Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 8

Ikon Maidowa—Jehovah Yana “Sabonta Dukan Abu”

Ikon Maidowa—Jehovah Yana “Sabonta Dukan Abu”

1, 2. Wadanne rashi ne suke damun iyalin ’yan Adam a yau, kuma ta yaya wadannan suka shafe mu?

YARO ya batar ko kuma ya karya abin wasan da yake so, sai ya fashe da kuka. Karar tana taba rai! Ka taba ganin yadda fuskar yaro ta cika da murna sa’ad da ubansa ya gyara abin da ya lalace? Ga uban, zai iya zama al’amari ne mai sauki a nemi abin wasan ko kuma a gyara shi. Sai yaron ya cika da murna da kuma mamaki. Abin da kamar ya lalace har abada ya gyaru!

2 Jehovah, Ubanmu mafi girma, yana da ikon ya gyara abin da yaransa na duniya suke tsammani lalacewarsa ya wuce gyara. Hakika, ba ma nufin abin wasa kawai hakanan. A wadannan “miyagun zamanu,” dole ne mu fuskanci rashi da suka fi tsanani. (2 Timothawus 3:1-5) Abubuwa da mutane suke dauka da muhimmanci suna cikin hadari—gida, kayayyaki, har ma da lafiyar jiki. Za mu razana sa’ad da muka yi tunani game da halaka mahalli da kuma rashi da take jawowa, ta wajen karewar wasu irin abubuwa masu rai. Duk da haka, babu abin da ya fi damunmu kamar mutuwar wanda muke kauna. Jin mun yi rashi kuma ba mu da ikon maidowa yana iya shan kanmu.—2 Samu’ila 18:33.

3. Wane abu ne mai karfafa da ake tsammani, aka lissafa a Ayukan Manzanni 3:21, kuma ta wace hanya ce Jehovah zai cika wannan?

3 To ai abin farin ciki ne, mu koyi game da ikon maidowa na Jehovah! Kamar yadda za mu gani, da akwai abubuwa da yawa da Allah zai gyara wa yaransa na duniya. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehovah yana da nufin ya “mayarda kowane abu.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Ayukan Manzanni 3:21) Domin a cim ma wannan, Jehovah zai yi amfani da Mulkin Almasihu, da Dansa Yesu Kristi yake sarauta. Tabbaci ya nuna cewa wannan Mulkin ya fara sarauta a sama a shekara ta 1914. * (Matta 24:3-14) Menene za a mayar? Bari mu bincika wasu cikin manyan ayyukan maidowa na Jehovah. Daya cikin wadannan mun riga mun gani kuma mun fuskanta. Wasu za su faru a nan gaba.

Maido da Tsarkakkiyar Bauta

4, 5. Menene ya faru da mutanen Allah a shekara ta 607 K.Z., kuma wane bege Jehovah ya ba su?

4 Aba daya da Jehovah ya riga ya maido da ita, ita ce tsarkakkiyar bauta. Domin mu fahimci abin da wannan take nufi, bari mu bincika tarihin sarautar Yahuda kadan. Yin haka zai ba mu fahimi mai ban mamaki game da ikon maidowa na Jehovah da ke aiki.—Romawa 15:4.

5 Ka yi tunanin yadda Yahudawa masu aminci suka ji a shekara ta 607 K.Z., sa’ad da aka halaka Urushalima. Birninsu da suke kauna an ragargaza shi, ganuwarsa an rushe ta. Mafi barna, haikali mai daukaka da Sulemanu ya gina, cibiyar tsarkakkiyar bauta ta Jehovah a dukan duniya, ya zama kango. (Zabura 79:1) Wadanda suka tsira an kwashe su zuwa bauta a Babila, an bar kasarsu ta zama kango wajen zaman namun daji. (Irmiya 9:11) Ga mutanen, kome ya lalace. (Zabura 137:1) Amma Jehovah, wanda da dadewa ya annabta wannan halaka, ya ba da bege cewa lokacin maidowa yana gaba.

6-8. (a) Wane jigo ne da aka yi ta maimaitawa za a samu a cikin rubuce-rubuce na annabawa Ibraniyawa, kuma ta yaya wadannan annabce-annabce suka samu cikarsu ta farko? (b) A zamanin yau, ta yaya mutanen Allah suka ga cikar annabce-annabce na maidowa?

6 Hakika, maidowa jigo ne da aka yi ta maimaitawa a rubuce-rubucen annabawa Ibraniyawa. * Ta bakinsu, Jehovah ya yi alkawarin za a gyara kasar kuma ta cika da mutane, ta zama mai albarka, kuma a kāre ta daga namun daji da kuma farmakin abokan gaba. Ya kwatanta kasarsu da aka gyara da aljanna ta gaske! (Ishaya 65:25; Ezekiel 34:25; 36:35) Mafi muhimmanci, za a sake kafa tsarkakkiyar bauta, a kuma sake gina haikalin. (Mikah 4:1-5) Wadannan annabce-annabcen sun bai wa Yahudawa da suke hijira bege, sun kuma taimake su su jure bautarsu ta shekara 70 a Babila.

7 A karshe, lokacin maidowa ya zo. Da aka ’yantar da su daga Babila, Yahudawan suka koma Urushalima suka sake gina haikalin Jehovah a can. (Ezra 1:1, 2) Idan suka rike tsarkakkiyar bauta, Jehovah yana yi musu albarka kuma yana yi wa kasarsu albarka kuma ta bunkasa. Ya kāre su daga abokan gaba da kuma namun daji da suka mamaye kasar na shekaru da yawa. Lallai za su yi murna da ikon maidowa na Jehovah! Amma wadannan aukuwa cika ce kawai ta farko, cika ce kawai kadan na annabce-annabce masu yawa na maidowa. Cika mai girma tana zuwa “a cikin kwanaki na karshe,” lokacinmu, sa’ad da Magajin Sarki Dauda da ake jira da dadewa zai hau gadon sarauta.—Ishaya 2:2-4; 9:6, 7.

8 Ba da dadewa ba bayan an dora Yesu bisa gadon sarauta a mulkin sama a shekara ta 1914 A.Z., ya mai da hankali ga bukatu na ruhaniya na mutanen Allah masu aminci a duniya. Kamar yadda jarumi na Pashiya Cyrus ya ’yantar da raguwar Yahudawa daga Babila a shekara ta 537 K.Z., Yesu ya ’yantar da raguwar Yahudawa na ruhaniya—wadanda suke bin sawunsa—daga rinjayar Babila ta zamani, daular duniya ta addinin karya. (Romawa 2:29; Ru’ya ta Yohanna 18:1-5) Daga shekara ta 1919 A.Z., zuwa gaba, tsarkakkiyar bauta an mai da ita wajen da ta dace a rayukan Kiristoci na gaskiya. (Malachi 3:1-5) Tun daga wannan lokacin, mutanen Jehovah suna bauta masa a cikin haikalinsa na ruhaniya mai tsabta—tsarin tsarkakkiyar bauta. Me ya sa wannan yake da muhimmanci a gare mu a yau?

Maidowa ta Ruhaniya—Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci

9. Bayan zamanin manzanni, menene cocin Kiristendam suka yi wa bautar Allah, amma kuma menene Jehovah ya yi a zamaninmu?

9 Ka yi la’akari da tsari na tarihi. Kiristoci a can karni na farko sun more albarka da yawa a ruhaniya. Amma Yesu da manzanninsa sun yi annabci cewa za a lalata bauta ta gaskiya kuma za ta bace. (Matta 13:24-30; Ayukan Manzanni 20:29, 30) Bayan zamanin manzanni, Kiristendam ya bayyana. Limamansa suka karbi koyarwar arna da kuma ayyukansu. Kuma suka sa yi wa Allah addu’a ya gagara, domin sun kwatanta shi da cewa Allah Uku ne Cikin Daya da ba za a fahimta ba kuma sun koyar da mutane su yi ikirari ga firist, su yi addu’a ga Maryamu da kuma wasu “waliyai” maimakon ga Jehovah. To, bayan karnuka na wannan lalata, menene Jehovah ya yi? A cikin duniya ta zamani—duniya da ta cunkushe da karyace-karyace na addini da ayyuka marasa tsarki—ya saka hannu ta maido da tsarkakkiyar bauta! Ba tare da karin gishiri ba, za mu iya cewa wannan maidowa tana daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci na wannan zamani.

10, 11. (a) Wadanne abubuwa biyu ne aljannarmu ta ruhaniya ta kunsa, kuma ta yaya sun shafe mu? (b) Wadanne irin mutane Jehovah ya tara a cikin aljanna ta ruhaniya, kuma menene za su sami gatar gani?

10 Saboda haka, Kiristoci na gaskiya a yau suna more aljanna ta ruhaniya. Me wannan aljannar ta kunsa? Ainihi, abubuwa biyu ne. Na farko tsarkakkiyar bauta ta Allah na gaskiya, Jehovah. Ya albarkace mu da hanyar bauta da babu karya ko wala-wala. Ya albarkace mu da abinci na ruhaniya. Wannan ya taimake mu mu koyi game da Ubanmu na samaniya, mu faranta masa rai, kuma mu kusace shi. (Yohanna 4:24) Sashe na biyu na aljannarmu ta ruhaniya ta kunshi mutane. Kamar yadda Ishaya ya annabta a “kwanaki na karshe,” Jehovah ya koya wa masu bauta masa hanyar salama. Ya kawar da yake-yake tsakaninmu. Duk da ajizancinmu, ya taimake mu mu yafa “sabon mutum.” Ya albarkaci kokarce-kokarcenmu da ruhunsa mai tsarki, wanda yake ba da ’ya’ya a cikinmu. (Afisawa 4:22-24; Galatiyawa 5:22, 23) Idan ka yi aiki cikin jituwa da ruhun Allah, lallai kana cikin aljanna ta ruhaniya.

11 Jehovah ya tara cikin aljanna ta ruhaniya irin mutane da yake kauna—wadanda suke kaunarsa, suke kaunar salama, kuma wadanda suka “san talaucinsu na ruhu.” (Matta 5:3) Irin wadannan mutane ne za su sami gatar su ga maidowa ta musamman—na ’yan Adam da kuma dukan duniya.

“Duba, Sabonta Dukan Abu Ni Ke Yi”

12, 13. (a) Me ya sa annabce-annabce na maidowa har yanzu za su sake cika? (b) Menene nufin Jehovah game da duniya kamar yadda ya ce a Adnin, kuma me ya sa wannan ya ba mu bege domin nan gaba?

12 Da yawa cikin annabce-annabce na maidowa ba maidowa ta ruhaniya kawai yake nufi ba. Alal misali, Ishaya ya rubuta game da lokaci da marasa lafiya, guragu, makafi, da kuma kurame za su warke, har mutuwa kanta za a hadiye ta har abada. (Ishaya 25:8; 35:1-7) Wadannan alkawura ba su cika ba a zahiri a Isra’ila ta dā. Ko da yake mun ga cika ta ruhaniya na wadannan alkawura a zamaninmu, muna da kyakkyawar dalili na gaskata cewa a nan gaba, za su cika sosai a zahiri. Ta yaya muka san wannan?

13 A Adnin, Jehovah ya bayyana sarai nufinsa game da duniya: Domin mutane masu farin ciki, masu hadin kai, masu koshin lafiya, su zauna cikinta ne. Mata da mijin za su kula da duniya da kuma dukan halittun da suke cikinta, kuma su mai da dukan duniya ta zama aljanna. (Farawa 1:28) Wannan ya bambanta kwarai da yadda abubuwa suke a yau. Amma za mu tabbata cewa nufe-nufen Allah ba su lalace ba. (Ishaya 55:10, 11) Yesu, Sarki Almasihu wanda Jehovah ya nada, zai kawo wannan Aljanna ta duniya.—Luka 23:43.

14, 15. (a) Ta yaya Jehovah zai “sabonta dukan abu”? (b) Yaya rayuwa za ta kasance a Aljanna, kuma wacce ka fi sha’awarta?

14 Ka yi tunanin ganin dukan duniya ta zama Aljanna! Jehovah ya ce game da wannan lokaci: “Duba, sabonta dukan abu ni ke yi.” (Ru’ya ta Yohanna 21:5) Ka yi la’akari da abin da wannan yake nufi. Sa’ad da Jehovah ya gama nuna ikonsa na halaka bisa wannan mugun tsohon zamani, zai rage “sababbin sammai da sabuwar duniya.” Wannan yana nufin cewa sabuwar gwamnati za ta yi sarauta daga sama bisa sabuwar duniya ta mutane wadanda suke kaunar Jehovah kuma suke yin nufinsa. (2 Bitrus 3:13) Shaidan, da aljannunsa, za su shiga zaman kashe wando. (Ru’ya ta Yohanna 20:3) Tun farko, a shekara dubun, ’yan Adam za su samu sukuni daga rinjaya ta lalata, mugunta, da barna. Lallai jin an samu sauki zai kasance kwarai.

15 A karshe za mu iya kula da wannan duniyar kamar yadda ainihi aka nufe mu da yi. Duniya tana da ikon gyara kanta. Gurbatattun tafkuna da kuma koguna za su iya tsabtace kansu idan aka kawar da tushen gurbatar; idan yaki ya kare, kasa da aka bata da yaki ta gyaru. Abin farin ciki ne a yi aiki cikin jituwa da dokokin halittar duniya, taimaka a mai da ita lambu, Adnin na dukan duniya cike da halittu iri-iri! Maimakon halaka dabbobi da itatuwa, mutum zai kasance cikin salama da dukan halitta a duniya. Har yara ma ba za su tsorata ba da namun daji.—Ishaya 9:6, 7; 11:1-9.

16. A cikin Aljanna, wace gyara ce za ta taba kowanne mutum mai aminci?

16 Za mu kuma ga gyara da kanmu. Bayan Armageddon, wadanda suka tsira za su ga warkarwa ta mu’ujiza a dukan duniya. Kamar yadda ya yi sa’ad da yake duniya, Yesu zai yi amfani da ikon da Allah ya ba shi ya maido da gani ga makafi, ji ga kurame, lafiya ga guragu da nakasassu. (Matta 15:30) Tsofaffi za su yi murna cikin karfi na kuruciya da kuma lafiya da kuzari. (Ayuba 33:25) Tamoji zai bace, gabobi za su mike, kuma tsoka za ta cika da sabon karfi. Dukan ’yan Adam masu aminci za su ji cewa sakamakon zunubi yana karewa a hankali, yana bacewa. Za mu gode wa Jehovah Allah domin ikonsa na maidowa! Bari yanzu mu mai da hankali ga bangare daya na lokaci mai ban mamaki na maidowa.

Mai da Rai ga Matattu

17, 18. (a) Me ya sa Yesu ya yi wa Saddukiyawa gargadi? (b) Wane yanayi ne ya sa Iliya ya roki Jehovah ya tashi matacce?

17 A karni na farko A.Z., wasu shugabannan addini da ake kira Saddukiyawa ba su yarda da tashin matattu ba. Yesu ya yi musu gargadi da wadannan kalmomi: “Kun kuskure, don rashin sanin Littattafai da ikon Allah kuma.” (Matta 22:29) Hakika, Nassosi sun nuna cewa Jehovah yana da irin wannan iko na maidowa. Yaya haka?

18 Ka yi tunanin abin da ya faru a zamanin Iliya. Gwauruwa tana rungume da mamacin danta a hannu. Yaron ya mutu. Annabi Iliya, wanda bakon gwauruwar ne na dan lokaci, babu shakka abin ya taba masa zuciya. Da farko, ya taimaka ya ceci yaron daga yunwa. Kuma watakila Iliya yana kaunar dan yaron. Abin ya taba wa uwar rai. Yaron shi ne kawai abin da yake tuna mata mijinta da ya mutu. Watakila tana sa rai cewa idan ta tsufa zai taimake ta. A rikice, gwauruwar ta tsorata cewa ko horo ake yi mata ne na wani kuskure da ta yi a dā. Iliya ya kasa jimrewa ya ga wannan bala’i ya yi tsanani. Ya dauki gawar a hankali daga kirjin uwar zuwa dakinsa, kuma ya roki Jehovah Allah ya mai da wa yaron ransa.—1 Sarakuna 17:8-21.

19, 20. (a) Ta yaya Ibrahim ya nuna yana da bangaskiya ga ikon Jehovah na maidowa, kuma menene dalilin irin wannan bangaskiyar? (b) Ta yaya Jehovah ya albarkaci bangaskiyar Iliya?

19 Iliya ba shi ne mutum na farko ba da ya gaskata da tashin matattu. Shekaru da yawa kafin haka, Ibrahim ya gaskata cewa Jehovah yana da ikon maidowa—kuma yana da kyakkyawar dalilin haka. Sa’ad da Ibrahim yake dan shekara 100 kuma Saratu take ’yar shekara 90, Jehovah ya mai da musu ikon haihuwa, cikin mu’ujiza Saratu ta haifi da. (Farawa 17:17; 21:2, 3) Daga baya, sa’ad da ya isa mutum, Jehovah ya ce wa Ibrahim ya yi hadaya da dansa. Ibrahim ya nuna bangaskiya, ya tabbata cewa Jehovah zai iya maido da Ishaku wanda yake kauna zuwa rai. (Ibraniyawa 11:17-19) Irin wannan bangaskiya ta bayyana dalilin da ya sa Ibrahim, kafin ya hau dutsen ya mika dansa, ya tabbatar wa bayinsa cewa shi da Ishaku za su komo tare.—Farawa 22:5.

“Ga danki, yana da rai”!

20 Jehovah ya rayar da Ishaku, saboda haka babu bukatar tashin wani matacce a wannan lokacin. A lokacin Iliya kuma, dan gwauruwar ya riga ya mutu—amma ba da dadewa ba. Jehovah ya albarkaci annabinsa ta wajen ta da yaron! Sai Iliya ya ba da yaron ga uwarsa, da wadannan kalmomi da suka fi gaban mantuwa: “Ga danki, yana da rai”!—1 Sarakuna 17:22-24.

21, 22. (a) Menene dalilin tashin matattu da aka rubuta a cikin Nassosi? (b) A cikin Aljanna, yaya yawan tashin matattu zai kasance, kuma wa zai yi shi?

21 Saboda haka lokaci na farko ke nan cikin Littafi Mai Tsarki, muka ga Jehovah ya yi amfani da ikonsa ya maido da ran mutum. Daga baya Jehovah ya ba wa Elisha, Bitrus, Bulus, da kuma Yesu ikon maida matattu zuwa rai. Hakika, wadanda aka ta da su daga matattu sun sake mutuwa. Duk da haka, irin wadannan tarihi na Littafi Mai Tsarki sun nuna mana abubuwa masu ban mamaki da za su zo a nan gaba.

22 A cikin Aljanna, Yesu zai cika aikinsa na ‘ta da matattu zuwa rai.’ (Yohanna 11:25) Zai ta da miliyoyi da yawa, a ba su damar rayuwa har abada cikin Aljanna a duniya. (Yohanna 5:28, 29) Ka yi tunanin abokane da ’yan’uwa, da mutuwa ta raba su da dadewa, suna rungumar juna, suna farin ciki kwarai! Dukan mutane za su yabi Jehovah domin ikonsa na maidowa.

23. Wannene nuna iko mafi girma na Jehovah, kuma ta yaya wannan ya ba da tabbaci ga begenmu na nan gaba?

23 Jehovah ya ba da tabbacin cewa wannan bege tabbatacce ne. A wajen nuna iko mafi girma duka, ya ta da Dansa, Yesu, zuwa ruhu mai girma, ya mai da shi na biyu wajen matsayi bayan Jehovah. Yesu da ya tashi daga matattu ya bayyana ga mutane darurruwa da suka gan shi. (1 Korinthiyawa 15:5, 6) Har ga ’yan shakka, wadannan alamu sun isa. Jehovah yana da ikon ya mai da rai.

24. Me ya sa za mu tabbata cewa Jehovah zai ta da matattu, kuma wane bege ne kowannenmu ya kamata ya yi kaunarsa?

24 Ba kawai Jehovah yana da ikon ya ta da matattu ba amma kuma yana da muradin yin haka. An hure mutum mai aminci Ayuba ya ce Jehovah yana marmarin ya maido da matattu zuwa rai. (Ayuba 14:15) Ba ka yi sha’awar kusantar Allah ba, wanda yake dokin ya yi amfani da ikonsa na maidowa a wannan hanya ta kauna? Ka tuna fa cewa tashin matattun, hanya daya ce a ayyukan maidowa masu girma na Jehovah da suke nan gaba. Yayin da ka matso kusa da shi, koyaushe ka kaunaci bege mai tamani na cewa za ka kasance a wurin, ka ga Jehovah ya “sabonta dukan abu.”—Ru’ya ta Yohanna 21:5.

^ sakin layi na 3 “Zamanin mayarda kowane abu” ya fara sa’ad da aka kafa Mulkin Almasihu magajin Sarki Dauda mai aminci a kan kujerar sarauta. Jehovah ya yi wa Dauda alkawari cewa wani magajinsa zai yi sarauta har abada. (Zabura 89:35-37) Amma bayan Babila ta halaka Urushalima a shekara ta 607 K.Z., babu dan Dauda da ya zauna a gadon sarauta na Allah. Yesu, wanda aka haife shi a duniya magajin Dauda, shi ya zama Sarki da ake saurara da dadewa da aka dora shi a gadon sarauta a sama.

^ sakin layi na 6 Alal misali, Musa, Ishaya, Irmiya, Ezekiel, Hosea, Joel, Amos, Obadiah, Mikah, da Zephaniah dukansu sun yi magana a kan wannan jigon.