Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 16

Yi “Aikin Gaskiya” Wajen Tafiya da Allah

Yi “Aikin Gaskiya” Wajen Tafiya da Allah

1-3. (a) Me ya sa muka ci albarkacin Jehovah? (b) Menene Macecinmu mai kauna yake bukata a gare mu?

KA YI tunanin ka kamu a cikin jirgin ruwa da yake nutsewa. Sa’ad da kake jin babu taimako, sai ga maceci ya zo ya cece ka. Za ka yi murna kuwa idan macecinka ya cire ka daga hadarin, ya ce: “Yanzu ka tsira”! Ba za ka yi wa wannan mutumin godiya ba? Hakika, domin albarkacinsa ka samu rai.

2 A wani hali, wannan ya kwatanta abin da Jehovah ya yi mana. Hakika, mun ci albarkacinsa. Tun da ya yi mana tanadin fansa, ya sa cetonmu ya yiwu daga hannun zunubi da mutuwa. Muna jin mun tsira, domin mun sani cewa idan muka nuna bangaskiya ga wannan hadaya mai tamani, an gafarta mana zunubinmu, kuma rayuwarmu ta har abada ba ta cikin hadari. (1 Yohanna 1:7; 4:9) Kamar yadda muka gani a Babi na 14, fansa nunakauna ce da shari’a mafi girma na Jehovah. Yaya ya kamata mu amsa?

3 Ya dace mu yi la’akari da abin da Macecinmu maikauna yake bukata a gare mu. Jehovah ya ce ta bakin annabi Mikah: “Ya dai nuna maka, ya mutum, abin da ke mai-kyau; me ne Ubangiji ya ke bida gareka kuma, sai aikin gaskiya, da son jinkai, ka yi tafiya da tawali’u tare da Allahnka?” (Mikah 6:8) Ka lura cewa daya cikin abubuwan da Jehovah yake bukata a gare mu shi ne mu yi “aikin gaskiya.” Ta yaya za mu yi haka?

Bin ‘Hakikanin Adalci’

4. Ta yaya muka sani cewa Jehovah yana son mu yi rayuwa cikin jituwa da mizanansa na adalci?

4 Jehovah ya bukace mu mu bi mizanansa na nagarta da mugunta. Tun da mizanansa nagargaru ne kuma masu adalci, muna bin shari’a da adalci sa’ad da muka bi su. “Ku koya aikin nagarta; ku bidi shari’a,” in ji Ishaya 1:17. Kalmar Allah ta yi mana gargadi mu “bidi adalci.” (Zephaniah 2:3) Kuma ta aririce mu mu “yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci.” (Afisawa 4:24) Hakikanin adalci—hakikanin shari’a—suna guje wa nuna karfi, rashin tsabta, da kuma rashin dabi’a, domin wadannan suna saba wa abin da yake mai tsarki.—Zabura 11:5; Afisawa 5:3-5.

5, 6. (a) Me ya sa ba nauyaya ba ce a gare mu mu yi ayyuka da suka jitu da mizanan Jehovah? (b) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa bidan adalci abu ne mai ci gaba?

5 Nauyaya ce a gare mu mu bi mizanan adalci na Jehovah? A’a. Zuciya da ta motsa wurin Jehovah ba ta fushi da bukatunsa. Domin muna kaunar Allahnmu da kuma yadda yake, muna so mu rayu a hanyar da za ta faranta masa rai. (1 Yohanna 5:3) Ka tuna cewa Jehovah “yana kaunar adalci.” (Zabura 11:7) Idan da gaske za mu yi koyi da shari’ar Allah, ko kuma adalci, to dole ne mu kaunaci abin da Jehovah yake kauna kuma mu guji abin da yake kyama.—Zabura 97:10.

6 Yana da wuya ga mutane ajizai su bidi adalci. Dole ne mu tube tsohon halinmu da ayyukansa na zunubi mu yafa sabo. Littafi Mai Tsarki ya ce ta wajen cikakken ilimi “a ke sabonta shi” sabon halin. (Kolossiyawa 3:9, 10) Kalmomin nan “a ke sabonta shi” suna nuna cewa yafa sabon halin abu ne da ke ci gaba, abu ne da ke bukatar kokari sosai. Ko yaya muke kokarin mu yi abin da yake daidai, akwai lokatai da ajizancinmu yake sa mu yi kuskure a magana ko kuma a ayyuka.—Romawa 7:14-20; Yakub 3:2.

7. Ta yaya ya kamata mu dauki tangarda a kokarinmu na bidan adalci?

7 Ta yaya za mu dauki tangarda a kokarinmu na bidan adalci? Hakika, ba za mu so mu rage tsananin zunubi ba. A haka kuma, kada mu kasala, mu ji cewa kurakuranmu sun sa ba mu dace da bauta wa Jehovah ba. Allahnmu mai alheri ya yi tanadin tagomashinsa ga wadanda suka tuba da gaske. Ka tuna da kalmomi masu tabbatarwa na manzo Yohanna: “Wadannan abu ni ke rubuta muku domin kada ku yi zunubi.” Sai kuma ya dada wannan zancen gaskiya: “Idan kowa ya yi zunubi [domin ajizanci da aka gada], muna da Mai-taimako wurin Uba, Yesu Kristi.” (1 Yohanna 2:1) Hakika, Jehovah ya yi tanadin hadayar fansa ta Yesu saboda mu bauta masa yadda zai karba duk da ajizancinmu. Wannan bai motsa mu mu yi iyakacin kokarinmu mu faranta wa Jehovah rai ba?

Bisharar da Kuma Shari’ar Allah

8, 9. Ta yaya shelar bishara ta nuna shari’ar Jehovah?

8 Za mu iya yin shari’a—hakika, za mu iya yin koyi da shari’ar Allah—ta wajen saka hannu sosai a wa’azin bisharar Mulkin Allah ga wasu. Wace nasaba take tsakanin shari’ar Jehovah da kuma bisharar?

9 Jehovah ba zai kawo karshen wannan zamanin ba ba tare da ya sa an yi gargadi ba da farko. A annabcinsa game da abin da zai faru a zamanin karshe, Yesu ya ce: “Dole kuma sai an yi wa’azin bishara ga al’ummai duka tukuna.” (Markus 13:10; Matta 24:3) Amfani da kalmar nan “tukuna” yana nufi cewa wasu abubuwa za su biyo bayan wa’azi ga dukan duniya. Wadannan abubuwa sun hada da kunci mai tsanani, wanda zai nufa halaka ga miyagu kuma ya bayar da hanya ga sabuwar duniya ta adalci. (Matta 24:14, 21, 22) Hakika, babu wanda zai tuhumi Jehovah da yin rashin adalci ga miyagu. Ta wajen gargadi da aka yi, ya bayar da isashen zarafi ga wadannan su yi canji kuma saboda haka su tsira daga halaka.—Yunana 3:1-10.

Muna nuna shari’a ta Allah sa’ad da muke gaya wa wasu bishara ba tare da son zuciya ba

10, 11. Ta yaya saka hannunmu cikin wa’azin bishara ke nuna shari’a ta Allah?

10 Ta yaya wa’azin bishara ya nuna shari’a ta Allah? Da farko, daidai ne mu yi abin da yake nagari da za mu iya mu taimaki wasu su samu ceto. Ka sake yin la’akari da misalin an cece ka daga jirgin ruwa da yake nutsewa. Bayan ka tsira kana cikin kwalekwale, hakika za ka so ka taimaki wasu da har ila suke cikin ruwan. Hakazalika, muna da hakki ga wadanda har yanzu suna kokari a cikin “ruwa” na wannan muguwar duniya. Hakika, da yawa suna kin sakonmu. Amma muddin Jehovah ya ci gaba da hakuri, muna da hakkin mu ba su zarafi su “kai ga tuba” domin su shigo hanyar ceto.—2 Bitrus 3:9.

11 Ta wajen yin wa’azi ga dukan wadanda muka sadu da su, muna nuna shari’a a wata muhimmiyar hanya: Muna nuna rashin son zuciya. Ka tuna cewa “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karba ne a gareshi.” (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Idan za mu yi biyayya da Shari’arsa, to, dole ne kada mu hukunta mutane. Maimakon haka, ya kamata mu yi musu bisharar ko yaya launin fatarsu, matsayinsu, ko kuma arzikinsu. Ta haka muna bai wa dukan wadanda za su saurara zarafin su ji kuma su yi na’am da bisharar.—Romawa 10:11-13.

Yadda Muke Bi da Wasu

12, 13. (a) Me ya sa ba za mu yi hanzarin hukunta wasu ba? (b) Menene ma’anar gargadin Yesu “kada ku zartar” da kuma “kada ku kayar”? (Duba hasiya.)

12 Za mu kuma nuna shari’a ta wajen bi da wasu kamar yadda Jehovah yake bi da mu. Ba shi da wuya mu hukunta wasu, muna kushe musu muna tuhumar halayensu. Amma wanene a tsakaninmu zai so Jehovah ya bincika dalilin abin da ya sa yake abu, ko kuma bincika kurakuransa babu jinkai? Ba haka Jehovah yake bi da mu ba. Mai Zabura ya lura cewa: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka kididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” (Zabura 130:3) Ba ma godiya ne cewa Allahnmu mai adalci mai jinkai ba ya mai da hankali ga kurakuranmu? (Zabura 103:8-10) To, yaya ya kamata mu bi da wasu?

13 Idan mun fahimci jinkai na shari’ar Allah, ba za mu yi hanzarin hukunta wasu ba a al’amuran da ba su shafe mu ba ko kuma wadanda ba su da muhimmanci sosai. A Hudubarsa Bisa Dutse, Yesu ya yi gargadi: “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku.” (Matta 7:1) In ji labarin Luka, Yesu ya dada cewa: “Kada ku kayar, ku kuwa ba za a kāshe ku ba.” * (Luka 6:37) Yesu ya nuna yana sane da cewa mutane ajizai suna da halin hukuntawa. Kowanne cikin masu sauraronsa wadanda suke da halin hukunta wasu da tsanani ya kamata su daina haka.

14. Domin wadanne dalilai dole mu daina “zartar” da wasu?

14 Me ya sa za ‘mu daina zartar’ wa wasu? Domin abu daya shi ne, ikonmu yana da iyaka. Almajiri Yakub ya tunasar da mu: “Daya ne kadai mai-bada shari’a, mai-yin shari’a kuma”—Jehovah. Saboda haka, Yakub ya yi tambayar kai tsaye: “Wanene kai da ka ke yi ma makwabcinka shari’a?” (Yakub 4:12; Romawa 14:1-4) Bugu da kari, ajizancinmu ba wuya zai sa hukuncinmu ya kasance da kuskure. Halaye da yawa da kuma dalilan da suka sa muka yi haka—hade da son zuciya, fahariya, kishi, da kuma adalcin-ka—za su iyabata yadda muke daukan ’yan’uwanmu mutane. Muna da karin iyaka, kuma yin bimbini bisa wadannan ya kamata ya hana mu hanzarin kushe wa wasu. Ba ma iya ganin zuciya ba; ba ma kuma iya sanin dukan yanayin wasu ba. To, wanene mu da za mu dora wa ’yan’uwanmu masu bi laifi ko kuma mu kushe kokarinsu a bautar Allah? Ya fi kyau mu yi koyi da Jehovah ta wajen ganin abin da ke nagari cikin ’yan’uwanmu maza da mata maimakon mai da hankali ga kurakuransu!

15. Wadanne kalmomi ne da kuma bi da mutane ba su da wuri tsakanin masu bauta wa Allah, me ya sa?

15 To, yaya batun hukunta wadanda suke cikin iyalinmu? Abin bakin ciki, a duniya ta yau wasu cikin hukunci mafiya tsanani an yi su ne a inda ya kamata ya zama mazaunin salama—gida. Ba abu ba ne mai wuya ka ji game da magidanta azzalumai, mata, da kuma iyaye wadanda suke yi wa iyalansu “hukuncin” zagi da dūka kullayaumin. Amma, batsa, zagi, da kuma zalunci ba su da waje tsakanin masu bauta wa Allah. (Afisawa 4:29, 31; 5:33; 6:4) Gargadin Yesu “kada ku zartar” da kuma “kada ku kayar” bai daina aiki ba yayin da muke gida. Ka tuna cewa yin shari’a ya kunshi bi da wasu kamar yadda Jehovah yake bi da mu. Kuma Allah ba ya tsananta mana a hanyar da yake bi da mu. Maimakon haka, yana “cike da tausayi” a kan wadanda suke kaunarsa. (Yakub 5:11) Misali ne mai ban sha’awa da ya kamata mu yi koyi da shi!

Dattawa Suna Hidima “da Shari’a”

16, 17. (a) Menene Jehovah yake bukata daga dattawa? (b) Menene dole a yi idan mai zunubi ya ki ya nuna ya tuba da gaske, kuma me ya sa?

16 Dukanmu muna da hakkin mu yi shari’a, amma dattawa musamman a ikilisiyar Kirista suke da wannan hakki. Ka lura da kwatanci na annabci na “hakimai,” ko kuma dattawa, da ke rubuce a Ishaya: “Duba, wata rana wani sarki za ya yi mulki cikin adalci, hakimai kuma za su yi mulki da shari’a.” (Ishaya 32:1) Hakika, Jehovah yana bukatar dattawa su yi hidima cikin shari’a. Ta yaya za su yi haka?

17 Wadannan mutane da suka kware a ruhaniya sun sani cewa ana bukatar shari’a, ko kuma adalci, a tsabtace ikilisiya. A wasu lokatai, ya wajaba dattawa su yi hukunci bisa laifi mai tsanani. Sa’ad da suke haka, suna tuna cewa shari’a ta Allah tana bidan ta yi jinkai idan hakan zai yiwu. Saboda haka, suna kokarin su kai mai zunubin ga tuba. Amma idan mai zunubin ya ki ya nuna ya tuba da gaske bayan dukan kokarinsu su taimake shi fa? A kamiltacciyar shari’a, Kalmar Allah ta umurci a dauki kakkarfar mataki: “Ku fitarda mugun nan daga cikinku.” Wannan yana nufin korar mutumin daga ikilisiya. (1 Korinthiyawa 5:11-13; 2 Yohanna 9-11) Yana bakanta wa dattawan rai su dauki irin wannan matsayi, amma sun fahimci cewa dole ne domin su kāre tsabta ta dabi’a da kuma ta ruhaniya ta ikilisiyar. Duk da haka, suna begen cewa wata rana wannan mai zunubi zai dawo hankalinsa ya komo ikilisiya.—Luka 15:17, 18.

18. Menene dattawa suke tunawa da shi sa’ad da suke ba da gargadi daga Littafi Mai Tsarki ga wasu?

18 Yin hidima domin shari’a kuma ya kunshi yin gargadi daga Littafi Mai Tsarki idan ana bukatar haka. Hakika, dattawa ba sa neman laifi daga wasu. Ba kuma suna amfani da kowane zarafi su yi gargadi ba. Amma dan’uwa mai bi zai iya yin ‘kuskure kafin ya fahimci haka.’ Tuna cewa shari’a ta Allah ba azzaluma ba ce ko kuma marar tausayi za ta motsa dattawa “cikin ruhun tawali’u [su] komo da irin wannan.” (Galatiyawa 6:1) Saboda haka, dattawa ba za su yi gargadi cikin fushi ba ko kuma da bakar magana. Maimakon haka, gargadi da aka yi cikin kauna yana karfafa wanda ake yi wa. Har sa’ad da ake tsautawa ta kai tsaye—ana lissafa sakamakon tafarki marar hikima kai tsaye—dattawa suna tuna cewa dan’uwa mai bi da ya yi laifi yana cikin tumakin garken Jehovah. * (Luka 15:7) Sa’ad da gargadi ko kuma tsautawar kauna ce ta motsa shi, kuma aka yi shi cikin kauna, zai fi komowa da mai laifin.

19. Wace shawara wani lokaci dattawa suke yankewa, kuma dole ne su yanke shawararsu bisa menene?

19 Sau da yawa, dole dattawa su yanke shawara da za ta shafi ’yan’uwansu masu bi. Alal misali, jifa-jifa dattawa suna taruwa su duba ko wasu ’yan’uwa maza a cikin ikilisiya sun kai a nada su su zama dattawa ko kuma bayi masu hidima. Dattawan sun san muhimmancin kasancewa marasa son zuciya. Suna bin farillan Allah na yin wannan nadin ya yi musu ja-gora a shawararsu, ba sa dogara bisa yadda suke ji. Saboda haka suna aikata “abu ba da tara ba, kada [su] aika komi bisa ga tara.”—1 Timothawus 5:21.

20, 21. (a) Menene dattawa suke kokarin su yi, kuma me ya sa? (b) Menene dattawa za su yi domin su taimaki “masu-raunanan zukata”?

20 Dattawa suna yin shari’a ta Allah a wasu hanyoyi ma. Bayan ya annabta cewa dattawa za su yi hidima “da shari’a,” Ishaya ya ci gaba da cewa: “[Kowanne] za ya zama kamar maboya daga iska, makāri kuma daga hadarin ruwa; kamar koguna cikin kekasashiyar kasa, kamar inuwar babban dutse cikin kasa mai-agazari.” (Ishaya 32:2) Saboda haka, dattawa suna kokari su zama tushen karfafa da kuma na wartsakewa ga ’yan’uwansu masu bi.

21 A yau, da dukan matsaloli da suke kawo kasala, mutane da yawa suna bukatar karfafa. Dattawa, menene za ku yi ku taimaki “raunanan zukata”? (1 Tassalunikawa 5:14) Ku saurare su da tausayi. (Yakub 1:19) Watakila su nemi su gaya wa wani da suka amince da shi ‘damuwa’ da take zuciyarsu. (Misalai 12:25) Ku tabbatar musu cewa ana bukatarsu, suna da tamani, kuma ana kaunarsu—hakika, Jehovah da kuma ’yan’uwansu maza da mata. (1 Bitrus 1:22; 5:6, 7) Bugu da kari, za ka iya yin addu’a domin wadannan kuma tare da su. Saurarar dattijo ya yi addu’a daga zuci dominsu yana da ban karfafa kwarai. (Yakub 5:14, 15) Kokarinku cikin kauna domin ku taimake masu raunannun zukata ba zai fadi banza ba daga Allah na shari’a.

Dattawa suna nuna shari’a ta Jehovah sa’ad da suka karfafa wadanda suka karaya a zukata

22. A wadanne hanyoyi ne za mu yi koyi da shari’a ta Jehovah, kuma menene sakamakon haka?

22 Hakika, muna kusantar Jehovah kwarai ta wajen koyi da shari’arsa! Sa’ad da muka daukaka mizanansa na adalci, sa’ad da muka yi wa wasu bishara mai ceton rai, da kuma sa’ad da muka zabi mu mai da hankali bisa halaye masu kyau na ’yan’uwanmu maimakon kushe musu, muna nuna shari’a da ke ta Allah. Dattawa, sa’ad da kuka kāre tsabtar ikilisiya, sa’ad da kuka yi gargadi daga Nassosi mai ginawa, da kuma sa’ad da kuka karfafa wadanda suka karaya a zuci, kuna nuna shari’a ta Allah. Kai, zai faranta wa Jehovah rai idan ya dubo daga sama kuma ya ga cewa mutanensa suna iyakar kokarinsu su yi “aikin gaskiya” wajen tafiya da Allahnsu!

^ sakin layi na 13 Fassarar nan “kada ku zartar” da kuma “kada ku kayar,” na nufin “kada ku fara zartarwa” da kuma “kada ku fara kayarwa.” Duk da haka, marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani ne da umurni a lamirin lokaci mai ci (mai ci gaba). Saboda haka ayyuka da aka kwatanta na kan faruwa tukuna amma za a daina su.

^ sakin layi na 18 A 2 Timothawus 4:2, Littafi Mai Tsarki ya ce, dattawa dole ne a wasu lokatai su ‘tsauta, su kwabe, su yi gargadi.’ Kalmar Helenanci da aka fassara “gargadar” (pa·ra·ka·leʹo) tana iya nufin “a karfafa.” ’Yar’uwar kalmar Helenancin, pa·raʹkle·tos, tana iya nufin mai roko a batun doka. Saboda haka, har sa’ad da dattawa suka tsauta, ya kamata su zama mataimakan wadanda suke bukatar taimako na ruhaniya.