Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 14

Jehovah Ya Yi Tanadin “Fansar Mutane Dayawa”

Jehovah Ya Yi Tanadin “Fansar Mutane Dayawa”

1, 2. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yanayin ’yan Adam, kuma mecece kadai hanyar tsira?

“DUKAN talikai suna nishi suna nakuda tare da mu.” (Romawa 8:22) Da wadannan kalmomi, manzo Bulus ya kwatanta yanayi na ban tausayi da muke ciki. Daga matsayin mutum, kamar dai babu hanyar tsira daga wahala, zunubi, da kuma mutuwa. Amma Jehovah ba shi da iyaka irin ta mutane. (Litafin Lissafi 23:19) Allah mai shari’a ya yi mana tanadin hanyar tsira daga wahalarmu. An kira ta fansa.

2 Fansar ita ce kyauta mafi girma da Jehovah ya bai wa ’yan Adam. Ta sa tsira daga zunubi da mutuwa ta yiwu. (Afisawa 1:7) Ita ce tushen begen rai madawwami, ko a sama ko kuma a aljanna a duniya. (Luka 23:43; Yohanna 3:16; 1 Bitrus 1:4) Amma shin mecece ainihi ita fansar take nufi? Ta yaya ta koya mana game da girmar shari’ar Jehovah?

Yadda Bukatar Fansa ta Kasance

3. (a) Me ya sa fansa ta wajaba? (b) Me ya sa Allah kawai bai canja hukuncin kisa a kan ’ya’yan Adamu ba?

3 Fansa ta wajaba domin zunubin Adamu. Ta wajen rashin biyayya ga Allah, Adamu ya bar gadōn ciwo, wahala, azaba, da kuma mutuwa ga zuriyarsa. (Farawa 2:17; Romawa 8:20) Allah ba zai mika kai ga motsin zuciya ya rage tsananin hukuncin kisa ba. Idan ya yi haka, to, yana taka dokarsa da kansa: “Hakkin zunubi mutuwa ne.” (Romawa 6:23) To, idan Jehovah ya taka nasa ka’ida na shari’a, hargitsi a dukan duniya da kuma yin laifi za su zama ruwan dare!

4, 5. (a) Ta yaya Shaidan ya bata wa Allah suna, kuma me ya sa Jehovah ya ga dole ne ya mai da martani ga wadannan kalubalai? (b) Wace tuhuma ce Shaidan ya yi wa bayin Jehovah masu aminci?

4 Kamar yadda muka gani a Babi na 12, tawaye a Adnin ya jawo babbar batu. Shaidan ya bata suna mai kyau na Allah. Hakika, ya zargi Jehovah da yin karya da kuma cin zali, wanda ke hana halittarsa ’yanci. (Farawa 3:1-5) Kuma domin kamar ya lalata nufin Allah na cika wannan duniyar da mutane masu adalci, ya ce Allah ya kasa. (Farawa 1:28; Ishaya 55:10, 11) Da Jehovah ya kyale wannan kalubalantarsa da aka yi, da yawa cikin halittarsa masu basira watakila za su yi rashin tabbaci da sarautarsa.

5 Shaidan kuma ya yi karya a kan bayin Jehovah masu aminci, ya tuhume su da bauta wa Allah kawai domin son kai, kuma wai idan aka matsa musu, babu wanda zai kasance da aminci ga Allah. (Ayuba 1:9-11) Wadannan batutuwa sun fi yanayi mai wuya na ’yan Adam muhimmanci. Jehovah ya ga tilas ne ya mai da wa Shaidan martani. Amma ta yaya Allah zai warware wannan batun kuma ya ceci ’yan Adam?

Fansa—Abar Daidaita

6. Wadanne furci ne aka yi amfani da su cikin Littafi Mai Tsarki wajen kwatanta hanyar ceto da Allah ya shirya ya ceci mutane?

6 Warwarewar da Jehovah ya yi, ta jinkai ne kwarai kuma cikakken adalci ne—wanda babu mutumin da zai iya kirkirowa. Amma, tana da sauki sosai. An kira ta da suna iri-iri, fanshe, sulhu, da kuma kafara. (Zabura 49:8; Daniel 9:24; Galatiyawa 3:13; Kolossiyawa 1:20; Ibraniyawa 2:17) Amma furci da watakila ya kwatanta batun da kyau shi ne wanda Yesu kansa ya yi amfani da shi. Ya ce: “Dan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta ma wadansu, shi bada ransa kuma abin fansar [Helenanci, ly ʹtron] mutane dayawa.”—Matta 20:28.

7, 8. (a) Mecece kalmar nan “fansa” take nufi a cikin Nassosi? (b) A wace hanya ce fansa ta kunshi daidaita?

7 Mecece fansa? Kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita a nan ta samo asali ne daga aikatau da take nufin “a kyale, ko a sake.” Wannan kalmar an yi amfani da ita wajen kwatanta kudi da aka biya domin musanya a saki dan fursuna na yaki. Saboda haka, za a iya bayyana ma’anar fansa da cewa abin da aka biya a sayo wani abu ne. A Nassosin Ibrananci, kalmar “fansa” (koʹpher) ta samo asali ne daga aikatau mai ma’anar “a rufe.” Alal misali, Allah ya gaya wa Nuhu cewa ya “samtse” (wani fasali na wannan kalmar) shi da karo ciki da baya.—Farawa 6:14.

8 Abin lura kuma, Theological Dictionary of the New Testament ya lura cewa wannan kalmar (koʹpher) “ko da yaushe tana nufin daidaita,” ko kuma kasancewa iri daya. Saboda haka, murfin sundukin alkawari yana da sifa iri daya da sundukin kansa. Hakanan, domin a yi fansa, ko kuma a rufe zunubi, dole ne a biya farashi da zai yi daidai da, ko kuma zai rufe barna da zunubi ya yi. Dokar Allah ga Isra’ila ta ce: “Rai maimakon rai ne, ido maimakon ido, hakori maimakon hakori, hannu maimakon hannu, kafa maimakon kafa.”—Kubawar Shari’a 19:21.

9. Me ya sa mutane masu bangaskiya suka mika hadaya ta dabba, kuma yaya Jehovah ya dauki irin wannan hadayar?

9 Mutane masu bangaskiya daga Habila zuwa sama sun mika hadayar dabbobi ga Allah. Ta wajen wannan, sun nuna cewa suna sane da zunubi da kuma bukatar fansa, kuma sun nuna bangaskiyarsu ga alkawarin Allah na ’yanci ta wajen ‘da.’ (Farawa 3:15; 4:1-4; Leviticus 17:11; Ibraniyawa 11:4) Jehovah ya dauki hadayunsu da muhimmanci kuma ya ba wa wadannan masu bauta salihanci. Duk da haka, mika dabba, da kyaunta, nuna godiya ce. Dabbobi ba za su iya rufe zunuban mutane ba, domin ba su kai mutane ba. (Zabura 8:4-8) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba shi yiwuwa jinin bajimai da na awakai shi kawarda zunubai.” (Ibraniyawa 10:1-4) Irin wadannan hadayu alama ne kawai, ta fansa ta gaskiya da za ta zo.

‘Fansa da ta Yi Daidai’

10. (a) Ga wa mai ba da fansar zai daidaita, kuma me ya sa? (b) Me ya sa hadayar mutum daya ce ta wajaba?

10 “Cikin Adamu duka suna mutuwa,” in ji manzo Bulus. (1 Korinthiyawa 15:22) Saboda haka fansar dole ta kunshi mutuwar wanda ya yi daidai da Adamu—mutum da kamili ne. (Romawa 5:14) Babu wata irin halitta da za ta daidaita kan mizanin shari’a. Sai dai kamilin mutum, wanda ba ya cikin hukuncin kisa na Adamu, shi ne zai iya ba da ‘fansa da ta yi daidai’—wadda ta yi daidai da kamilin mutum Adamu. (1 Timothawus 2:6) Ba zai wajaba a yi hadayar mutane miliyoyi babu iyaka domin su yi daidai da kowannen ’ya’yan Adamu ba. Manzo Bulus ya yi bayani: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum daya [Adamu], mutuwa kuwa ta wurin zunubi.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Romawa 5:12) “Tun da mutuwa ta wurin mutum ta ke,” Allah ya shirya fansa domin mutane ta “wurin mutum.” (1 Korinthiyawa 15:21) Ta yaya?

‘Fansa da ta yi daidai ga duka’

11. (a) Ta yaya mai ba da fansar zai ‘dandana mutuwa sabili da kowane mutum’? (b) Me ya sa Adamu da Hauwa’u ba za su amfana ba daga fansar? (Duba hasiya.)

11 Jehovah ya shirya ya samu kamilin mutum ya ba da hadayar ransa da son rai. In ji Romawa 6:23, “hakkin zunubi mutuwa ne.” Ta wajen ba da hadayar ransa mai ba da fansar zai “dandana mutuwa sabili da kowane mutum.” Watau, zai biya hakkin zunubin Adamu. (Ibraniyawa 2:9; 2 Korinthiyawa 5:21; 1 Bitrus 2:24) Wannan yana da babbar ma’ana ga sakamakon hukunci. Ta wajen shafe hukuncin kisa da yake kan ’ya’yan Adamu masu biyayya, fansar ta cire ikon halakarwa na zunubi daga tushensa. *Romawa 5:16.

12. Ka ba da misalin yadda biyan bashi daya zai iya amfanar da mutane da yawa.

12 Ga misali: A ce kana da zama a birnin da yawancin mazaunan suna aiki a wata babbar masana’anta. Kai da makwabtanka ana biyan ku kudi mai yawa domin aikinku kuma kuna da kwanciyar hankali. Har sai ranar da masana’antar ta rufe kofofinta. Me ya sa? Manajan masana’antar ya zama malalaci, ya karya jarin masana’antar. Farat daya ba ku da aiki, kai da makwabtanka ba za ku iya biyan bashinku ba. Mata, yara, da kuma wadanda suka ba da bashi dukansu sun wahala domin lalacin wannan mutumin. Akwai makawa kuwa? Hakika! Wani attajiri ya yi taimako. Ya san amfanin masana’antar. Kuma yana jin tausayin ma’aikata da yawa da iyalansu. Saboda haka, ya shirya ya biya bashin masana’antar kuma ya zuba jari. Biyan bashin ya kawo sauki ga ma’aikata da yawa da kuma iyalansu da masu binsu bashi. Hakanan, biyan bashin Adamu ya kawo amfani ga miliyoyin mutane.

Waye Ya Yi Tanadin Fansar?

13, 14. (a) Ta yaya Jehovah ya yi tanadin fansa ga ’yan Adam? (b) Ga wa aka ba da fansar, kuma me ya sa wannan ya wajaba?

13 Jehovah ne kadai zai iya tanadin “Dan rago . . . wanda yana dauke da zunubin duniya.” (Yohanna 1:29) Amma Allah bai aiko da wani mala’ika kawai ba ya ceci ’yan Adam. Maimakon haka, ya aiko da Wanda zai ba da amsa ta karshe ga kalubalantar Shaidan game da bayin Jehovah. Hakika, Jehovah ya ba da hadaya mafi girma ta wajen aiko da Dansa makadaici, “abin daularsa.” (Misalai 8:30) Da son rai, Dan Allah ya “wofinta kansa” daga rayuwarsa ta sama. (Filibbiyawa 2:7) A mu’ujizance, Jehovah ya mai da rai da kuma mutuntakar Dan farinsa zuwa cikin budurwa Maryamu Bayahudiya. (Luka 1:27, 35) Da yake shi mutum ne, za a kira shi Yesu. Amma a shari’ance, za a kira shi Adamu na biyu, domin ya daidaita da Adamu. (1 Korinthiyawa 15:45, 47) Saboda haka, Yesu zai iya ba da kansa domin hadaya ta fansa ga mutane masu zunubi.

14 Ga wa za a ba wannan fansar? Zabura 49:7 ta fadi cewa an ba da fansar ainihi “ga Allah.” Amma ba Jehovah ba ne ainihi ya shirya fansar? Kwarai kuwa, amma wannan bai mai da fansar ta zama musanya marar ma’ana ba—kamar cire kudi daga aljihu kuma a mai da shi wani aljihu. Dole ne a fahimci cewa fansar ba musanya ba ce ta zahiri amma hulda ce ta shari’a. Ta wajen yin tanadin biyar fansar, ko da yake ta yi masa zafi kwarai, Jehovah ya tabbatar da mannewarsa ga kamiltacciyar shari’arsa.—Farawa 22:7, 8, 11-13; Ibraniyawa 11:17; Yakub 1:17.

15. Me ya sa ya wajaba Yesu ya wahala kuma ya mutu?

15 A farkon shekara ta 33 A.Z., Yesu Kristi da son rai ya mika kai ga azabar da ta kai ga ba da fansar. Ya yarda aka kama shi bisa tuhumar karya, aka same shi da laifi, kuma aka kafa shi da kusa a kan itacen kisa. Amma ya wajaba ne Yesu ya wahala haka kwarai? I, domin batun aminci na bayin Allah dole ne a kammala shi. Saboda haka, Allah bai yarda Hirudus ya kashe jariri Yesu ba. (Matta 2:13-18) Amma lokacin da Yesu ya zama mutum, ya jure wa kunar farmakin Shaidan da cikakken fahimtar batun. * Ta wajen kasancewa “mai-tsarki, mara-kirsa, mara-kazanta, rababbe ne da masu-zunubi” duk da azaba da ya sha, Yesu ya tabbatar kwarai cewa Jehovah yana da bayi da za su kasance da aminci a lokacin jarraba. (Ibraniyawa 7:26) Saboda haka, babu mamaki, kafin mutuwarsa, Yesu ya yi kukar nasara: “Ya kare!”—Yohanna 19:30.

Kammala Aikinsa na Fansa

16, 17. (a) Ta yaya Yesu ya ci gaba da aikinsa na fansa? (b) Me ya sa ya wajaba Yesu ya shiga “gaban fuskar Allah sabili da mu”?

16 Har yanzu da saura Yesu ya gama aikinsa na fansa. A rana ta uku bayan mutuwar Yesu, Jehovah ya ta da shi daga matattu. (Ayukan Manzanni 3:15; 10:40) Ta wannan aikin da ba za a manta da shi ba, Jehovah ba kawai ya saka wa Dansa domin hidimarsa ta aminci ba amma ya ba shi zarafin ya gama aikinsa na fansa na Babban Firist na Allah. (Romawa 1:4; 1 Korinthiyawa 15:3-8) Manzo Bulus ya yi bayani: “Kristi, da shi ke ya zo babban [firist] . . . ba kuwa ta wurin jinin awakai da ’yan maraka ba, amma ta wurin jini nasa, ya shiga sau daya dungum cikin wuri mai-tsarki, bayanda ya kawo fansa ta har abada. Gama Kristi ba ya shiga cikin wani wuri mai-tsarki wanda aka yi da hannuwa ba, mai-kama da na gaskiya ga zancen fasali; amma cikin sama kanta, shi bayyana a gaban fuskar Allah sabili da mu yanzu.”—Ibraniyawa 9:11, 12, 24.

17 Kristi ba zai dauki jininsa na zahiri zuwa sama ba. (1 Korinthiyawa 15:50) Maimakon haka, ya dauki abin da jinin yake alama: tamani na shari’a na hadayarsa na ran kamiltaccen mutum. A gaban Allah, ya mika tamani na ransa na fansa domin musanya da mutane masu zunubi. Shin Jehovah ya karbi wannan hadayar? Hakika, wannan ya bayyana a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., sa’ad da aka zubo da ruhu mai tsarki bisa almajirai 120 a Urushalima. (Ayukan Manzanni 2:1-4) Ko da yake wannan aukuwa abin farin ciki ne, fansar a lokacin farin tanadin amfani masu kyau ne.

Fa’idar Fansar

18, 19. (a) Wadanne rukuni biyu na mutane ne suke amfana daga sulhu da jinin Kristi ya sa ya yiwu? (b) Ga wadanda suke cikin “taro mai-girma,” menene wasu amfani na yanzu da kuma na nan gaba na fansar?

18 A wasikarsa ga Kolossiyawa, Bulus ya yi bayanin cewa Allah ya ga yana da kyau ta wajen Kristi Ya sulhunta da dukan abu ta wajen yin salama ta jinin Yesu da ya zuba bisa gungumen azaba. Bulus kuma ya yi bayani cewa sulhun ya kunshi rukuni biyu dabam dabam, watau, “abubuwan da ke cikin sammai” da kuma “abubuwan da ke bisa duniya.” (Kolossiyawa 1:19, 20; Afisawa 1:10) Rukuni na farko ya kunshi Kiristoci 144,000 wadanda aka ba su begen hidimar firistoci a samaniya da kuma sarauta ta bisa duniya da Kristi Yesu. (Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 7:4; 14:1-3) Ta wajen su za a bai wa mutane masu biyayya amfanin fansar a hankali a cikin shekara dubu.—1 Korinthiyawa 15:24-26; Ru’ya ta Yohanna 20:6; 21:3, 4.

19 “Abubuwa da ke bisa duniya” mutane ne wadanda suke kan hanyar more kamiltaccen rayuwa a Aljanna a duniya. Ru’ya ta Yohanna 7:9-17 sun kwatanta su da “taro mai-girma” da za ta tsira daga “babban tsananin” da yake zuwa. Amma ba za su jira har sai wannan lokacin ba kafin su more amfanin fansar. Sun riga sun “wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Dan ragon.” Domin sun ba da gaskiya ga fansar, suna samun amfani na ruhaniya daga wannan tanadi na kauna. An riga an ce da su amintattun abokanan Allah! (Yakub 2:23) Domin hadaya ta Yesu, za su iya ‘gusowa da gaba gadi zuwa kursiyi na alheri.’ (Ibraniyawa 4:14-16) Idan suka yi zunubi, suna samun gafara ta gaske. (Afisawa 1:7) Ko da yake ajizai ne, suna da lamiri mai kyau. (Ibraniyawa 9:9; 10:22; 1 Bitrus 3:21) Saboda haka, sulhuntuwa da Allah, ba abin da ake tsammaninsa ba ne, amma abu ne da ke faruwa yanzu! (2 Korinthiyawa 5:19, 20) A cikin Alif din, za “su tsira daga bautar bacewa” kuma a karshe su samu, “ ’yanci na darajar ’ya’yan Allah.”—Romawa 8:21.

20. Ta yaya bimbini a kan fansar ta shafe ka?

20 “Na gode ma Allah ta wurin Yesu Kristi” domin hadayar! (Romawa 7:25) Mizani ne mai sauki, amma tana cike da hikima da za ta cika mu da mamaki. (Romawa 11:33) Ta wajen bimbininmu na godiya a kanta, fansar ta taba zukatanmu, ta jawo mu kusa da Allah mai shari’a. Kamar mai Zabura, muna da dalilai na yabon Jehovah domin “yana kaunar adalci da shari’a.”—Zabura 33:5.

^ sakin layi na 11 Adamu da Hauwa’u ba za su amfana ba daga fansar. Dokar Musa ta fadi wannan mizanin game da mai kisa da gangan: “Ba za ku karbi diyya a kan ran mai-kisa ba, wanda shi ke da laifin mutuwa.” (Litafin Lissafi 35:31) A bayyane yake, Adamu da Hauwa’u sun cancanci su mutu domin sun yi wa Allah rashin biyayya da saninsu kuma da gangan. Saboda haka, sun yasar da begen rayuwa ta har abada.

^ sakin layi na 15 Domin ya daidaita zunubin Adamu, Yesu dole ya mutu, ba kamilin yaro ba, amma kamilin mutum. Ka tuna cewa zunubin Adamu da son rai ne, da cikakken sanin tsananinsa da kuma sakamakonsa. Saboda haka domin ya zama “Adamu na karshe” kuma ya rufe wannan zunubi, Yesu dole ne ya zama mutum, ya zabi ya kasance da aminci ga Jehovah. (1 Korinthiyawa 15:45, 47) Saboda haka, dukan rayuwarsa ta aminci—hade da mutuwarsa ta hadaya—ta kasance “aiki guda mai-adalci.”—Romawa 5:18, 19.