Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 13

‘Dokar Jehovah Cikakkiya Ce’

‘Dokar Jehovah Cikakkiya Ce’

1, 2. Me ya sa mutane ba su dauki doka kome ba, duk da haka yaya za mu ji game da dokar Allah?

“DOKA rami ne marar iyaka, tana . . . hadiye ko menene.” Wannan furcin ya bayyana a wani littafi da aka wallafa a shekara ta 1712. Mawallafinsa ya nuna rashin yardarsa ne game da tsarin doka wanda kara a kotu wani lokaci za ta rika ja har na wasu shekaru, ta talautar da wadanda suke nema a yi musu adalci. A kasashe da yawa, tsarin kafa doka da yin hukunci sun kasance da wuya, kuma sun cika da rashin adalci, son zuciya, da kuma rashin jituwa, saboda haka kyamar dokar ta yi yawa.

2 Akasarin haka ka yi la’akari da kalmomin da aka rubuta shekaru 2,700 da suka shige: ‘Ina kaunar dokarka ba misali!’ (Zabura 119:97) Me ya sa mai Zabura yake da irin wannan kaunar sosai? Domin doka da ya yaba wa ba ta kasance daga wata gwamnati ba, amma daga Jehovah Allah ne. Yayin da ka yi nazarin dokar Jehovah, za ka ji kamar yadda mai Zabura ya ji. Irin wannan nazarin zai ba ka fahimi cikin tunani mafi muhimmanci na hanyar hukunci a dukan sararin samaniya.

Mai Ba da Doka Mafi Girma

3, 4. A wadanne hanyoyi ne Jehovah ya kasance Mai Ba da Doka?

3 ‘Daya ne kadai mai-bada doka, mai-yin shari’a,’ Littafi Mai Tsarki ya gaya mana. (Yakub 4:12) Hakika, Jehovah ne kadai Mai Ba da Doka ta gaske. Har tafiyar ababan sammai ma “dokokin sammai” suke musu ja-gora. (Ayuba 38:33, The New Jerusalem Bible) Tsarkakkan mala’ikun Jehovah masu yawa ma dokar Allah ce take yi musu ja-gora, domin an tsara su matsayi matsayi kuma suna bauta ne masu hidima bisa umurnan Jehovah.—Zabura 104:4; Ibraniyawa 1:7, 14.

4 Jehovah ya ba da dokoki ga ’yan Adam ma. Kowanne cikinmu yana da lamiri, nuni ne na shari’ar Jehovah. Doka ce ta ciki, lamirin zai iya taimakonmu bambance tsakanin abin da ke nagari da kuma mugu. (Romawa 2:14) Iyayenmu na farko an albarkace su da kamiltaccen lamiri, saboda haka ba sa bukatar dokoki da yawa. (Farawa 2:15-17) Amma, mutum ajizi yana bukatar dokoki su yi masa ja-gora wajen yin nufin Allah. Iyaye kamar su Nuhu, Ibrahim, da kuma Yakubu sun karbi dokoki daga Jehovah Allah kuma sun koyar ga iyalansu. (Farawa 6:22; 9:3-6; 18:19; 26:4, 5) Jehovah ya sa kansa ya kasance Mai Ba da Doka a hanyar da ba ta biyunta lokacin da ya ba wa al’ummar Isra’ila Doka ta hannun Musa. Wannan tsarin doka ya ba mu fahimi kwarai bisa shari’ar Jehovah.

Dokar Musa—Takaitacciya

5. Shin tsarin dokoki na Dokar Musa tsari ne kawai na dokoki masu yawa kuma masu wuya, me ya sa ka fadi haka?

5 Mutane da yawa suna tsammanin cewa Dokar Musa tsarin dokoki ne masu yawa, masu wuya. Irin wannan ra’ayin ya yi nesa da gaskiya. Tsarin dokokin ya kunshi fiye da dokoki 600. Kamar dai suna da yawa, amma ka yi tunani: A karshen karni na 20, dokokin kasa na Amirka sun cika shafuffuka 150,000 na littattafan dokoki. Bayan kowacce shekara biyu ana dada dokoki 600! Idan muka yi maganar yawa kawai, yawan dokokin mutane ya wadantar da Dokar Musa. Duk da haka, Dokar Allah ta yi wa Isra’ilawa ja-gora a bangarorin rayuwa da dokokin zamani ba su ma fara tabawa ba tukuna. Ga shi a takaice.

6, 7. (a) Menene ya bambanta Dokar Musa daga kowane irin tsarin doka, kuma wacce ce babba cikin Dokar? (b) Ta yaya Isra’ilawan za su nuna yardarsu ga ikon mallaka na Jehovah?

6 Dokar ta daukaka ikon mallaka na Jehovah. Saboda haka, Dokar Musa ta fi gaban a gwada ta da kowane tsarin dokoki. Babba cikin dokokin ita ce wannan: “Ka ji fa, ya Isra’ila: Ubangiji Allahnmu Ubangiji daya ne: kuma za ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan karfinka.” Yaya mutanen Allah za su nuna kauna gare shi? Za su bauta masa, su kuma mika kai ga ikonsa na mallaka.—Kubawar Shari’a 6:4, 5; 11:13.

7 Kowanne Ba’isra’ile zai nuna yardarsa ga ikon mallaka na Jehovah ta wajen sadaukar da kai ga wadanda ya ba su iko bisa kansa. Iyaye, hakimai, alkalai, firistoci, da kuma a karshe sarki dukan wadannan suna wakiltan ikon Allah ne. Jehovah yana daukar kowane tawaye ga wadannan tawaye ne gare shi. A wani bangare kuma, wadanda aka ba su iko za su fuskanci fushin Jehovah idan suka bi da mutanensa cikin rashin adalci da kuma mugunta. (Fitowa 20:12; 22:28; Kubawar Shari’a 1:16, 17; 17:8-20; 19:16, 17) Saboda haka, da masu iko da wadanda ake mallaka suna da hakkin daukaka ikon mallaka na Allah.

8. Ta yaya Dokar ta daukaka mizanin Jehovah na tsarki?

8 Dokar ta daukaka mizanin Jehovah na tsarki. Kalmar nan “tsarki” da kuma “tsarkaka” sun bayyana fiye da sau 280 a cikin Dokar Musa. Dokar ta taimaki mutanen Allah su bambance tsakanin abin da yake da tsarki da abin da ba shi da tsarki, ya fadi abubuwa dabam dabam kusan 70 da za su iya sa Ba’isra’ile ya zama marar tsarki a jiki. Wadannan dokokin sun yi maganar tsabta ta jiki, abinci, har da kawar da najasa. Irin wadannan dokokin sun kawo amfani na ban mamaki ga lafiyar jiki. * Amma suna da ma’ana mai zurfi—domin mutanen su ci gaba da kasancewa da tagomashin Jehovah, a ware daga ayyukan zunubi na mugayen al’ummai da suka kewaye da su. Ga misali.

9, 10. Dokar alkawari ta hada da wadanne dokoki ne game da jima’i da kuma haihuwa, kuma wadanne amfani wadannan dokoki suka bayar?

9 Tsarin Dokar alkawari ya ce jima’i da kuma haihuwa—har a tsakanin ma’aurata—suna kawo rashin tsarkaka na dan lokaci. (Leviticus 12:2-4; 15:16-18) Irin wadannan dokoki ba su kushe wa wannan kyautar ba mai tsabta daga Allah. (Farawa 1:28; 2:18-25) Maimakon haka, wadannan dokokin suna daukaka tsarkakar Jehovah, suna kāre bayinsa daga gurbacewa. Abin lura ne cewa al’ummai da suka kewaye Isra’ila suna hada bauta da jima’i, bukukuwan ni’ima. Addinin Kan’aniyawa ya hada da karuwai maza da mata. Aka samo ayyukan rashin kunya mafi muni kuma suka yadu. Akasin haka, Dokar ta ware bautar Jehovah gabaki daya daga ayyukan jima’i. * Da wasu amfani har ila.

10 Wadannan dokokin suna koyar da gaskiya mai muhimmanci. * Kuma ta yaya ake gādar zunubin Adamu daga tsara zuwa tsara? Ba ta wajen jima’i ne da kuma haihuwa ba? (Romawa 5:12) Hakika, Dokar Allah tana tunasar da mutanensa kasancewa ta kullum na zunubi. Dukanmu babu shakka, an haife mu cikin zunubi. (Zabura 51:5) Muna bukatar gafara da kuma ceto domin mu matso kusa da Allahnmu mai tsarki.

11, 12. (a) Dokar ta daukaka wane mizani ne mai muhimmanci na shari’a? (b) Wace kāriya ce game da rashin adalci take kunshe cikin Dokar?

11 Dokar ta daukaka kamiltacciyar shari’a ta Jehovah. Dokar ta daukaka mizanin daidaitawa, a batun shari’a. Saboda haka, Dokar ta ce: “Rai maimakon rai ne, ido maimakon ido, hakori maimakon hakori, hannu maimakon hannu, kafa maimakon kafa.” (Kubawar Shari’a 19:21) A batun laifi, horon zai yi daidai da laifin da aka yi. Wannan bangare na shari’ar Allah ya rinjayi Dokar kuma har zuwa yau tana da muhimmanci wajen fahimtar hadayar fansa na Yesu Kristi, kamar yadda Babi na 14 zai nuna.—1 Timothawus 2:5, 6.

12 Dokar kuma ta hada da kāriya game da yin rashin adalci. Alal misali, ana bukatar akalla shaidu biyu domin a tabbatar da gaskiyar tuhuma. Sakamakon shaidan zur yana da tsanani. (Kubawar Shari’a 19:15, 18, 19) An haramta cin hanci da rashawa. (Fitowa 23:8; Kubawar Shari’a 27:25) Har a huldarsu ta kasuwanci, mutanen Allah dole su daukaka mizanai masu girma na shari’a ta Jehovah. (Leviticus 19:35, 36; Kubawar Shari’a 23:19, 20) Wancan tsarin dokoki mai kyau kuma marar son zuciya babbar albarka ce ga Isra’ila!

Doka da ta Nanata Jinkai da Nuna Rashin Son Zuciya Wajen Hukunci

13, 14. Ta yaya Dokar ta daukaka hukuncin adalci ga barawo da kuma wanda aka yi wa sata?

13 Shin Dokar Musa tarin dokoki ne kawai, kagagge, marar jinkai? A’a! An hure Sarki Dauda ya rubuta: ‘Dokar Jehovah cikakkiya ce.’ (Zabura 19:7) Kamar yadda ya sani kwarai, Dokar ta daukaka jinkai da kuma rashin son zuciya. Ta yaya ta yi haka?

14 A wasu kasashe a yau, dokar kasar kamar dai tana nuna laushin hali da kuma tagomashi ga mai laifi fiye da yadda take yi ga wadanda aka cuta. Alal misali, barayi za a kai su kurkuku. Har ila, wadanda aka yi musu sata ba su samu kayansu ba kuma dole su biya haraji kuma a yi amfani da shi wajen ciyar da barayin kuma a ba su wajen kwana. A Isra’ila ta dā, babu kurkuku kamar wadanda muka san su a yau. Da akwai iyaka game da tsananin horo. (Kubawar Shari’a 25:1-3) Barawo dole ya biya wanda ya yi wa sata abin da ya sace. Kari ga haka, barawon dole ya biya diyya. Nawa? Ya bambanta. Hakika, an bai wa alkalai damar su dubi wasu ka’idodi, kamar su tuba ta mai zunubin. Wannan zai bayyana dalilin da ya sa diyya da ake bukata daga barawon in ji Leviticus 6:1-7 bai kai ko kusan abin da aka ka’ide ba a Fitowa 22:7.

15. Ta yaya Dokar ta tabbatar da jinkai da kuma shari’a a batun wanda ya kashe mutum cikin tsausayi?

15 Dokar ta yi la’akari da cewa ba dukan laifi ba ake yi da gangan. Alal misali, idan mutum ya kashe wani cikin tsausayi, ba dole ba ne ya bayar da rai ga rai idan ya yi abin da ke daidai ta wajen gudu zuwa biranen mafaka da aka baza a cikin dukan Isra’ila. Bayan kwararrun alkalai sun bincika batunsa, dole ne ya zauna a birnin mafaka, har sai mutuwar babban firist. Sannan zai sami ’yancin zama a dukan inda ya zaba. Ta haka ya amfana daga jinkai na Allah. A haka, wannan dokar ta nanata muhimmancin ran mutum.—Litafin Lissafi 15:30, 31; 35:12-25.

16. Ta yaya Dokar ta kāre wasu hakkoki na mutum?

16 Dokar ta kāre hakkin mutum. Ka yi la’akari da hanyoyin da ta kāre wadanda ake bi bashi. Dokar ta hana shiga cikin gidan wanda ya ci bashi a kwace kayansa a maimakon bashin. Maimakon haka, wanda aka ci bashinsa zai tsaya a waje wanda ya ci bashin ya fito masa da kayan jingina. Saboda haka, gidan mutumin ba wurin shiga a yi kwace ba ne. Idan mai ba da bashi ya karbi rigar wanda ya ci bashi jingina, dole ya mayar masa da maraice, domin wanda ya ci bashin watakila zai bukaci mayafinsa cikin dare.—Kubawar Shari’a 24:10-14.

17, 18. A al’amura na yaki, ta yaya Isra’ilawa suka bambanta da wasu al’ummai, kuma me ya sa?

17 Har yaki ma yana da ka’idodi a cikin Dokar. Mutanen Allah za su yi yaki ba domin su cika burin samun iko ko kuma su ci kasashe ba ne, amma su kasance wakilan Allah a ‘yakokin Jehovah.’ (Litafin Lissafi 21:14) A yanayi da yawa, Isra’ilawan suna ba da gari da farko. Idan birnin ya ki, sai Isra’ilawan su kai masa hari—amma bisa umurnan Allah. Ba kamar sojoji ba a cikin dukan tarihi, sojojin Isra’ila ba a yarda musu su yi wa mata fyade ba ko kuma su yi kisa ba ji ba gani. An dokace su ma su daraja mahallin, kada su tuge itatuwan abokan gāba. * Wasu sojoji ba su da irin wannan hanin.—Kubawar Shari’a 20:10-15, 19, 20; 21:10-13.

18 Kana bakin ciki idan ka ji cewa a wasu kasashe ana horar yara su zama sojoji? A Isra’ila ta dā, babu mutumin da ya gaza shekara 20 da zai shiga soja. (Litafin Lissafi 1:2, 3) Har wanda ya kai namiji ana kyale shi idan matsoraci ne. Ana kyale ango na shekara guda domin watakila a haifa masa magajinsa kafin ya je irin wannan hidima mai hadari. A wannan hanyar, Dokar ta yi bayani, wanda ya yi sabon aure ya ‘faranta’ wa amaryarsa rai.—Kubawar Shari’a 20:5, 6, 8; 24:5.

19. Wane tanadi ne Dokar ta kunsa domin kāre mata, yara, iyalai, gwauraye, da kuma marayu?

19 Dokar kuma ta kāre mata, yara, da kuma iyalai, ta wajen yi musu tanadi. Ta umurci iyaye su mai da hankali ga yaransu kuma su koyar da su a abubuwa na ruhaniya. (Kubawar Shari’a 6:6, 7) Ta haramta dukan ire-iren jima’i tsakanin dangi da dangi, kuma sakamakon haka mutuwa ne. (Leviticus, sura 18) Hakanan kuma ta haramta zina, da sau da yawa take raba iyalai kuma take halaka kwanciyar ransu da kuma darajarsu. Dokar ta yi tanadi wa gwauraye da kuma marayu, kuma cikin kakkarfan harshe ta haramta wulakanta su.—Fitowa 20:14; 22:22-24.

20, 21. (a) Me ya sa Dokar Musa ta kyale aurar mata fiye da daya tsakanin Isra’ilawa? (b) Game da batun kashe aure, me ya sa Dokar ta bambanta daga ka’idar da Yesu daga baya ya maido?

20 Amma a nan, wasu za su yi mamaki, ‘Me ya sa Dokar ta kyale auren mata fiye da daya?’ (Kubawar Shari’a 21:15-17) Muna bukatar yin la’akari da dokokin daidai da zamansu lokacin. Wadanda suka kwatanta Dokar Musa bisa lokatai na zamani da kuma al’adu babu shakka ba za su fahimce ta ba. (Misalai 18:13) Ka’idar Jehovah, da ya kafa a Adnin, ta sa aure ya kasance gami ne na dindindin tsakanin namiji da tamace. (Farawa 2:18, 20-24) A lokacin da Jehovah ya bai wa Isra’ila Dokar, ayyuka kamar su aurar mata fiye da daya ya riga ya kahu da dadewa. Jehovah ya san cewa ‘mutanensa masu taurin kai’ za su ki biyayya da har umurnai da suka kasance dole ma, kamar wadanda ke haramta bauta wa gunki. (Fitowa 32:9) Cikin hikima, bai zabi wannan zamanin domin ya sake dukan sha’anonin aurensu ba. Ka tuna cewa, Jehovah bai kafa auren fiye da mace guda ba. Amma, ya yi amfani da Dokar Musa ya kafa ka’ida game da aurar mata fiye da daya tsakanin mutanensa kuma don ya hana su bata ka’idar.

21 Hakazalika, Dokar Musa ta kyale mutum ya saki matarsa domin abubuwa da yawa masu tsanani. (Kubawar Shari’a 24:1-4) Yesu ya kira ta dama da Allah ya bai wa Yahudawa, “domin taurin zuciyar[su].” Amma dai, irin wannan damar ba ta dindindin ba ce. Ga mabiyansa, Yesu ya maido da ka’idar aure ta asali.—Matta 19:8.

Dokar ta Daukaka Kauna

22. A wadanne hanyoyi ne Dokar Musa ta karfafa kauna, ga wa?

22 Za ka iya tunanin tsarin dokoki na zamani da ya karfafa cewa a yi kauna? Dokar Musa ta daukaka kauna fiye da kome. Hakika, a cikin littafin Kubawar Shari’a kawai, kalmar nan “kauna” ta bayyana a yanayi dabam dabam wajen fiye da sau 20. “Ka yi kaunar makwabcinka kamar ranka,” ita ce doka mafi girma ta biyu a Dokar. (Leviticus 19:18; Matta 22:37-40) Mutanen Allah za su yi kaunar ba junansu kawai ba amma har da baki da suke da zama a tsakaninsu, suna tuna cewa su ma sun taba zaman bakunci. Za su yi kaunar gajiyayyu da wahalallu, za su taimake su da abin da suke da shi kuma za su guji ci wa wadanda suka galabaita zarafi. An umurce su su bi da jaki da kirki da kuma sanin ya-kamata.—Fitowa 23:6; Leviticus 19:14, 33, 34; Kubawar Shari’a 22:4, 10; 24:17, 18.

23. Menene marubucin Zabura ta 119 ya motsa ya yi, kuma menene za mu daura aniyyar yi?

23 Wace al’umma ce ban da wannan da aka yi wa albarka take da irin wannan tsarin doka? Ba mamaki da mai Zabura ya rubuta: ‘Ina kaunar dokarka ba misali!’ Babu shakka, kaunarsa ba motsin zuciya ba ne kawai. Ta motsa shi ga yin aiki, domin ya yi kokari ya yi biyayya ga dokar kuma ya rayu bisanta. Ya ci gaba da cewa: “[Dokarka] abin tunawa ne a gareni dukan yini.” (Zabura 119:11, 97) Hakika, yana ba da lokaci ya yi nazarin dokokin Jehovah a kai a kai. Babu shakka cewa da ya yi haka, kaunarsa ga dokokin ta karu. Hakanan, kaunarsa ga Mai Ba da Dokar, Jehovah Allah ma ta karu. Yayin da ka ci gaba da nazarin dokar Allah, bari kai ma ka matso kusa da Jehovah, Mai Ba da Doka Mai Girma kuma Allah na shari’a.

^ sakin layi na 8 Alal misali, da dadewa kafin wasu su kai ga fahimin, doka ta bukaci a rufe kashin mutum, a ware majiyyaci, kuma dukan wanda ya taba gawa ya wanke jikinsa.—Leviticus 13:4-8; Litafin Lissafi 19:11-13, 17-19; Kubawar Shari’a 23:13, 14.

^ sakin layi na 9 Kuma haikalin Kan’aniyawa suna da dakuna da aka kebe domin ayyukan jima’i, Dokar Musa ta ce wadanda ba su da tsarki ba za su shiga cikin haikali ba ma. Saboda haka, tun da jima’i yana kawo rashin tsabta, babu wanda zai yi jima’i cewa daidai ne domin bauta a gidan Jehovah.

^ sakin layi na 10 Koyarwa ita ce ainihin dalilin Dokar. Hakika, Encyclopaedia Judaica ya lura cewa kalmar Ibrananci na “doka,” toh·rahʹ, tana nufin “koyarwa.”

^ sakin layi na 17 Dokar ta yi tambaya: “Itacen saura mutum ne da za ka kai masa yaki?” (Kubawar Shari’a 20:19) Philo, manazarci na karni na farko Bayahude, ya yi kaulin wannan dokar, ya yi bayani cewa Allah ya ga “rashin adalci ne fushin da ake yi da mutane a kai shi bisa abubuwa da ba su da laifin kome.”