Jehovah yana farin cikin ba wa amintattun bayinsa iko. Yana ba wa wasu iko da ya dace—kamar Dansa. (Matta 28:18) Jehovah kuma yana ba wa bayinsa iko a wata hanya. Littafi Mai Tsarki ya yi bayani: “Girma, da iko, da daukaka, da nasara, da sarauta, naka ne, ya Ubangiji: gama abin da ke cikin sama da kasa duk naka ne; . . . a cikin hannunka akwai iko da karfi; naka ne kuma ka bada girma, da karfi ga kowa.”—1 Labarbaru 29:11, 12.

23 Hakika, Jehovah zai yi farin ciki ya ba ka karfi. Yana bayar da “mafificin girman iko” ga wadanda suke so su bauta masa. (2 Korinthiyawa 4:7) Ba ka ji kana so ka matso kusa da wannan Allah mai karfi ba, wanda yake yin amfani da ikonsa a wannan hanya ta kirki da kuma ka’ida? A babi na gaba, za mu mai da hankali ga yadda Jehovah yake amfani da ikonsa ya yi halitta.

^ sakin layi na 6 Kalmar Helenanci da aka fassara “Mai-iko duka” a zahiri tana nufin “Mai Iko Bisa Kowa; Wanda Yake da Dukan Iko.”

^ sakin layi na 15 Littafi Mai Tsarki ya ce ‘[Jehovah] ba ya cikin iska . . . , girgizar kasa . . . da wutar.’ Ba kamar masu bauta wa allolin kage ba, bayin Jehovah ba sa nemansa cikin ikon halitta. Ya fi karfin a neme shi cikin dukan wani abin da ya halitta.—1 Sarakuna 8:27.