Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 12

“Da Rashin Adalci ne Tare da Allah?”

“Da Rashin Adalci ne Tare da Allah?”

1. Ta yaya rashin adalci yake shafanmu?

WATA gwauruwa tsohuwa an damfare ta ajiyar da ta yi a rayuwarta. Uwa marar kauna ta yar da dan jariri. An daure wani mutum a fursuna bisa laifin da bai yi ba. Yaya ka ji game da irin wadannan yanayin? Watakila, kowanne ya ta da maka hankali, kuma da dalilin haka. Mu mutane muna da azanci mai karfi na bambance abin da yake nagari da kuma mugu. Idan aka yi rashin adalci yana damunmu. Muna son a saka wa wanda aka cuta kuma a hukunta macucin. Idan ba a yi haka ba, watakila mu yi tambaya: ‘Allah yana ganin abin da yake faruwa kuwa? Me ya sa bai yi kome ba?’

2. Me Habakkuk ya yi domin rashin adalci, kuma me ya sa Jehovah bai kushe shi ba domin wannan?

2 A cikin dukan tarihi, amintattun bayin Jehovah sun yi irin wadannan tambayoyi. Alal misali, annabi Habakkuk ya yi wa Allah tambaya: “Don me ka ke nuna mini sabo, ka sa ni in duba shiririta kuma? gama barna da mugunta suna gabana; akwai husuma, jayayya kuma ta taso.” (Habakkuk 1:3) Jehovah bai kushe Habakkuk ba domin tambayarsa ta adalci, domin shi ne wanda ya saka shari’a a zuciyar ’yan Adam. Hakika, Jehovah ya albarkace mu da dan azancinsa na shari’a.

Jehovah Yana Kyamar Rashin Adalci

3. Me ya sa za a ce Jehovah yana sane da rashin adalci fiye da mu?

3 Jehovah yana damuwa da rashin adalci. Yana ganin abin da yake faruwa. Game da zamanin Nuhu, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Ubangiji ya ga muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowace shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce dadai kullayaumi.” (Farawa 6:5) Ka yi la’akari da muhimmancin wannan furci. Sau da yawa, fahiminmu na shari’a ya dangana ne bisa wasu aukuwa da muka ji ko kuma wadanda muka fuskanta mu kanmu. Akasin haka, Jehovah yana sane da rashin adalci na dukan duniya. Yana ganin dukansu! Fiye ma da haka, zai iya fahimtar tunanin zuciya—mummunan tunani da yake karkashin rashin adalci.—Irmiya 17:10.

4, 5. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehovah ya damu da wadanda aka yi musu rashin adalci? (b) Ta yaya Jehovah kansa rashin adalci ya taba shi?

4 Amma, Jehovah yana yi fiye da kawai ya lura da rashin adalci. Yana damuwa da wadanda ya shafe su. Sa’ad da al’ummai abokan gāba ke azabtar da mutanensa, Jehovah ya ji zafin “nishinsu a hannun wadanda suka tsananta musu da wulakanci.” (Alkalawa 2:18) Watakila ka lura cewa da zarar wasu mutane suka dinga ganin rashin adalci, hakanan zuciyarsu za ta taurara da shi. Ba haka yake ba da Jehovah! Ya ga rashin adalci a launinsa iri-iri na shekara 6,000, duk da haka bai motsa ba daga kyamarsa. Maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa irin wadannan abubuwa kamar su “harshe mai-karya,” “hannuwa masu-zubda jinin mara-laifi,” “mai-shaidan zur wanda ya ke furtawa da karya” ransa yana kyamarsu.—Misalai 6:16-19.

5 Ka yi la’akari kuma da yadda Jehovah ya kushe kwarai shugabannin Isra’ila marasa adalci. “Ba naku ba ne ku san shari’a?” ya hure annabinsa ya tambaye su. Bayan ya kwatanta yadda suka yi barna da ikonsu cikin kalmomi na musamman, Jehovah ya fadi sakamakon ga wadannan mutane malalata: “Za su tada murya ga Ubangiji, amma ba za ya amsa musu ba; i, za ya boye musu fuskatasa a loton nan, daidai yadda suka yi zunubi cikin aikinsu.” (Mikah 3:1-4) Jehovah yana kyamar rashin adalci kwarai! Hakika, shi kansa ma ya fuskanci rashin adalci! Shekaru aru-aru, Shaidan yana ta zolayarsa cikin rashin adalci. (Misalai 27:11) Bugu da kari, mugun aikin rashin adalci ya taba Jehovah sa’ad da Dansa, wanda “ba ya yi zunubi ba,” aka kashe shi kamar mai laifi. (1 Bitrus 2:22; Ishaya 53:9) A bayyane yake, Jehovah ya damu da wahalar wadanda suke wahala daga rashin adalci.

6. Me muke yi sa’ad da muka fuskanci rashin adalci, kuma me ya sa?

6 Shi ya sa, sa’ad da muka lura da rashin adalci—ko mu kanmu aka yi mana rashin adalci—sai ya kasance kamar mu yi kuka. An halicce mu a kamanin Allah, kuma rashin adalcin akasin dukan abin da matsayin Jehovah yake nufi ne. (Farawa 1:27) To, me ya sa Allah ya kyale rashin Adalci?

Batun Ikon Mallaka na Allah

7. Ka kwatanta yadda aka kalubalanci ikon mallaka na Jehovah.

7 Amsar tambayar ta dangana a kan batun ikon mallaka. Kamar yadda muka gani, Mahalicci yana da hakkin ya yi sarauta bisa duniya da dukan abin da suke cikinta. (Zabura 24:1; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Amma da farko cikin tarihin ’yan Adam, an kalubalanci ikon mallaka na Jehovah. Ta yaya wannan ya faru? Jehovah ya dokaci mutum na farko, Adamu, kada ya ci daga wani itace a lambun da gidansa ne, Aljanna. Kuma idan ya yi rashin biyayya fa? “Mutuwa za ka yi lallai,” Allah ya gaya masa. (Farawa 2:17) Dokar Allah ba wahala ba ce ga Adamu ko kuma matarsa, Hauwa’u. Duk da haka, Shaidan ya rudi Hauwa’u cewa Allah yana hana su sukuni ne kawai. Me zai faru idan ta ci daga itacen? Shaidan ya gaya wa Hauwa’u kai tsaye: “Ba lallai za ku mutu ba: gama Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su bude, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; Farawa 3:1-5.

8. (a) Menene manufar furcin Shaidan ga Hauwa’u? (b) Menene Shaidan ya kalubalanta game da ikon mallaka na Allah?

8 Wannan furcin Shaidan yana nufin ba kawai cewa Jehovah ya hana Hauwa’u sani da ya wajaba ba ne amma cewa Ya yi mata karya. Shaidan ya mai da hankali don kada ya tuhumi gaskiyar cewa Allah ne mamallakin dukan halitta. Amma ya kalubalanci dacewarsa, cancantarsa, da kuma adalcinsa. Watau, yana nufi ne cewa Jehovah bai yi amfani da Ikonsa na mallaka da adalci ba domin ya amfani talakawansa.

9. (a) Ga Adamu da Hauwa’u, menene sakamakon rashin biyayyarsu, kuma wadanne tambayoyi ne masu muhimmanci suka taso? (b) Me ya sa Jehovah bai halaka ’yan tawayen nan a take ba?

9 Daga baya, Adamu da Hauwa’u suka yi wa Jehovah rashin biyayya ta wajen cin itace da aka haramta musu. Domin rashin biyayyarsu horonsu mutuwa ne, kamar yadda Allah ya fada. Karyar Shaidan ta jawo tambayoyi. Shin da gaske ne cewa Jehovah yana da hakkin ya yi sarauta bisa ’yan Adam, ko dai ya kamata mutum ya mallaki kansa? Shin Jehovah yana amfani da ikon mallakarsa ta hanya mafi kyau kuwa? Da Jehovah zai yi amfani da ikonsa mai girma ya halaka ’yan tawayen nan da nan. Amma tambayoyi da suka taso, game da sarautar Allah ne, ba ikonsa ba. Saboda haka, kashe Adamu, Hauwa’u da kuma Shaidan ba zai tabbatar da adalcin mulkin Allah ba. Akasin haka, sai dai ya kara sa a tuhumi sarautarsa. Hanyar da kawai za ta tabbata ko ’yan Adam za su iya nasara wajen mallakar kansu, da ’yanci daga Allah, ita ce a ba su lokaci.

10. Menene tarihi ya nuna game da sarautar ’yan Adam?

10 Menene ya bayyana da shigewar lokaci? A duk cikin karnuka, mutane sun gwada ire-iren gwamnatoci da yawa, hade da sarautar mutum daya, dimokuradiyya, rugurguzu, da kuma kwaminis. An takaita dukansu cikin furci na gaskiya na Littafi Mai Tsarki: “Mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya cuce shi.” (Mai-Wa’azi 8:9) Da kyakkyawar dalili, annabi Irmiya ya ce: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.”—Irmiya 10:23.

11. Me ya sa Jehovah ya kyale ’yan Adam su sha wahala?

11 Jehovah ya sani tun da farko cewa ’yancin ’yan Adam, ko kuma mallakar kansu, zai kawo wahala kwarai. Amma rashin adalci ne a gare shi ya kyale wannan yanayi ya cika? A’a! Alal misali: A ce kana da yaro wanda yake bukatar fida domin a yi maganin cuta da take so ta kasance ajalinsa. Ka lura cewa wannan fidar za ta dan wahalar da yaron, kuma wannan ya dame ka kwarai. Amma kuma, ka sani cewa wannan za ta sa yaron ya more rayuwa mafi kyau a nan gaba. Hakazalika, Allah ya sani—har ma ya annabta—cewa kyale sarautar ’yan Adam zai kawo dan azaba da kuma wahala. (Farawa 3:16-19) Amma ya sani kuma cewa sauki mai ma’ana kuma na dindindin zai yiwu ne kawai idan ya kyale ’yan Adam suka ga mugun sakamakon tawaye. A wannan hanyar ce kawai za a iya sulhunta wannan batun dindindin, har abada.

Batun Amincin Mutum

12. Kamar yadda aka nuna a batun Ayuba, wace tuhuma ce Shaidan ya yi wa ’yan Adam?

12 Da akwai kuma wani bangare na wannan batun. Wajen kalubalantar dacewar sarautar Allah da kuma adalcinsa, ba kawai Shaidan ya yi karya game da Jehovah da kuma ikon mallakarsa ba; amma kuma ya yi karya game da bayin Allah da amincinsu. Alal misali, ka lura da abin da Shaidan ya gaya wa Jehovah game da mutum mai aminci Ayuba: “Ba ka kewaye shi da shimge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da yake da shi, a kowane sassa? Ka albarkaci aikin hannuwansa, dabbobinsa sun karu a kasa. Mika hannunka kadai yanzu, ka taba dukan abin da yake da shi, za ya la’anta ka a fuskarka!”—Ayuba 1:10, 11.

13. Menene Shaidan yake nufi a tuhumarsa game da Ayuba, kuma ta yaya wannan ya shafi dukan ’yan Adam?

13 Shaidan ya ce wai Jehovah yana amfani ne da Ikonsa na kāriya ya yi wa Ayuba toshiya. Watau, wannan yana nufi ne cewa amincin Ayuba riya ce kawai, wai yana bauta wa Allah ne kawai domin abin da zai samu. Shaidan ya ce idan aka hana Ayuba albarkar Allah, wannan mutumin zai sabi Mahaliccinsa. Shaidan ya san cewa Ayuba shahararre ne wajen kasancewa “kamili . . . , mutum mai-adalci, mai-tsoron Allah, yana kin mugunta.” * Saboda haka, idan Shaidan zai iya sa Ayuba ya yi rashin aminci, menene wannan zai nufa ga sauran ’yan Adam? Saboda haka Shaidan yana kalubalantar amincin dukan wadanda suke so su bauta wa Allah ne. Hakika, in aka fadada batun, Shaidan ya ce wa Jehovah: “Dukan abin da mutum [ba Ayuba ba kawai] ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; Ayuba 1:8; 2:4.

14. Menene tarihi ya nuna game da zargin ’yan Adam da Shaidan ya yi?

14 Tarihi ya nuna cewa mutane da yawa, kamar Ayuba, sun kasance da aminci ga Allah sa’ad da suke fuskantar jarraba—akasin da’awar Shaidan. Sun faranta wa Jehovah rai ta wajen tafarkinsu na aminci, kuma wannan ya ba wa Jehovah amsa ga zolaya cikin fahariya na Shaidan cewa ’yan Adam za su daina bauta wa Allah idan aka azabtar da su. (Ibraniyawa 11:4-38) Hakika, masu zuciyar kirki suna ki su juya wa Allah baya. Har lokacin da suka rikice domin yanayi mai wuya, suna dogara ga Jehovah ya ba su karfi da za su jimre.—2 Korinthiyawa 4:7-10.

15. Wace tambaya za a yi game da hukuncin Allah na dā da kuma mai zuwa a nan gaba?

15 Amma nuna shari’a na Jehovah ya kunshi fiye da batutuwan mulkin mallaka da amincin mutum. Littafi Mai Tsarki ya ba mu tarihin hukuncin Jehovah bisa mutane dai-dai da har ma da dukan al’umma. Kuma ya kunshi annabce-annabce na hukuncin da zai yi a nan gaba. Me ya sa za mu tabbata cewa Jehovah yana yi kuma zai yi adalci a hukuncinsa?

Dalilin da Ya Sa Shari’ar Allah ta Fi Girma

Jehovah ba zai taba “halaka mai-adalci tare da miyagu” ba

16, 17. Wadanne misalai ne suka nuna cewa mutane suna da iyaka wajen fahimi idan ya zo ga shari’a ta gaskiya?

16 Game da Jehovah, da gaske za a iya cewa: “Dukan tafarkunsa shari’a ne.” (Kubawar Shari’a 32:4) Babu wani cikinmu da zai iya yin wannan da’awar game da kansa, domin sau da yawa fahiminmu mai iyaka zai iya duhunta fahimtar abin da yake nagari. Alal misali, ka yi la’akari da Ibrahim. Ya roki Jehovah game da halaka Saduma—duk da mugunta da take ko’ina a can. Ya tambayi Jehovah: “Za ka halaka mai-adalci tare da miyagu?” (Farawa 18:23-33) Hakika, a’a. Sai dai Lot mai aminci da ’ya’yansa mata suka sauka lafiya a birnin Zoar kafin Jehovah ya “zubarda kibiritu da wuta” bisa Saduma. (Farawa 19:22-24) Akasin haka, Yunana ya cika da “fushi” sa’ad da Allah ya yi wa mutanen Nineveh jinkai. Tun da Yunana ya riga ya sanar da halakarsu, da zai yi farin ciki ya ga an shafe su—ko yaya tubar zuciyarsu.—Yunana 3:10–4:1.

17 Jehovah ya tabbatar wa Ibrahim cewa nuna shari’arsa ya kunshi ceton masu adalci ba halaka miyagu kawai ba. A wani bangare kuma, Yunana dole ya koyi cewa Jehovah yana da jinkai. Idan miyagu suka sake tafarkinsu, yana “hanzarin gafartawa.” (Zabura 86:5) Ba kamar mutane ba wadanda suke cike da tsoro, Jehovah ba ya yin hukunci mai tsanani kawai domin ya nuna ikonsa, ko kuma ya ki tausayawa domin yana tsoron za a ce da shi raunane. Hanyarsa ta nuna jinkai ne a dukan wurin da akwai dalilin yinsa.—Ishaya 55:7; Ezekiel 18:23.

18. Ka nuna daga cikin Littafi Mai Tsarki cewa Jehovah ba ya aikata abu bisa motsin zuciya.

18 Duk da haka, motsin zuciya ba ta rufe wa Jehovah idanu. Sa’ad da mutanensa suka bunkasa cikin bautar gumaka, Jehovah ya ce: “Zan yi miki shari’a bisa ga al’amuranki; zan kuma jawo miki alhakin dukan kazantarki. Idona ba za ya kebe ki ba, ba kuwa zan ji tausayi ba: amma zan jawo miki alhakin al’amuranki.” (Ezekiel 7:3, 4) Idan mutane suka taurara cikin ayyukansu, Jehovah yana hukunci hakanan. Amma hukuncinsa bisa karfafar tabbaci ne. Saboda haka, sa’ad da ‘kara mai yawa’ ta fada kunnuwansa game da Saduma da Gwamrata, Jehovah ya ce: “Ni sauka yanzu, in gani ko aikinsu ya kai gwargwadona kararsa, wadda ta zo gareni.” (Farawa 18:20, 21) Muna godiya kwarai da yake Jehovah ba kamar mutane ba ne wadanda suke hukunci cikin gaggawa kafin ma su ji gaskiyar! Hakika, Jehovah yana nan kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shi: “Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi.”—Kubawar Shari’a 32:4.

Ka Dogara Bisa Shari’ar Jehovah

19. Menene za mu yi sa’ad da muke da tambaya domin rikicewa game da yadda Jehovah ya nuna shari’a?

19 Littafi Mai Tsarki bai amsa kowacce tambaya ba game da ayyukan Jehovah a dā; kuma bai ba da bayani dalla-dalla ba game da yadda Jehovah zai yi hukunci game da mutane da kuma rukuninsu a nan gaba. Sa’ad da muka rikice domin tarihi ko kuma annabci na Littafi Mai Tsarki domin babu karin bayani, za mu nuna irin aminci da annabi Mikah ya nuna, wanda ya rubuta: “Zan jira Allah na cetona.”—Mikah 7:7.

20, 21. Me ya sa za mu tabbata cewa Jehovah zai yi abin da yake nagari ko da yaushe?

20 Za mu tabbata cewa a kowane yanayi, Jehovah zai yi abin da yake daidai. Ko lokacin da kamar mutane sun kyale rashin adalci, Jehovah ya yi alkawari: “Daukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako.” (Romawa 12:19) Idan muka nuna halin hakuri, za mu maimaita tabbaci da manzo Bulus ya furta: “Da rashin adalci tare da Allah? Dadai!”—Romawa 9:14.

21 A yanzu dai, muna rayuwa ne a “miyagun zamanu.” (2 Timothawus 3:1) Rashin adalci da “zilama” ya kai ga zalunci iri-iri. (Mai-Wa’azi 4:1) Duk da haka, Jehovah bai canja ba. Har yanzu yana kyamar rashin aminci, kuma yana damuwa kwarai da wadanda aka yi musu rashin aminci. Idan muka manne wa Jehovah da ikon mallakarsa, zai ba mu karfin da za mu jimre har zuwa lokacin da ya ka’ide zai gyara dukan rashin aminci a karkashin Mulkinsa.—1 Bitrus 5:6, 7.

^ sakin layi na 13 Jehovah ya ce game da Ayuba: “Babu mai-kama da shi cikin duniya.” (Ayuba 1:8) Watakila, Ayuba ya rayu ne bayan mutuwar Yusufu kuma kafin Musa ya zama nadadden shugaban Isra’ila. Saboda haka, a wannan lokacin za a iya cewa daidai babu wanda yake da aminci kamar na Ayuba.