Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 10

“Ku Zama fa Masu-Koyi da Allah” Wajen Amfani da Iko

“Ku Zama fa Masu-Koyi da Allah” Wajen Amfani da Iko

1. Ga wane tarko ne mutane ajizai suke fadāwa ciki da sauki?

“BABU ikon da ba shi da tarko.” Wadannan kalmomin zabiya ta karni na 19 sun jawo hankali ga hadari da ke boye: yin barna da iko. Abin bakin ciki, mutum ajizi ba wuya ya fadā cikin wannan tarkon. Hakika, a duk cikin tarihi “mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya ciwuce shi.” (Mai-Wa’azi 8:9) Nuna iko ba tare da kauna ba ya kai ga wahalar da babu iyaka na ’yan Adam.

2, 3. (a) Menene abin ban mamaki game da nuna iko na Jehovah? (b) Menene ikonmu ya kunsa, kuma yaya ya kamata mu nuna dukan irin wadannan ikon?

2 Amma ba abin mamaki ba ne cewa Jehovah Allah, wanda yake da iko marar iyaka, bai taba barna ba da ikonsa? Kamar yadda muka lura a babobi da suka shige, yana amfani da ikonsa—ko na halitta ne, ko na halaka, ko na kāriya, ko na maidowa—cikin jituwa da nufe-nufensa na kauna. Sa’ad da muka yi tunani game da yadda yake nuna ikonsa, mun motsa mu kusace shi. Hakan kuma zai motsa mu mu zama “masu-koyi da Allah” wajen amfani da iko. (Afisawa 5:1) Amma wane iko mu mutane raunanu muke da shi?

3 Ka tuna cewa an halicci mutum cikin ‘surar’ Allah da kuma kamaninsa. (Farawa 1:26, 27) Saboda haka, muna da iko—akalla dan kadan. Ikonmu zai hada da iyawarmu mu cim ma abubuwa, mu yi aiki; iko bisa wasu; iyawarmu mu rinjayi wasu, musamman ma wadanda suke kaunarmu; karfi na jiki; ko kuma arziki. Game da Jehovah, mai Zabura ya ce: “Wurinka mabulbular rai ta ke.” (Zabura 36:9) Saboda haka, ko kai tsaye ko a’a, Allah shi ne tushen kowane iko mai kyau da muke da shi. Saboda haka, muna so mu yi amfani da shi a hanya mai kyau da zai faranta masa rai. Ta yaya za mu yi wannan?

Kauna Ita ce Mabudi

4, 5. (a) Menene mabudin nuna iko yadda ya dace, kuma yaya misalin Allah kansa ya nuna haka? (b) Ta yaya kauna za ta taimake mu mu yi amfani da ikonmu yadda ya dace?

4 Mabudin nuna iko yadda ya dace kauna ce. Misalin Allah bai nuna haka ba ne? Ka tuna da tattauna halayen Allah hudu na musamman—iko, shari’a, hikima, da kuma kauna—a cikin Babi na 1. A cikin halayen hudu, wanne ne ya fi? Kauna. “Allah kauna ne,” in ji 1 Yohanna 4:8. Hakika, Jehovah kansa kauna ne; tana rinjayar dukan abin da yake yi. Saboda haka, dukan nuna ikonsa kauna ce take motsa shi kuma domin amfanin wadanda suke kaunarsa ne.

5 Kauna za ta taimake mu mu yi amfani da ikonmu yadda ya dace. Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa kauna tana da “nasiha” kuma “ba ta bida ma kanta.” (1 Korinthiyawa 13:4, 5) Saboda haka, kauna ba za ta kyale mu mu yi zafin hali ko mugunta ba ga wadanda muke da dan iko a kansu. Maimakon haka, za mu bi da wasu da daraja kuma mu saka muradinsu da kuma yadda suke ji gaba da namu.—Filibbiyawa 2:3, 4.

6, 7. (a) Menene tsoron Allah ya kunsa, kuma me ya sa wannan halin zai taimake mu mu guji yin barna da iko? (b) Ka kwatanta dangantakar da take tsakanin tsoron mu bata wa Allah rai da kuma kaunar Allah.

6 Kauna tana da dangantaka da wani hali da zai taimake mu mu guji yin barna da iko: tsoron Allah. Menene muhimmancin wannan halin? “Ta wurin tsoron Ubangiji kuma mutane su kan rabu da mugunta,” in ji Misalai 16:6. Yin barna da iko hakika yana cikin mugunta da ya kamata mu rabu da ita. Tsoron Allah zai hana mu zaluntar wadanda muke da iko a kansu. Me ya sa? Abu daya shi ne, mun san cewa Allah zai yi mana hisabi game da yadda muka bi da irin wadannan. (Nehemiah 5:1-7, 15) Amma tsoron Allah ya kunshi fiye da haka. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya danganta tsoro da kaunar Allah. (Kubawar Shari’a 10:12, 13) Wannan daraja Allah ta hada da tsoro da ya dace na kin bakanta wa Allah rai—ba domin muna tsoron sakamakon hakan ba amma domin muna kaunarsa da gaske.

7 Alal misali: Ka yi tunanin dangantaka mai kyau tsakanin yaro da ubansa. Yaron zai fahimci cewa ubansa yana kaunarsa. Amma yaron ya san abin da ubansa yake bukata a gare shi, kuma ya san cewa ubansa zai yi masa horo idan ya yi rashin hankali. Yaron ba zai razana ba idan ya ga ubansa. Maimakon haka, zai yi kaunar ubansa kwarai da gaske. Matashin yana farin ciki wajen yin abin da zai kawo yardan ubansa. Haka yake da tsoron Allah. Domin muna kaunar Jehovah, Ubanmu na samaniya, muna tsoron yin abin da zai “bata masa zuciya.” (Farawa 6:6) Maimakon haka, muna so mu sa ya yi farin ciki. (Misalai 27:11) Abin da ya sa ke nan muke so mu nuna ikonmu yadda ya dace. Bari mu bincika yadda za mu yi hakan.

A Cikin Iyali

8. (a) Wane iko magidanta suke da shi bisa iyali, kuma ta yaya za su nuna ikon? (b) Ta yaya maigida zai nuna cewa yana girmama matarsa?

8 Da farko, ka yi la’akari da iyali. “Miji kan mata ya ke,” in ji Afisawa 5:23. Ta yaya maigida zai nuna ikon da Allah ya ba shi? Littafi Mai Tsarki ya gaya wa magidanta su zauna da matansu bisa “sani, kuna bada girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin karfi.” (1 Bitrus 3:7) Kalmar suna ta Helenanci da aka fassara “girmamawa” tana nufin “tamani, . . . daraja.” Wasun wannan kalmar an fassara su ‘kyauta’ da kuma ‘tamani.’ (Ayukan Manzanni 28:10; 1 Bitrus 2:7) Maigida da yake girmama matarsa ba zai taba bugunta ba; ko kuma ya kaskantar da ita, ya sa ta ji ba ta da amfani. Maimakon haka, zai fahimci tana da tamani kuma ya bi da ita da daraja. Zai nuna cikin kalmomi da kuma ayyuka—a boye da a fili—tana da tamani. (Misalai 31:28) Irin wannan maigida ba kawai matarsa za ta yi kaunarsa kuma ta yi masa ladabi ba, amma mafi muhimmanci, zai sami yardar Allah.

Mata da magidanta suna amfani yadda ya dace da ikonsu ta wajen bi da juna da kauna da kuma daraja

9. (a) Wane iko mata suke da shi a cikin iyali? (b) Menene zai taimaki mace ta yi amfani da iyawarta ta tallafa wa mijinta, kuma da wane sakamako?

9 Mata ma suna da dan iko a cikin iyali. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da mata masu ibada wadanda ba tare da taka dokar shugabanci ba, suka rinjayi mazansu zuwa hanya mai kyau ko kuma suka taimake su suka guje wa yin kuskure. (Farawa 21:9-12; 27:46–28:2) Watakila mace ta fi mijinta fahimi, ko kuma tana da wasu halaye da ba shi da su. Duk da haka, ta kasance da “kwarjinin” mijinta kuma ta yi “zaman biyayya” da shi “kamar ga Ubangiji.” (Afisawa 5:22, 33) Tunanin tana so ta faranta wa Allah rai zai iya taimakon matar ta yi amfani da iyawarta ta tallafa wa mijinta, maimakon raina shi ko kuma kokarin ta shugabance shi. Irin wannan “mace mai-hikima” tana ba da hadin kai ga mijinta su gina iyalinsu. Ta haka za ta kasance da salama da Allah.—Misalai 14:1.

10. (a) Wane iko Allah ya ba wa iyaye? (b) Menene ma’anar kalmar nan “horo,” kuma yaya ya kamata a yi shi? (Dubi hasiya.)

10 Iyaye suna da ikon da Allah ya ba su. Littafi Mai Tsarki ya yi gargadi: “Ku ubanni kuma, kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargadinsa.” (Afisawa 6:4) A cikin Littafi Mai Tsarki, “horo” yakan nufi “reno, koyarwa, umurni.” Yara suna bukatar horo; sun fi farin ciki in aka kafa musu ka’ida, da iyaka. Littafi Mai Tsarki ya nasabta horo, ko umurni, da kauna. (Misalai 13:24) Saboda haka, kada a yi barna da “sandar horo”—a motsin rai ko kuma a jiki. * (Misalai 22:15; 29:15) Horo mai tsanani ba tare da kauna ba barna ne da iko na iyaye kuma zai raunana ruhun tuba na yaro. (Kolossiyawa 3:21) A wani bangare kuma, horo da ya dace idan aka yi shi yana nuna wa yara cewa iyayensu suna kaunarsu kuma sun damu da irin mutane da za su zama.

11. Ta yaya yara za su yi amfani da ikonsu yadda ya dace?

11 Yara kuma fa? Ta yaya za su yi amfani da ikonsu yadda ya dace? “Fahariyar samari karfinsu ne,” in ji Misalai 20:29. Hakika babu wata hanya da ta fi cewa matasa su yi amfani da karfinsu da kuzari fiye da bauta wa ‘Mahaliccinmu.’ (Mai-Wa’azi 12:1) Ya kamata matasa su tuna cewa abin da suke yi zai shafi iyayensu. (Misalai 23:24, 25) Idan yara suka yi wa iyayensu masu ibada biyayya suka bi hanya mai kyau, suna faranta wa iyayensu zuciya. (Afisawa 6:1) Irin wannan hali “abin yarda ne cikin Ubangiji.”—Kolossiyawa 3:20.

A Cikin Ikilisiya

12, 13. (a) Yaya dattawa ya kamata su dauki ikonsu a cikin ikilisiya? (b) Ka kwatanta dalilin da ya sa dattawa ya kamata su kula da tumakin da kyau.

12 Jehovah ya yi tanadin dattawa su yi ja-gora a cikin ikilisiyar Kirista. (Ibraniyawa 13:17) Wadannan kwararrun mutane ya kamata su yi amfani da ikon da Allah ya ba su, su ba da taimako kuma su ba da gudummawa domin lafiyar garken. Shin matsayinsu na dattawa don su yi sarauta ne bisa ’yan’uwa masu bi? A’a! Dattawa suna bukatar su fahimci daidai matsayinsu cikin tawali’u a ikilisiya. (1 Bitrus 5:2, 3) Littafi Mai Tsarki ya gaya wa dattawa: “Ku yi kiwon ikilisiyar Allah, wadda ya sayi da jinin [Dansa].” (Ayukan Manzanni 20:28) Wannan babban dalilin ya sa ya kamata a bi da kowanne cikin garken da kyau.

13 Za mu iya kwatanta shi a wannan hanyar. Aboki na kud da kud ya ba ka amanar abin da yake kauna kwarai. Kuma ka sani cewa abokinka ya sayi abin da tsada. Ba za ka kula da abin sosai ba kuma ka mai da hankali a kansa? Hakazalika, Allah ya ba wa dattawa hakkin kula da abin da yake so kwarai: ikilisiya, wadda wadanda suke cikinta an kwatanta su da tumaki. (Yohanna 21:16, 17) Jehovah yana kaunar tumakinsa kwarai—yana kaunarsu kwarai da gaske, saboda haka ya saye su da jini mai tamani na Dansa makadaici, Yesu Kristi. Jehovah ya saye su da tsada kwarai. Dattawa masu tawali’u suna tuna da wannan kuma su kula da tumakin Jehovah da kyau.

“Ikon Harshe”

14. Wane iko harshe yake da shi?

14 “Mutuwa da rai suna cikin ikon harshe,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Misalai 18:21) Hakika, harshe zai iya yin barna kwarai. Waye a cikinmu bai taba yin bakin ciki ba domin bakar magana? Amma harshe kuma yana da ikon yin gyara. “Harshen mai-hikima lafiya ne,” in ji Misalai 12:18. Hakika, kalmomi masu karfafawa za su iya zama kamar man zuciya. Bari mu bincika wasu misalai.

15, 16. A wadanne hanyoyi ne za mu yi amfani da harshenmu wajen karfafa wasu?

15 “Ku karfafa masu-raunanan zukata,” yadda 1 Tassalunikawa 5:14 ta aririta. Hakika, har amintattun bayin Jehovah wani lokaci za su yi ta jimrewa da raunanniyar zuciya. Ta yaya za mu taimaki irin wadannan mutane? Ka yi yabo takamamme na kwarai ka taimaka musu su ga suna da amfani a idanun Jehovah. Ka nuna musu ayoyin Littafi Mai Tsarki masu karfi da suka nuna cewa Jehovah da gaske yana kaunarsu kuma yana kula da “masu-karyayyar zuciya” da kuma “wadanda su ke da ruhu mai-tuba.” (Zabura 34:18) Idan muka yi amfani da ikon harshenmu muka karfafa wasu, muna nuna cewa muna koyi da Allahnmu mai tausayi, “wanda ya ke yi wa masu raunanar zuciya ta’aziyya.”—2 Korinthiyawa 7:6, New American Standard Bible.

16 Mu ma za mu iya yin amfani da ikon harshenmu mu ba da karfafa da wasu suke bukata. Wani dan’uwa mai bi ya yi rashin wani wanda yake kauna ne? Kalmominmu na ta’aziyya da suke nuna damuwarmu da kuma kauna za su iya karfafa zuciya da take makoki. Wani dan’uwa ko wata ’yar’uwa yana ko tana jin ba a bukatarta? Mai maganar kirki zai iya tabbatar wa tsofaffi suna da tamani kuma ana kaunarsu. Akwai wanda yake fama da ciwo mai tsanani? Maganar alheri a tarho ko kuma fuska da fuska za ta taimaka wa wanda yake ciwon. Mahaliccinmu zai yi murna idan muka yi amfani da ikon magana wajen furta magana da suke “mai-kyau garin ginawa”!—Afisawa 4:29.

Ba da bishara—muhimmiyar hanya ce ta yin amfani da ikonmu

17. A wace muhimmiyar hanya ce za mu iya amfani da harshenmu mu amfani wasu, kuma me ya sa za mu yi haka?

17 Babu wata hanya da ta fi muhimmanci wajen amfani da ikon harshe fiye da gaya wa wasu bisharar Mulkin Allah. “Kada ka hana alheri ga wadanda ya wajibce su, lokacin da yana cikin ikon hannunka da za ka aika,” in ji Misalai 3:27. Wajibinmu ne mu gaya wa wasu bishara mai ceton rai. Ba zai dace ba mu rufe bakinmu ga sako na gaggawa da Jehovah ya ba mu hannu sake. (1 Korinthiyawa 9:16, 22) Amma har yaya Jehovah yake so mu yi wannan aikin?

Bauta wa Jehovah da “Dukan Karfinmu”

18. Menene Jehovah yake zato wajenmu?

18 Kauna da muke yi wa Jehovah tana motsa mu mu shagala cikin hidimar Kirista. Menene Jehovah yake bukata wajenmu game da wannan? Abin da dukanmu, ko yaya yanayinmu a rayuwa za mu iya bayarwa: “Iyakar abin da ku ke yi, ku aika da zuciya daya kamar ga Ubangiji, ba ga mutane ba.” (Kolossiyawa 3:23) Wajen fadar doka mafi girma, Yesu ya ce: “Ka yi kaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka, da dukan karfinka.” (Markus 12:30) Hakika, Jehovah yana bukatar kowannenmu ya yi kaunarsa kuma ya bauta masa da dukan ransa.

19, 20. (a) Tun da rai ya kunshi zuciya, da azanci, da kuma karfi, me ya sa aka ambaci wadannan a Markus 12:30? (b) Me yake nufi a bauta wa Jehovah da dukan rai?

19 Menene yake nufi a bauta wa Allah da dukan rai? Ran yana nufin mutumin ne dungum, da dukan iyawarsa na zahiri da basira. Tun da ran ya kunshi zuciya, azanci, da kuma karfi, me ya sa aka lissafa su a Markus 12:30? Ka ga wannan misalin. A zamanin Littafi Mai Tsarki, mutum zai iya sayar da kansa (ransa) ga bauta. Amma, bawan ba zai bauta wa ubangidansa da dukan zuciyarsa ba; ba zai yi amfani da dukan karfinsa ba ko kuma basirarsa don ya bunkasa amfanin ubangidansa. (Kolossiyawa 3:22) Saboda haka, babu shakka Yesu ya lissafa wadannan domin ya nanata cewa kada mu janye kome daga bauta wa Allah. Bauta wa Allah da dukan ranmu yana nufin ba da kanmu, yin amfani da karfinmu cikakke a bautarsa.

20 Shin bauta da dukan ranmu yana nufi ne cewa dole mu ba da yawan lokaci daya daidai da kowa da kuma karfi a hidimarmu? Hakan da kyar zai yiwu, domin yanayi da kuma iyawa sun bambanta daga mutum zuwa mutum. Alal misali, saurayi mai koshin lafiya da kuma karfi zai iya ba da lokaci da yawa wajen wa’azi fiye da wanda tsufa ta ci karfinsa. Wani da ba shi da hakkin iyali zai iya yin fiye da wanda yake da iyalin da zai kula da ita. Idan muna da karfi kuma yanayi ya kyale mu mu yi aiki da yawa a hidima, ya kamata mu yi godiya! Hakika, ba ma son mu kasance da halin sūka, mu rika gwada kanmu da wasu a wannan. (Romawa 14:10-12) Maimakon haka, mu yi amfani da ikonmu mu karfafa wasu.

21. Wacce ce muhimmiyar hanya da za mu yi amfani da ikonmu?

21 Jehovah ya kafa kamiltaccen misali wajen amfani da ikonsa yadda ya dace. Za mu so mu bi misalinsa gwargwadon iyawarmu mu mutane ajizai. Za mu iya yin amfani da ikonmu yadda ya dace ta wajen bi da wasu da daraja wasu da muke da dan iko a kansu. Bugu da kari, muna so mu yi bauta da dukan ranmu wajen yin aikin ceton rai na wa’azi da Jehovah ya ba mu. (Romawa 10:13, 14) Ka tuna, Jehovah yana farin ciki idan ka ba da abu mafi kyau da kai—ranka—zai iya bayarwa. Zuciyarka ba ta motsa ka ba, ka yi dukan abin da za ka iya wajen bautar irin wannan Allah mai fahimi da kuma kauna? Babu wata muhimmiyar hanya fiye da wannan da za mu yi amfani da ikonmu.

^ sakin layi na 10 A zamanin Littafi Mai Tsarki, kalmar Ibrananci na “sanda” tana nufin kere, kamar wanda makiyayi yake amfani da shi wajen tsare tumakinsa. (Zabura 23:4) Hakanan, “sandar” ikon iyaye yana nufin ja-gora cikin kauna, ba horo mai tsanani ba.