Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 7

Ikon Kāriya—“Allah Mafaka ne a Gare Mu”

Ikon Kāriya—“Allah Mafaka ne a Gare Mu”

1, 2. Isra’ilawa suna cikin wane hadari sa’ad da suka shiga cikin yankin Sinai a shekara ta 1513 K.Z., kuma yaya Jehovah ya ba su tabbaci?

ISRA’ILAWA suna cikin hadari sa’ad da suka shiga yankin Sinai a farkon shekara ta 1513 K.Z. Tafiya mai ban tsoro yana gabansu, tafiya cikin “babban jeji, mai-ban tsoron nan, wurinda macizai masu-wuta su ke, da kunamai.” (Kubawar Shari’a 8:15) Sun fuskanci burga daga al’ummai masu hamayya. Jehovah ya sa mutanensa cikin wannan yanayin. Tun da Allahnsu ne, zai iya kāre su kuwa?

2 Kalmomin Jehovah suna ba da tabbaci: “Kun ga abin da na yi ma Masarawa, yadda na dauke ku kuma bisa fukafukan gaggafa, na kawo ku gareni.” (Fitowa 19:4) Jehovah ya tunasar da mutanensa cewa ya cece su daga Masarawa, ya yi amfani da gaggafa, cikin alama ya dauko su su tsira. Amma kuma da akwai wasu dalilai da ya sa “fukafukan gaggafa” suka dace wajen kwatanta kāriya daga Allah.

3. Me ya sa “fukafukan gaggafa” sun dace wajen kwatanta kāriyar Allah?

3 Gaggafa tana amfani da fukafukanta masu girma, masu karfi fiye da ta tashi sama kawai. Sa’ad da rana take da zafi, gaggafa za ta mike fukafukanta—da zai kai wajen kafa bakwai—ta yi laima, ta kāre ’yan kanananta daga zafin rana. A wani lokaci, tana kewaye ’yan kanananta da fukafukanta ta kāre su daga iska mai sanyi. Kamar yadda gaggafar take kāre ’yan kanananta, haka Jehovah ya kāre karamar al’ummar Isra’ila. Yanzu a daji, mutanensa za su ci gaba da fakewa a inuwar fukafukinsa mai girma muddin sun ci gaba da aminci. (Kubawar Shari’a 32:9-11; Zabura 36:7) Amma daidai ne mu yi tsammanin kāriyar Allah a yau?

Alkawarin Kāriyar Allah

4, 5. Me ya sa za mu dogara ga alkawarin Allah na kāriya?

4 Babu shakka Jehovah zai iya kāre bayinsa. Shi ne ‘Allah Madaukaki Duka’—lakabi da ya nuna cewa yana da iko da babu iyaka. (Farawa 17:1) Kamar malalar teku, ikon da Jehovah ya sa a aiki ba za a iya wargaje shi ba. Tun da zai iya yin duk abin da ya nufa, za mu iya tambaya, ‘Nufin Jehovah ne ya yi amfani da ikonsa ya kāre mutanensa?’

5 E! Jehovah ya tabbatar mana cewa zai kāre mutanensa. “Allah mafakanmu ne da karfinmu, taimako ne na kurkusa cikin wahala,” in ji Zabura 46:1. Tun da Allah “ba shi iya yin karya,” za mu iya dogara ga alkawarinsa na kāriya. (Titus 1:2) Bari mu bincika wasu kwatanci da Jehovah ya yi amfani da su wajen kwatanta kāriyarsa.

6, 7. (a) Makiyayi na lokatan Littafi Mai Tsarki yana ba da wace kāriya ce ga tumakinsa? (b) Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta muradin Jehovah na kāre mu da kuma kula da tumakinsa?

6 Jehovah makiyayi ne, kuma “mu mutanensa ne, tumakin makiyayatasa kuma.” (Zabura 23:1;100:3) Dabbobi kadan ne kawai ba su da kāriya kamar tumaki. Makiyayi na lokatan Littafi Mai Tsarki dole ne ya mazakuta ya kāre tumakinsa daga zakuna, karnukan daji, da kuma barayi. (1 Samu’ila 17:34, 35; Yohanna 10:12, 13) Amma akwai lokacin da kāre tumakin yana bukatar hankali. Idan tunkiya ta haihu nesa da garke, makiyayi mai kauna zai yi gadin uwar, a wannan lokacin kuma ya dauki dan tunkiyar marar karfi zuwa garken.

“A ƙirjinsa ya ɗauke su”

7 Ta wajen kwatanta kansa da makiyayi, Jehovah ya tabbatar mana muradinsa na son ya kāre mu. (Ezekiel 34:11-16) Ka tuna kwatancin Jehovah da aka samu a Ishaya 40:11, da aka tattauna a Babi na 2 na wannan littafin: “Za ya yi kiwon garkensa kamar makiyayi, za ya tattara ’ya’yan tumaki a hannunsa, ya dauke su a cikin kirjinsa.” Ta yaya dan tunkiya ya kasance a “kirjin” makiyayin—a ninki na saman rigarsa? Dan tunkiyar zai je ga makiyayin, har ma ya shafi kafarsa. Amma, makiyayin ne dole ya sunkuya, ya dauki dan tunkiyar, kuma ya daura shi a kirjinsa wajen kāriya a hankali. Wannan kwatanci ne mai kyau na son ran Makiyayinmu Mai Girma ya yi mana mafaka kuma ya kāre mu!

8. (a) Alkawarin kāriyar Allah an mika wa wanene, kuma yaya aka nuna wannan a Misalai 18:10? (b) Menene samun mafaka cikin sunan Allah ya kunsa?

8 Alkawarin kāriyar Allah, yana bisa sharadi ne—wadanda suka matso kusa da shi ne kawai suke samu. Misalai 18:10 ta ce: “Sunan Ubangiji kagara ne mai-karfi: mai-adalci ya kan gudu ya shiga ciki, shi sami lafiya.” A lokatan Littafi Mai Tsarki, wani lokaci ana gina hasumiya a daji, watau, wajen mafaka ce. Amma hakkin wanda yake cikin hadari ne ya ruga zuwa wannan hasumiyar domin ya samu kāriya. Kama yake da neman mafaka cikin sunan Allah. Wannan ya kunshi fiye da kiran sunan Allah kawai; sunan Allah ba layar zana ba ce. Maimakon haka, muna bukatar mu sani kuma mu dogara ga Mai sunan kuma mu rayu cikin jituwa da mizanansa na adalci. Jehovah yana da kirki da ya tabbatar mana cewa idan muka juya gare shi cikin bangaskiya, zai kasance hasumiyar kāriya dominmu!

“Allahnmu . . . Yana da Iko Ya Cece Mu”

9. Ta yaya Jehovah ya yi fiye da yin alkawarin kāriya kawai?

9 Jehovah ya yi fiye da yin alkawarin kāriya. A zamanin Littafi Mai Tsarki, ya nuna ta hanyoyin mu’ujiza cewa zai iya kāre mutanensa. Lokacin tarihin Isra’ila, ‘hannu’ mai girma na Jehovah sau da yawa yake korar abokan gaba. (Fitowa 7:4) Amma, Jehovah ya yi amfani da ikonsa na kāriya domin wasu mutane.

10, 11. Wane misali ne ya nuna yadda Jehovah yake amfani da ikonsa na kāriya domin mutane dai-dai?

10 Sa’ad da samari Ibraniyawa uku—Shadrach, Meshach, da Abednego—suka ki su yi sujjada ga gunkin zinariya na Sarki Nebuchadnezzar, sarki da ya fusata ya yi burgar jefa su cikin tanderu mai kuna. “Wanene allahn nan fa da za ya cece ku daga hannuna?” zolayar Nebuchadnezzar sarki mafi iko a duniya ke nan. (Daniel 3:15) Matasan uku suna da cikakken tabbaci ga ikon Allahnsu ya kāre su, amma ba su yi tsammanin cewa zai yi haka ba. Saboda haka, suka amsa: “In hakanan ne, Allahnmu wanda mu ke bauta masa, yana da iko ya cece mu.” (Daniel 3:17) Hakika, tanderu mai kuna, har ma lokacin da aka kara masa wuta sau bakwai fiye da yadda yake, bai zama kalubale ba ga Allahnsu mafi iko. Ya kāre su, kuma sarkin an tilasta masa ya fahimci cewa: “Babu wani allah wanda yake da iko shi yi ceto bisa ga wannan kwatanci.”—Daniel 3:29.

11 Jehovah ya ba da kwatanci na musamman na ikonsa na kāriya sa’ad da ya juya ran Dansa makadaici zuwa cikin budurwa Bayahudiya, Maryamu. Mala’ika ya gaya wa Maryamu cewa za ta yi “ciki, za [ta] haifi da.” Mala’ikan ya yi bayani: “Ruhu Mai-tsarki za ya auko miki, ikon Madaukaki kuma za ya inuwantadda ke.” (Luka 1:31, 35) Hakika, Dan Allah bai taba kasancewa a irin wannan yanayi mai hadari ba. Shin zunubi da ajizancin uwa talika za su shafi tayin ne? Shaidan zai iya ji ma ko kuma ya kashe Dan ne kafin a haife Shi? Ba zai yiwu ba! Jehovah ya yi ganuwa, garu domin kāriya ya kewaye Maryamu domin kada kome ya shafe shi—babu ajizanci, babu mugunta, ko kuma mutane masu kisa, ko aljani—da zai iya halaka tayi da yake girma, daga lokacin daukan ciki zuwa gaba. Jehovah ya ci gaba da kāre Yesu lokacin da yake saurayi. (Matta 2:1-15) Har sai lokaci da Allah ya ka’ide, Dansa da yake kauna ba abin da za a iya tabawa ba ne.

12. Me ya sa Jehovah ya kāre wasu mutane a zamanin Littafi Mai Tsarki?

12 Me ya sa Jehovah ya kāre wasu a irin wannan hanya ta mu’ujiza? Ko yaya dai Jehovah ya kāre wasu mutane domin ya kāre abin da ya fi muhimmanci: cika nufinsa. Alal misali, tsirar jariri Yesu tilas ne wajen cika nufin Allah, wanda nan take zai amfani dukan ’yan Adam. Tarihi da yawa da suka nuna iko na kāriya, sashe ne na hurarrun Nassosi, da “aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin hakuri da ta’aziyyar littattafai mu zama da bege.” (Romawa 15:4) Hakika, wadannan misalai suna karfafa bangaskiyarmu ga Allahnmu mafi iko. Amma wace kāriya za mu yi tsammani daga wajen Allah a yau?

Abin da Kāriyar Allah ba ta Nufa Ba

13. Tilas ne Jehovah ya yi mu’ujiza dominmu? Ka yi bayani.

13 Alkawarin kāriyar Allah ba ya nufin cewa tilas ne Jehovah ya yi mu’ujiza dominmu. A’a, Allahnmu bai ba mu tabbaci na rayuwa marar wahala ba a wannan tsohon zamanin. Bayin Jehovah masu aminci da yawa sun fuskanci wahala mai tsanani, hade da talauci, yaki, ciwo, da kuma mutuwa. Yesu ya fito fili ya gaya wa almajiransa cewa wasu za a kashe su domin bangaskiyarsu. Wannan shi ne dalilin da ya sa Yesu ya nanata bukatar jimiri har matuka. (Matta 24:9, 13) Idan Jehovah zai yi amfani da ikonsa ya yi kāriya ta mu’ujiza a kowanne yanayi, Shaidan zai samu dalilin yi wa Jehovah zolaya kuma ya tuhumi gaskiyar ibadarmu ga Allah.—Ayuba 1:9, 10.

14. Wadanne misalai suka nuna cewa Jehovah ba ya kāre dukan bayinsa a hanya iri daya?

14 Har a zamanin Littafi Mai Tsarki, Jehovah bai yi amfani da ikonsa na kāriya ba ya kāre kowanne bawansa daga mutuwa. Alal misali, Hirudus ya kashe manzo Yakub a shekara ta 44 A.Z.; ba da jimawa ba bayan haka, aka ceci Bitrus daga “hannun Hirudus.” (Ayukan Manzanni 12:1-11) Kuma Yohanna, dan’uwan Yakub, ya rayu fiye da Bitrus da kuma Yakub. Hakika, ba za mu yi tsammanin Allah zai kāre dukan bayinsa a hanya iri daya ba. Ban da haka, ‘sa’a da tsautsayi’ sukan sami kowannenmu. (Mai-Wa’azi 9:11) To, ta yaya Jehovah yake kāre mu a yau?

Jehovah Yana Ba da Kāriya ta Zahiri

15, 16. (a) Wane tabbaci ne da akwai cewa Jehovah ya kāre rukunin masu bauta masa a zahiri? (b) Me ya sa za mu tabbata cewa Jehovah zai kāre bayinsa yanzu da kuma a lokacin “babban tsananin”?

15 Da farko, ka yi la’akari da batun kāriya ta zahiri. Masu bauta wa Jehovah za su yi tsammanin irin wannan kāriyar a rukuninsu. Idan ba haka ba, da mun zama abinci mai saukin samu ga Shaidan. Ka yi tunani game da wannan: Shaidan, “mai-mulkin wannan duniya,” ba zai so wani abu ba sai dai ya kawar da bauta ta gaskiya. (Yohanna 12:31; Ru’ya ta Yohanna 12:17) Wasu gwamnatocin duniya masu iko suna hana mu aikin wa’azi kuma sun yi kokarin su shafe mu daga doron kasar gabaki daya. Duk da haka, mutanen Jehovah sun kasance da karfi kuma sun ci gaba da wa’azi ba tare da sanyin gwiwa ba! Me ya sa al’ummai masu karfi sun kasa hana wannan karamin rukuni na Kiristoci da kamar ba su da mai kāre su? Domin Jehovah ya kāre mu da fukafukansa masu karfi ne!—Zabura 17:7, 8.

16 To, kāriya ta zahiri lokacin “babban tsananin” da yake zuwa fa? Bai kamata mu ji tsoron hukuncin Allah ba. Ban da ma haka, “Ubangiji ya san yadda za ya ceci masu-ibada daga cikin jaraba, ya tsare marasa-adalci kuma karkashin hukunci har zuwa ranar shari’a.” (Ru’ya ta Yohanna 7:14; 2 Bitrus 2:9) Kafin nan, za mu iya kasancewa da tabbaci kullum game da abubuwa biyu. Na farko, Jehovah ba zai kyale a kau da bayinsa ba daga duniya. Na biyu, zai albarkaci wadanda suke da aminci da rai madawwami a sabuwar duniyarsa—idan ya zama dole, ta tashin matattu. Ga wadanda suka mutu, babu wajen kwanciyar rai kamar cikin tunanin Allah.—Yohanna 5:28, 29.

17. Ta yaya Jehovah yake kāre mu ta wurin Kalmarsa?

17 Har a yanzu ma, Jehovah yana kāre mu ta wurin ‘kalmarsa,’ wadda take da karfin motsawa ta warkar da zukata kuma ta canja rayuwa. (Ibraniyawa 4:12) Ta wajen amfani da mizananta, a wasu bangare za a kāre mu daga rauni na zahiri. “Ni ne Ubangiji . . . wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka,” in ji Ishaya 48:17. Babu shakka, rayuwa cikin jituwa da Kalmar Allah za ta iya ta kyautata lafiyarmu ta jiki kuma ta ba mu tsawon rai. Alal misali, domin muna amfani da gargadin Littafi Mai Tsarki mu guje wa fasikanci kuma mu tsarkake kanmu daga dukan kazanta, muna guje wa ayyuka da ba su da tsabta da kuma halaye masu lahani da suke halaka rayuwan mutane da yawa marasa ibada. (Ayukan Manzanni 15:29; 2 Korinthiyawa 7:1) Muna godiya domin kāriyar Kalmar Allah!

Jehovah Yana Kāre Mu a Ruhaniya

18. Wace kāriya ta ruhaniya Jehovah ya yi mana tanadinta?

18 Mafi muhimmanci, Jehovah yana kāre mu a ruhaniya. Allahnmu mai kauna yana kāre mu daga hadari ta wajen shirya mu da abubuwa da muke bukata domin mu jure wa gwaji kuma mu kāre dangantakarmu da shi. Da haka Jehovah yana kāre ranmu, ba kawai na dan shekaru ba amma na har abada. Ka yi la’akari da wasu abubuwa da Allah ya yi tanadinsu da za su iya kāre mu a ruhaniya.

19. Ta yaya ruhun Jehovah zai sa mu iya jimre da gwaji da za mu fuskanta?

19 Jehovah “mai-jin addu’a” ne. (Zabura 65:2) Sa’ad da matsi na rayuwa ya kasance kamar ya fi karfinmu, bude masa zuciyarmu zai sa mu samu saukin abin. (Filibbiyawa 4:6, 7) Ba zai cire mana gwajinmu ba ta mu’ujiza, amma wajen amsa addu’armu, zai ba mu hikima da za mu bi da shi. (Yakub 1:5, 6) Fiye da wannan, Jehovah yana ba da ruhu mai tsarki ga wadanda suka roke shi. (Luka 11:13) Wannan ruhu ne mai karfi da zai sa mu iya jimre gwaji ko matsala da za mu fuskanta. Zai iya ba mu “mafificin girman iko” mu jure har sai Jehovah ya cire dukan matsaloli masu azabtarwa a sabuwar duniya da ta yi kusa.—2 Korinthiyawa 4:7.

20. Ta yaya ikon kāriyar Jehovah za ta iya bayyana ta wajen ’yan’uwanmu masu bi?

20 Wani lokaci, ta wajen ’yan’uwanmu masu bi, ikon kāriyar Jehovah zai bayyana. Jehovah ya jawo mutanensa a dukan duniya zuwa zaman “’yan’uwanci.” (1 Bitrus 2:17; Yohanna 6:44) A tsakanin ’yan’uwancin, muna ganin tabbaci a zahiri na ikon ruhu mai tsarki na Allah, yana rinjayar mutane ga yin nagarta. Wannan ruhun yana ’ya’ya a cikinmu—kyawawa, halaye masu tamani da ya hada da kauna, kirki, da kuma nagarta. (Galatiyawa 5:22, 23) Saboda haka, sa’ad da muke wahala kuma wani dan’uwa mai bi ya motsa ya ba da shawara mai taimako ko kuma ya karfafa mu, za mu yi godiya ga Jehovah domin wannan kāriyarsa.

21. (a) Wane abinci na ruhaniya Jehovah yake tanadinsa ta wajen “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”? (b) Kai kanka ka taba amfana daga tanadi na Jehovah na kāre mu a ruhaniya?

21 Jehovah ya yi tanadin wani abu kuma don ya kare mu: abinci na ruhaniya a kan kari. Domin ya taimake mu mu sami karfi daga Kalmarsa, Jehovah ya umurci “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya ba da abinci na ruhaniya. Wannan bawa mai aminci yana amfani da littattafai, hade da jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake!, da kuma taro, manyan taro, da kuma taron gunduma domin ya ba mu ‘abinci a lokacinsa’—abin da muke bukata, lokacin da muke bukatarsa. (Matta 24:45) Ka taba jin wani abu a taron Kirista—a kalami, a jawabi, ko kuma a addu’a ma—da ya ba ka karfi da kuma karfafa da ka ke bukata? Wani talifi da aka buga a jaridunmu ya taba taba rayuwarka? Ka tuna, Jehovah yana yin dukan wannan tanadin domin ya kāre mu a ruhaniya.

22. A wace hanya Jehovah yake amfani da ikonsa koyaushe, kuma me ya sa yin hakan domin amfaninmu ne?

22 Babu shakka Jehovah garkuwa ne “ga dukan wadanda su ke dogara a gareshi.” (Zabura 18:30) Mun fahimci cewa ba ya yin amfani da ikonsa ya kāre mu daga dukan bala’i a yanzu. Amma, koyaushe yana amfani da ikonsa na kāriya ya tabbatar da nufinsa. A karshe, abin da ya yi zai kasance domin albarkar mutanensa. Idan muka matso kusa da shi kuma muka kasance cikin kaunarsa, Jehovah zai ba mu dawwama ta kamiltaccen rai. Da wannan a zuci, za mu iya daukan wahalar wannan tsari ‘mai-sauki ne kuma na dan lokaci.’—2 Korinthiyawa 4:17.