Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 6

Ikon Halaka—Jehovah, “Mayaki Ne”

Ikon Halaka—Jehovah, “Mayaki Ne”

1-3. (a) Wace barazana Isra’ilawa suka fuskanta a hannun Masarawa? (b) Ta yaya Jehovah ya yi yaki domin mutanensa?

ISRA’ILAWA sun kamu—tsakanin manyan duwatsu da kuma teku. Sojojin Masar marasa jinkai suna binsu, sun kuduri aniyyar sai sun halaka su. * Duk da haka, Musa ya aririci mutanen Allah kada su fid da rai. Ya ba su tabbaci, “Ubangiji za shi yi yaki dominku.”—Fitowa 14:14.

2 Duk da wannan, Musa babu shakka ya yi wa Jehovah kuka, kuma Allah ya ce: “Don me ka ke yi mini kuka? . . . ka cira sandarka, ka mika hannunka bisa teku, ka raba shi biyu.” (Fitowa 14:15, 16) Ka yi tunanin abubuwan da suka fara aukuwa. Sai Jehovah ya umurci mala’ikansa, kuma umudi na gajimare ya koma bayan Isra’ilawan, watakila yana bazuwa kamar garu yana rufe inda Masarawan za su kai farmaki. (Fitowa 14:19, 20; Zabura 105:39) Musa ya mika hannunsa. Iska mai karfi ta busa, tekun ta rabu biyu. Ruwan ya daskare ya tsaya kamar garu, ya bude hanya mai isashen fadi da ya dauki dukan al’ummar!—Fitowa 14:21; 15:8.

3 Da ya fuskanci wannan nuna iko, da Fir’auna ya koma gida da rundunarsa. Maimakon haka, Fir’auna mai fahariya ya ba da umurnin a kai farmaki. (Fitowa 14:23) Masarawan suka yi sauri suka bi Isra’ilawan ba tare da wani tunani ba, amma farmakinsu ya koma dimaucewa sa’ad da kafafun karusansu suka soma bangalewa. Da isar Isra’ilawa ketaren tekun, Jehovah ya umurci Musa: “Mika hannunka bisa teku, domin ruwaye su koma bisa Masarawa, bisa karusansu, da bisa mahayansu.” Garu na ruwan kuwa ya rushe, ya binne Fir’auna da rundunarsa!—Fitowa 14:24-28; Zabura 136:15.

A Jar Teku, Jehovah ya tabbatar da kansa “mayaki”

4. (a) Menene Jehovah ya tabbatar a Jar Teku? (b) Yaya wasu za su ji game da wannan kwatanci na Jehovah?

4 Ceton al’ummar Isra’ila a Jar Teku abu ne na tunawa a tarihin sha’ani da Allah ya yi da ’yan Adam. A wannan wajen Jehovah ya tabbatar da kansa “mayaki ne.” (Fitowa 15:3) Yaya ka ji game da wannan kwatanci na Jehovah? Hakika, yaki kan jawo azaba da bala’i ga ’yan Adam. Shin amfani da ikon halaka da Allah ya yi ya kasance ne kamar abin da zai hana ka kusantarsa maimakon ka matso kusa da shi?

Yake-Yake na Allah da Kuma na Mutane

5, 6. (a) Me ya sa ya dace da aka kira Allah “Ubangiji mai-runduna”? (b) Ta yaya yake-yake na Allah ya bambanta da na mutane?

5 Kusan sau dari uku a cikin Nassosin Ibrananci kuma sau biyu a Nassosin Helenanci na Kirista, aka bai wa Allah lakabin nan “Ubangiji mai-runduna.” (1 Samu’ila 1:11) Tun da Mamallaki ne, Jehovah yana ja-gorar runduna mai girma na mala’iku. (Joshua 5:13-15; 1 Sarakuna 22:19) Halaka da wannan rundunar za ta iya yi abin ban tsoro ne. (Ishaya 37:36) Halaka mutane ba ta da dadin a yi tunaninta. Amma, dole ne mu tuna cewa yake-yake na Allah ba kamar dan tashin hankali ba ne na mutane. Shugabanni na soja da na siyasa za su yi kokari su nuna suna da kyakkyawar niyya wajen nuna karfinsu. Amma yake-yake na mutane babu shakka ya kunshi hadama da son kai.

6 Akasin haka, motsin zuciya ba ya rufe wa Jehovah hankali. Kubawar Shari’a 32:4 ta ce: “Fa ne shi, aikinsa cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne: shi Allah mai-aminci ne, mara-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” Kalmar Allah ta haramta fushi da ba ta da makawa, mugunta, da kuma nuna karfi. (Farawa 49:7; Zabura 11:5) Jehovah ba ya aikata abu babu dalili. Yana amfani kadan ne kawai da ikonsa na halakarwa, sai ya kasance babu wani abin yi kuma. Kamar yadda ya ce ne ta bakin annabi Ezekiel: “Ni ina jin dadin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Yahweh: ban gwammace ya juya ga barin aikinsa ya yi rai ba?”—Ezekiel 18:23.

7, 8. (a) Menene Ayuba ya kammala cikin kuskure game da wahalarsa? (b) Ta yaya Elihu ya gyara tunanin Ayuba game da wannan? (c) Menene za mu iya koya daga abin da Ayuba ya fuskanta?

7 To, me ya sa Jehovah yake amfani da ikonsa na halakarwa? Kafin mu amsa, za mu tuna da mutumin nan mai aminci Ayuba. Shaidan ya kalubalanci cewa ko Ayuba—hakika, kowanne taliki—zai rike amincinsa cikin gwaji. Jehovah ya amsa ta kyale Shaidan ya gwada amincin Ayuba. Domin wannan, Ayuba ya yi ciwo, ya yi hasarar arzikinsa, kuma ya yi rashin ’ya’yansa. (Ayuba 1:1–2:8) Cikin rashin sanin abin da ke tafiya, Ayuba ya kammala cikin kuskure cewa wahalarsa horo ne kawai na rashin adalci daga Allah. Ya tambayi Allah dalilin da ya sa Ya mai da shi abin ‘bārata,’ kuma ‘makiyinsa.’—Ayuba 7:20; 13:24.

8 Wani saurayi mai suna Elihu ya fallasa kuskure da ke cikin tunanin Ayuba, ya ce: “Adalcina ya fi na Allah, in ji ka.” (Ayuba 35:2) Hakika, ba hikima ba ce mu yi tunanin cewa mun fi Allah sani ko kuma mu yi tsammanin cewa abin da ya yi bai dace ba. “Dadai Allah shi yi mugunta! Mai-iko duka shi yi aikin sabo,” in ji Elihu. Daga baya ya ce: “Ubangiji! ya fi karfinmu mu gane shi; mafifici ne shi cikin iko: a cikin shari’ar gaskiya da adalci ba shi ciwuci mutum ba.” (Ayuba 34:10; 36:22, 23; 37:23) Za mu tabbata cewa idan Allah ya yi fadā, yana da kyakkyawan dalilin yin haka. Da wannan, bari mu bincika wasu dalilai da ya sa Allah na salama wasu lokatai yake damarar yaki.—1 Korinthiyawa 14:33.

Abin da Yake Tilasta wa Allah na Salama Ya Yi Yaki

9. Me ya sa Allah na salama yake yaki?

9 Bayan ya yabi Allah cewa “mayaki ne,” Musa ya ce: “Wanene ya yi kama da kai, ya Ubangiji, a cikin alloli? Wanene kamarka, madaukaki cikin tsarki?” (Fitowa 15:11) Annabi Habakkuk hakanan ya rubuta: “Kai wanda tsarkin idonka ya fi gaban duban mugunta, ba ka iya kallon shiririta ba.” (Habakkuk 1:13) Ko da yake Jehovah Allah ne na kauna, har ila shi Allah na tsarkaka, adalci, da kuma shari’a. Wasu lokatai, wadannan halaye suke tilasta masa ya yi amfani da ikonsa na halakarwa. (Ishaya 59:15-19; Luka 18:7) Allah baya kazantar da tsarkakarsa sa’ad da ya yi yaki. Maimakon haka, yana yaki ne domin yana da tsarki.—Fitowa 39:30.

10. (a) Yaushe kuma ta yaya bukatar Allah ya yi yaki ya fara tasowa? (b) Yaya za a warware magabtaka da aka annabta a Farawa 3:15, kuma yaya mutane adalai za su amfana?

10 Ka yi la’akari da abin da ya faru bayan mata da miji na farko, Adamu da Hauwa’u, suka yi wa Allah tawaye. (Farawa 3:1-6) Da ya kyale rashin amincinsu, da Jehovah ya rage matsayinsa na Mamallakin Dukan Halitta. Tun da Allah mai adalci ne, ya zama dole ya yi musu hukuncin kisa. (Romawa 6:23) A cikin annabci na farko na Littafi Mai Tsarki, ya ce magabtaka za ta kasance tsakanin bayinsa da kuma mabiyan “macijin,” Shaidan. (Ru’ya ta Yohanna 12:9; Farawa 3:15) A karshe, wannan magabtakar za ta kare ne kawai ta wajen kuje Shaidan. (Romawa 16:20) Amma wannan shari’ar za ta kawo albarka mai girma ga mutane adalai, ta kawar da rinjayar Shaidan a duniya kuma ta bude hanyar mai da duniya aljanna. (Matta 19:28) Har sai lokacin, wadanda suke gefen Shaidan za su ci gaba da razana ga lafiyar jiki da ta ruhaniya ta mutanen Allah. A wasu lokatai, dole ne Jehovah ya saka hannu.

Allah Ya Aikata don Ya Kawar da Mugunta

11. Me ya sa Allah ya ga ya zama dole ya kawo rigyawa ta dukan duniya?

11 Rigyawa ta zamanin Nuhu aukuwa ce ta irin wannan saka hannu. Farawa 6:11, 12, ta ce: “Duniya kuwa ta baci a gaban Allah, duniya kuma ta cika da zalunci. Allah ya duba duniya, ga ta kuwa batacciya ce; gama dukan masu-rai sun bata tafarkinsu a duniya.” Allah zai kyale miyagu ne su kawar da dabi’a ’yar kadan da ta rage a duniya? A’a. Jehovah ya ga ya zama dole ya kawo rigyawa ta duniya ta halaka wadanda suke da sha’awa na kwarai na nuna karfi da kuma yin lalata.

12. (a) Menene Jehovah ya annabta game da “zuriyar” Ibrahim? (b) Me ya sa za a halaka Amoriyawa?

12 Hakanan ma hukuncin Allah bisa Kan’aniyawa. Jehovah ya bayyana cewa daga Ibrahim za a yi “da” ta wurin wanda za a albarkaci dukan iyalai na duniya. Cikin jituwa da wannan nufin, Allah ya kafa doka cewa za a ba dan Ibrahim kasar Kan’ana, kasar da mutane da ake kira Amoriyawa suke zaune. Yaya za a ce Allah ya yi adalci idan ya fid da mutanen nan da karfi daga kasarsu? Jehovah ya annabta cewa sai bayan shekaru 400—sai “alhakin Amoriyawa” ya ‘cika tukuna.’ * (Farawa 12:1-3; 13:14, 15; 15:13, 16; 22:18) Cikin wannan lokacin, Amoriyawan suka dada nitsewa cikin muguwar lalata. Kan’ana ta zama kasar bautar gumaka, kisa, da kuma kazamin jima’i. (Fitowa 23:24; 34:12, 13; Litafin Lissafi 33:52) Mazauna kasar suna kashe yara cikin wutar hadaya ma. Allah mai tsarki zai kyale mutanensa ga irin wannan muguntar? A’a! Ya ce: “Kasa kuwa ta kazantu; domin wannan ni ke jawo mata alhakinta, kasa kuwa tana harasda mazaunanta.” (Leviticus 18:25) Jehovah bai halaka mutanen ba kawai, ba ji ba gani ba. Kan’anawa masu zukatan kirki, kamar su Rahab da kuma Gibiyonawa, an kyale su.—Joshua 6:25; 9:3-27.

Yaki Domin Sunansa

13, 14. (a) Me ya sa ya zama dole Jehovah ya tsarkake sunansa? (b) Ta yaya Jehovah ya tsabtace sunansa daga zargi?

13 Domin Jehovah mai tsarki ne, sunansa yana da tsarki. (Leviticus 22:32) Yesu ya koya wa almajiransa su yi addu’a: “A tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) Tawaye a Adnin ya kazantar da sunan Allah, ya ta da shakka game da darajarsa da kuma yadda yake mulki. Jehovah ba zai taba kyale irin wannan zagi da kuma tawaye ba. Dole ne ya tsarkake sunansa daga zargi.—Ishaya 48:11.

14 Ka sake yin la’akari da Isra’ilawa. Idan suka ci gaba da kasancewa bayi a kasar Masar, alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim cewa ta wajen Zuriyarsa dukan iyalai na duniya za su albarkaci kansu ya kasance wofi. Amma ta wajen cetonsu da kuma shirya su su zama al’umma, Jehovah ya tsabtace sunansa daga zargi. Saboda haka, annabi Daniel ya tuna cikin addu’a: “Ya Ubangiji Allahnmu, . . . ka fito da mutanenka daga cikin kasar Masar da hannu mai-iko, ka sami wa kanka suna.”—Daniel 9:15.

15. Me ya sa Jehovah ya ceci Yahudawa daga bauta a Babila?

15 Abin farin ciki, Daniel ya yi wannan addu’ar a lokacin da Yahudawa suke bukatar Jehovah ya sake ceto domin Sunansa. Yahudawa marar biyayya sun samu kansu cikin bauta, lokacin kuwa a Babila ne. Nasu babban birni, Urushalima, ya kasance kango. Daniel ya san cewa mai da Yahudawan kasarsu zai daukaka sunan Jehovah. Saboda haka Daniel ya yi addu’a: “Ya Ubangiji, ka gafarta; ya Ubangiji, ka kasa kunne ka aika; kada ka yi jinkiri; sabili da kanka, ya Allahna, domin ana kiran birninka da mutanenka da sunanka.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; Daniel 9:18, 19.

Yaki Domin Mutanensa

16. Ka ba da bayanin dalilin da ya sa son ya kāre sunansa ba ya nufin cewa Jehovah ba shi da tausayi kuma yana da son kai.

16 Domin Jehovah yana son kāre sunansa yana nufin cewa marar tausayi ne shi kuma mai son kai? A’a, domin ta aikata cikin jituwa da tsarkakarsa da kaunar shari’a, yana kāre mutanensa. Ka yi la’akari da Farawa sura 14. A nan mun karanta game da sarakuna hudu da suka kai hari kuma suka kama dan wan Ibrahim, Lot, tare da iyalinsa. Da taimakon Allah, Ibrahim ya yi kyakkyawar nasara bisa runduna mai yawa da ta dara tashi! Tarihin nasararsa watakila shi ne tarihi na farko a cikin “littafin Yakin Ubangiji,” watakila littafin da yake dauke da wasu arangama na sojoji da ba a rubuta cikin Littafi Mai Tsarki ba. (Litafin Lissafi 21:14) Nasarori da yawa za su biyo.

17. Menene ya nuna cewa Jehovah ya yi yaki domin Isra’ilawa bayan sun shiga kasar Kan’ana? Ka ba da misalai.

17 Ba da jimawa ba kafin Isra’ilawa su shiga kasar Kan’ana, Musa ya tabbatar musu cewa: “Ubangiji Allahnku wanda ke tafiya a gabanku, shi za ya yi yaki dominku, bisa dukan irin abin da ya yi muku cikin Masar.” (Kubawar Shari’a 1:30; 20:1) Farawa da magajin Musa, Joshua, kuma ya ci gaba a lokacin Mahukunta da kuma lokacin sarautar sarakuna masu aminci na Yahuda, babu shakka Jehovah ya yi yaki domin mutanensa, ya ba su nasarori masu ban sha’awa da yawa bisa abokan gabansu.—Joshua 10:1-14; Alkalawa 4:12-17; 2 Samu’ila 5:17-21.

18. (a) Me ya sa za mu yi godiya cewa Jehovah bai canja ba? (b) Me zai faru sa’ad da magabtaka da aka kwatanta a Farawa 3:15 ta zo karshenta?

18 Jehovah bai canja ba; kuma nufinsa na mai da wannan duniya ta zama aljanna mai salama bai canja ba. (Farawa 1:27, 28) Har ila Allah yana kyamar mugunta. Hakanan kuma, yana kaunar mutanensa kwarai da gaske kuma ba da dadewa ba zai yi yaki dominsu. (Zabura 11:7) Hakika, magabtaka da aka kwatanta a Farawa 3:15 ana tsammanin za ta kai lokaci na musamman na nuna karfi ba da dadewa ba. Domin ya tsarkake sunansa kuma ya kāre mutanensa, Jehovah zai sake zama “mayaki”!—Zechariah 14:3; Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.

19. (a) Ka kwatanta abin da ya sa amfani da ikon halakarwa na Allah zai iya jawo mu kusa da shi. (b) Yaya ya kamata yadda Allah yake son ya yi yaki da son rai dominmu ya taba mu?

19 Ka yi la’akari da wannan kwatanci: A ce wata muguwar dabba ta fadā wa iyalin wani mutum, sai mutumin ya shigo ya kashe dabbar. Za ka zaci matar da ’ya’yan su guje shi domin abin da ya yi? Akasin haka, za ka so kauna marar son kai ta motsa su. Hakazalika, bai kamata ba mu guji Allah domin ikonsa na halakarwa. Yaki da son ransa domin ya kāre mu ya kamata ya zurfafa kaunar da muke masa. Kuma daraja da muke ba shi domin ikonsa mara iyaka ya kamata ta karu ita ma. Da haka, za mu “yi ma Allah sujjada abin karba gareshi tare da ladabi da saduda.”—Ibraniyawa 12:28.

Ka Matso Kusa da “Mayaki”

20. Idan muka karanta tarihin Littafi Mai Tsarki game da yake-yake na Allah da ba mu fahimta ba sosai, me ya kamata mu yi, kuma me ya sa?

20 Hakika, Littafi Mai Tsarki bai ba da cikakken bayani ba game da dukan yake-yake na Allah. Amma game da wannan za mu iya kasancewa kullum da tabbaci: Jehovah ba ya amfani da ikonsa na halakarwa cikin rashin adalci, mugunta, ko kuma keta. Sau da yawa, bincika matanin tarihin Littafi Mai Tsarki ko kuma wasu barin bayani zai iya taimakawa a fahimci batun. (Misalai 18:13) Ko sa’ad da ba mu samu cikakken bayani ba, koyo game da Jehovah da kuma bimbini bisa halayensa masu tamani za su taimake mu warware kowacce tantama da za ta taso. Idan muka yi wannan, za mu ga cewa muna da dalilai masu yawa na dogara ga Allahnmu, Jehovah.—Ayuba 34:12.

21. Ko da yake “mayaki” ne wani lokaci, yaya Jehovah yake ainihinsa?

21 Ko da yake Jehovah “mayaki” ne idan yanayi ya bukaci haka, wannan ba ya nufin cewa shi masoyin yaki ne ainihi. A wahayin karusa na sama na Ezekiel, an kwatanta Jehovah da cewa yana shirye ya yi yaki da abokan gabansa. Duk da haka, Ezekiel ya ga bakan gizo ya kewaye Allah—alamar salama. (Farawa 9:13; Ezekiel 1:28; Ru’ya ta Yohanna 4:3) Babu shakka, Jehovah mai kamewa ne kuma mai salama. “Allah kauna ne,” in ji manzo Yohanna. (1 Yohanna 4:8) Dukan halayen Jehovah sun kasance daidai. Lallai muna da gata, mu kusaci irin wannan Allah mai iko har ila kuma mai kauna!

^ sakin layi na 1 In ji Bayahude dan tarihi Josephus, wajen “karusa 600 tare da mahayan dawakai 50,000 da dakaru wajen 200,000 suka bi Ibraniyawan.”—Jewish Antiquities, II, 324 [xv, 3].

^ sakin layi na 12 Hakika, kalmar nan “Amoriyawa” ya kunshi dukan mutanen Kan’ana.—Kubawar Shari’a 1:6-8, 19-21, 27; Joshua 24:15, 18.