Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 11

“Dukan Tafarkunsa Shari’a Ne”

“Dukan Tafarkunsa Shari’a Ne”

1, 2. (a) Wane rashin adalci Yusufu ya fuskanta? (b) Ta yaya Jehovah ya gyara rashin adalcin?

RASHIN adalci ne kwarai. Kyakkyawan saurayi bai aikata laifi ba, amma sai ga shi a kurkuku, ana tuhumarsa da kokarin yin fyade. Amma wannan ba shi ne rashin adalci na farko da ya fuskanta ba. Wasu shekaru kafin wannan, sa’ad da yake dan shekara 17, wannan saurayin, Yusufu, ’yan’uwansa suka ci amanarsa, suka kusa su halaka shi. Suka sayar da shi zuwa bauta a wata kasa. Can, ya ki rinjayar matar ubangidansa. Matar da ta fusata sai ta yi masa kissa, ta yi masa mugun sharri, haka abin ya faru da ya kasance a tsare. Abin bakin ciki, kamar dai babu wanda zai yi roko domin Yusufu.

Yusufu ya fuskanci rashin adalci a ‘kurkuku’

2 Amma, Allah wanda yake “kaunar adalci da shari’a” yana gani. (Zabura 33:5) Jehovah ya gyara rashin adalcin, ya juya abubuwa, kuma a karshe aka ’yantar da Yusufu. Kari ga hakan, Yusufu—mutumin da aka jefa a “kurkuku”—a karshe aka dora shi bisa hakki mai girma kuma na daukaka mai girma sosai. (Farawa 40:15; 41:41-43; Zabura 105:17, 18) A karshe, aka kunita Yusufu, kuma ya yi amfani da matsayinsa mai girma wajen daukaka nufin Allah.—Farawa 45:5-8.

3. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa dukanmu muna son a yi mana adalci?

3 Irin wannan labarin yana sosa mana zuciya, ko ba haka ba? Waye a tsakaninmu bai taba ganin rashin adalci ba ko kuma ba a taba yi masa rashin adalci ba? Hakika, dukanmu muna so a yi mana adalci, babu son rai. Wannan ba abin mamaki ba ne, tun da Jehovah ya ba mu hali irin na mutuntakarsa, kuma shari’a tana cikin halayensa na musamman. (Farawa 1:27) Domin mu san Jehovah da kyau, muna bukatar mu fahimci shari’arsa. Sa’an nan za mu kai ga son hanyoyinsa na ban mamaki sosai kuma ta motsa mu mu matso kusa da shi.

Mecece Shari’a

4. A ra’ayi na ’yan Adam, yaya aka fahimci shari’a sau da yawa?

4 A ra’ayi na ’yan Adam, sau da yawa shari’a ba ta shige amfani da ka’idodin doka ban da son zuciya. Littafin nan Right and Reason—Ethics in Theory and Practice ya ce “shari’a tana da nasaba da doka, wajibi, hakki, da kuma ayyuka, kuma tana yanke shawararta babu son zuciya ko kuma ayyuka da suka cancanta.” Amma, shari’ar Jehovah ta kunshi fiye da yin amfani kawai da abin da doka ta ce domin cewa wajibi ne.

5, 6. (a) Menene ma’anar asalin kalmar da aka fassara ta “shari’a”? (b) Me ake nufi cewa Allah adali ne?

5 Fadi da zurfin shari’ar Jehovah za a fahimce ta sosai idan aka bincika kalmomi na asali da aka yi amfani da su cikin Littafi Mai Tsarki. A cikin Nassosin Ibrananci, an yi amfani da kalmomi uku na musamman. Kalmar ana yawar fassara ta “shari’a” za a iya fassara ta ‘abin da yake daidai.’ (Farawa 18:25) Sauran kalmomi biyun ana fassara su “adalci” ne. A cikin Nassosin Kirista na Helenanci, kalmar da aka fassara ta “adalci” an fassara ta da ma’anar “kasancewa da gaskiya ko kuma daidaita.” Saboda haka, babu bambanci tsakanin adalci da shari’a.—Amos 5:24.

6 Idan Littafi Mai Tsarki ya ce Allah adali ne, yana gaya mana ne cewa yana yin abin da yake daidai ko da ba na tara ba kuma yana yin haka ko da yaushe, ba tare da wariya ba. (Romawa 2:11) Hakika, ya fi gaban fahimi a ce zai aikata abu akasarin haka. Elihu mai adalci ya ce: “Dadai Allah shi yi mugunta! Mai-iko duka shi yi aikin sabo!” (Ayuba 34:10) Hakika, ba zai yiwu ba Jehovah “shi yi aikin sabo.” Me ya sa? Domin dalilai biyu masu muhimmanci.

7, 8. (a) Me ya sa Jehovah ba zai iya rashin adalci ba? (b) Me yake motsa Jehovah ya yi adalci da gaskiya a sha’aninsa?

7 Na farko, yana da tsarki. Kamar yadda muka gani a Babi na 3, Jehovah tsarkinsa babu iyaka kuma adali ne. Saboda haka, ba zai iya yin rashin adalci ko rashin gaskiya ba. Ka yi la’akari da abin da wannan yake nufi. Tsarkakkar Ubanmu na samaniya ya ba mu dalilin tabbaci cewa ba zai taba zaluntar yaransa ba. Yesu ya kasance da wannan tabbacin. A rana ta karshe na rayuwarsa a duniya, ya yi addu’a: “Ya Uba mai-tsarki, ka kiyaye su [almajiran] a cikin sunanka.” (Yohanna 17:11) “Uba mai-tsarki”—a cikin Nassosi lakabi ne ga Jehovah shi kadai. Wannan ya dace, domin babu uba na jiki da za a gwada shi da Allah a tsarki. Yesu yana da cikakken tabbaci cewa almajiran suna kāre a hannun Uban, wanda yake da cikakken tsabta kuma yana da cikakken kebewa daga zunubi.—Matta 23:9.

8 Na biyu, kauna marar son kai muhimmiya ce ga mutuntakar Allah. Irin wannan kauna ta motsa shi ya kasance adali a sha’aninsa da wasu. Amma, rashin adalci iri-iri ne—ya hada da kabilanci, wariya, da kuma son zuciya—sau da yawa hakan na tasowa ne daga hadama da son kai, kishiyar kauna. Game da Allah na kauna, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana: “Ubangiji mai-adalci ne; yana kaunar adalci.” (Zabura 11:7) Jehovah ya ce game da kansa: “Ni, Ubangiji, ina kaunar shari’a.” (Ishaya 61:8) Ba abin karfafa ba ne mu sani cewa Allah yana farin ciki wajen yin abin da yake nagari?—Irmiya 9:24.

Jinkai da Kuma Kamiltacciyar Shari’a ta Jehovah

9-11. (a) Wace dangantaka ce take tsakanin shari’ar Jehovah da kuma jinkansa? (b) Ta yaya shari’ar Jehovah da kuma jinkansa suka bayyana a hanyar da yake bi da mutane masu zunubi?

9 Shari’ar Jehovah, kamar kowanne cikin mutuntakarsa ba ta da ta biyu, kamiltacciya ce, ba ta bukatar gyara. Da yake daukaka Jehovah, Musa ya rubuta: “Fa ne shi, aikinsa cikakke ne; gama dukan tafarkunsa shari’a ne: Shi Allah mai-aminci ne, mara-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 32:3, 4) Kowacce shari’ar Jehovah ba ta da aibi—ba ta da saukin banza kuma ba ta da azaba.

10 Da akwai dangantaka ta kusa tsakanin shari’ar Jehovah da kuma jinkansa. Zabura 116:5 ta ce: “Mai-alheri ne Ubangiji, mai-adalci kuma; I, Allahnmu mai-jinkai ne.” Hakika, Jehovah mai adalci ne kuma mai jinkai. Halaye biyun ba su saba ba. Yin jinkansa ba rage shari’arsa ba ne, kamar a ce shari’arsa idan ba haka ba za ta kasance da tsanani kwarai. Maimakon haka, halaye biyun sau da yawa yana nuna su a lokaci daya, har ma a aukuwa iri daya. Alal misali.

11 Dukan mutane sun gāji zunubi kuma domin haka sun cancanci sakamakon zunubi—watau mutuwa. (Romawa 5:12) Amma Jehovah baya farin ciki a mutuwar masu zunubi. Shi Allah ne “mai-son aikin gafara, . . . mayalwaci da jinkai.” (Nehemiah 9:17) Duk da haka, domin shi mai tsarki ne, ba zai kyale rashin adalci ba. To, ta yaya zai nuna jinkai ga mutane da suka gāji zunubi? An samu amsar a cikin daya daga cikin muhimmiyar gaskiya ta Kalmar Allah: tanadin Jehovah na fansa domin ceton ’yan Adam. A Babi na 14 za mu sami karin bayani game da wannan tsarin kauna. A karo daya, adalci ne kwarai kuma jinkai ne mai girma. Ta wajen su, Jehovah zai nuna jinkai ga masu zunubi da suka tuba yayin nan kuma yana rike da mizanansa na kamiltacciyar shari’a.—Romawa 3:21-26.

Shari’ar Jehovah Tana Dadada Zuciya

12, 13. (a) Me ya sa shari’ar Jehovah take jawo mu gare shi? (b) Yaya Dauda ya kammala game da shari’ar Jehovah, kuma ta yaya wannan zai karfafa mu?

12 Shari’ar Jehovah ba hali ba ce na rashin tausayi da take korarmu, amma hali ne mai kyau da yake jawo mu kusa da shi. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta tausayi na shari’ar Jehovah, ko kuma adalcinsa. Bari mu bincika wasu hanyoyi masu dadada zuciya da Jehovah yake yin shari’arsa.

13 Kamiltacciyar shari’ar Jehovah ce take motsa shi ya yi aminci kuma ya manne wa bayinsa. Mai Zabura Dauda ya fahimci wannan fanni na shari’ar Jehovah da kansa. Daga abin da ya fuskanta da kuma nasa nazarin hanyoyin Allah, yaya Dauda ya kammala? Ya ce: “Ubangiji yana son shari’a, kuma ba ya yarda tsarkakansa ba; yana kiyaye su har abada.” (Zabura 37:28) Wannan tabbaci ne kwarai mai karfafawa! Allahnmu ba zai taba yasar da wanda ya manne masa ba ko na dan lokaci. Saboda haka, za mu iya dogara bisa kusancinsa da kuma kulawarsa mai kyau. Shari’arsa ta ba da tabbacin wannan!—Misalai 2:7, 8.

14. Ta yaya damuwar Jehovah ga matsiyata ya bayyana a cikin Dokar da ya ba wa Isra’ila?

14 Shari’ar Allah tana sane da bukatun wadanda suke wahala. Damuwa da Jehovah yake yi da matsiyata ya bayyana cikin Dokar da ya ba wa Isra’ila. Alal misali, Dokar ta yi tanadi na musamman ta tabbata cewa an kula da marayu da gwauraye. (Kubawar Shari’a 24:17-21) Fahimtar yadda rayuwa za ta kasance da wuya ga irin wadannan iyalan, Jehovah da kansa ya zama ubansu Alkali da kuma Mai Kāre su, wanda yake “aika shari’a domin maraya da gwauruwa.” * (Kubawar Shari’a 10:18; Zabura 68:5) Jehovah ya yi wa Isra’ilawa gargadi cewa idan suka zalunci mata da yara, babu shakka zai saurari kukansu. Ya ce: “Fushina kuma za ya kuna da zafi.” (Fitowa 22:22-24) Ko da yake fushi ba ya cikin hali na musamman na Jehovah, ana sa ya yi fushi na adalci ta wajen ayyuka marasa adalci da gangan, musamman ma idan wadanda ake zalunta marasa karfi ne marasa taimako.—Zabura 103:6.

15, 16. Menene tabbaci mai ban mamaki na rashin son zuciya na Jehovah?

15 Jehovah kuma ya tabbatar mana cewa “ba ya tara, ba ya kuwa karban rashawa ba.” (Kubawar Shari’a 10:17) Ba kamar mutane da yawa ba da suke da iko ko rinjaya, ba a rinjayar Jehovah da dukiya ko kuma siffa. Ba shi da magudi ko son kai. Ka ga tabbaci na ban mamaki na rashin nuna son zuciya na Jehovah. Damar zama masu bauta masa na gaske, da begen rai na har abada, ba a kebe ga masu ilimi kalilan ba kawai. Maimakon haka, “cikin kowacce al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karba ne gareshi.” (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Wannan dama mai ban sha’awa an ba wa kowa ko yaya matsayinsa, ko yaya launin fatarsa, ko yaya kasar da yake zaune cikinta. Wannan ba ita ce shari’a ba mafi kyau?

16 Da akwai wani bangaren shari’ar Jehovah da ya isa mu mai da hankali gare shi kuma mu daraja shi: hanyar da yake bi da wadanda suka taka mizanansa na adalci.

Babu Wanda Za a Kyale Babu Horo

17. Ka yi bayanin abin da ya sa zunubi na wannan duniyar ba zai shafi shari’ar Jehovah ba.

17 Wasu za su yi mamaki: ‘Tun da Jehovah ba ya kyale rashin adalci, yaya za mu yi bayani game da wahala daga rashin adalci da kuma miyagun ayyuka da suka cika duniya a yau?’ Irin wadannan zunubi ba za su shafi shari’ar Jehovah ba. Rashin adalci da yawa a wannan muguwar duniya sakamako ne na zunubin da mutane suka gāda daga Adamu. A duniya da mutane ajizai suka zabi hanyarsu ta zunubi, rashin adalci ya yi yawa—amma ba na dogon lokaci ba.—Kubawar Shari’a 32:5.

18, 19. Menene ya nuna cewa Jehovah ba zai kyale wadanda suke taka dokokinsa na adalci da gangan har abada ba?

18 Yayin da Jehovah yake nuna jinkai ga wadanda suka matso kusa da shi cikin gaskiya, ba zai kyale yanayin da yake bata masa suna ba har abada. (Zabura 74:10, 22, 23) Allah mai shari’a ba za a yi masa ba’a ba; ba zai kāre masu zunubi da gangan daga shari’a mai tsanani ba domin ayyukansu. Jehovah “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinkai da gaskiya; . . . ba shi kubutadda mai-laifi ko kadan.” (Fitowa 34:6, 7) Cikin jituwa da wadannan kalmomin, a wasu lokatai Jehovah ya ga ya zama dole ya hukunta wadanda da gangan suka taka dokokinsa na adalci.

19 Alal misali, ka lura da yadda Allah ya bi da Isra’ila ta dā. Har bayan sun zauna cikin Kasar Alkawari, Isra’ilawa suka rika fadawa cikin rashin aminci. Ko da yake miyagun ayyukansu ya sa Jehovah ya yi ‘fushi,’ ba kawai nan da nan ya yasar da su ba. (Zabura 78:38-41) Maimakon haka, ya yi musu jinkai ya ba su zarafin su canja tafarkunsu. Ya roke su: “Ba ni da wani jin dadi cikin mutuwar mugu ba, gwamma dai shi mugun shi juyo ga barin hanyarsa shi yi rai; ku juyo dai, ku bar miyagun halulukanku; domin me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?” (Ezekiel 33:11) Ganin tamanin rai, Jehovah ya yi ta aika musu da annabawa saboda Isra’ilawan su juyo daga miyagun hanyoyinsu. Amma galibinsu, mutanen masu taurin zuciya suka ki su saurara kuma su tuba. A karshe, domin sunansa mai tsarki da kuma dukan abin da yake nufi, Jehovah ya bayar da su ga hannun abokan gabansu.—Nehemiah 9:26-30.

20. (a) Yadda Jehovah ya bi da Isra’ilawa ya koya mana menene game da shi? (b) Me ya sa zaki alama ce da ta dace na shari’ar Jehovah?

20 Yadda Jehovah ya bi da Isra’ilawa ya koya mana abubuwa da yawa game da shi. Mun koyi cewa Jehovah idanunsa da suke ganin ko’ina suna lura da rashin adalci kuma abin da yake gani suna damunsa. (Misalai 15:3) Kuma ya ba da karfafa mu sani cewa yana neman hanyar da zai yi jinkai idan da dalilin yin haka. Bugu da kari, mun koyi cewa shari’arsa ba a cikin hanzari ba ne. Domin hakurin Jehovah da kuma tsawon jimrewarsa, mutane da yawa suna kammala cikin kuskure cewa ba zai hukunta miyagu ba. Amma wannan ya yi nesa da gaskiya, domin yadda Allah ya bi da Isra’ilawa ya koya mana cewa hakurin Allah yana da iyaka. Jehovah yana rike adalci kwarai. Ba kamar mutane ba, wadanda sau da yawa suna janyewa daga nuna shari’a, bai taba rashin gaba gadi ba domin ya tsaya ga abin da yake nagari. Kamar yadda ya dace, zaki alamar gaba gadi na shari’a yana da mahadi da bayyanar Jehovah da kuma kursiyinsa.  * (Ezekiel 1:10; Ru’ya ta Yohanna 4:7) Domin haka za mu tabbata cewa zai cika alkawarinsa na share rashin adalci daga duniya. Hakika, hanyar shari’arsa za a iya cewa: tsayin daka a dukan inda ya dace, jinkai a dukan inda ya yiwu.—2 Bitrus 3:9.

Matsowa Kusa da Allah Mai Shari’a

21. Sa’ad da muka yi bimbini bisa yadda Jehovah yake yin shari’a, a wace hanya ce ya kamata mu yi tunaninsa, kuma me ya sa?

21 Sa’ad da muka yi bimbini bisa yadda Jehovah ya nuna shari’a, bai kamata ba mu yi tunaninsa kamar marar tausayi, alkali mai zalunci da ya damu da hora marasa laifi kawai. Maimakon haka, ya kamata mu yi tunaninsa kamar Uba ne mai tsayawa tsayin daka wanda koyaushe yana bi da yaransa ta hanya mafi kyau. Tun da shi ne Uba mai adalci, Jehovah yana daidaita tsayawa tsayin dakarsa game da abin da yake nagari da tausayi ga ’ya’yansa na duniya, wadanda suke bukatar taimakonsa da kuma gafara.—Zabura 103:10, 13.

22. Ta ja-gorar shari’arsa, Jehovah ya sa me ya yiwu mana domin mu sami wace dama, kuma me ya sa yake bi da mu ta wannan hanyar?

22 Kai, muna godiya cewa shari’ar Allah ta wuce yanke hukunci bisa masu laifi kawai! Ta wajen ja-gorar shari’arsa, Jehovah ya sa ya yiwu mana mu samu dama mai ban sha’awa—kamiltacciya, rai madawwami a duniya inda “adalci ya ke zaune.” (2 Bitrus 3:13) Allahnmu yana bi da mu ta wannan hanyar domin shari’arsa tana neman ta yi ceto ne maimakon ta halaka. Hakika, fahimtar zurfin shari’ar Jehovah tana jawo mu gare shi! A babi na gaba, za mu bincika yadda Jehovah yake nuna wannan hali mai ban sha’awa.

^ sakin layi na 14 Ko da yake Kalmar Ibrananci ta “maraya” namiji ne kawai, wannan ba ya nufin cewa bai damu da ’ya’ya mata ba. A cikin Dokar Jehovah ya hada da ka’ida da ta ba da tabbacin bai wa ’ya’yan Zelophehad marayu mata gadō. Wannan hukuncin ya kafa ka’ida, saboda haka ya ba wa marayu mata hakkinsu.—Litafin Lissafi 27:1-8.

^ sakin layi na 20 Daidai fa, Jehovah ya kwatanta kansa da zaki wajen yin hukunci bisa Isra’ilawa marasa adalci.—Irmiya 25:38; Hosea 5:14.