Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 17

“Ya Zurfin . . . Hikimar Allah!”

“Ya Zurfin . . . Hikimar Allah!”

1, 2. Menene nufin Jehovah ga rana ta bakwai, kuma ta yaya aka gwada hikimar Allah a farkon rana ta bakwan?

AN HALAKA! Mutum, daukaka ta rana ta shida ta halitta, farat daya ya fado daga sama zuwa kasa. Jehovah ya furta cewa “kowane abin da ya yi,” har da mutane, “yana da kyau kwarai.” (Farawa 1:31) Amma a farkon kwana ta bakwai, Adamu da Hauwa’u suka zabi su bi Shaidan su yi tawaye. Suka fada cikin zunubi, da ajizanci, da kuma mutuwa.

2 Watakila ya bayyana kamar dai nufin Jehovah ga rana ta bakwai ta kauce a hanya ke nan babu bege. Wannan ranar, kamar ranaku shida da suka gabace ta, za ta kasance da tsawon shekaru dubbai. Jehovah ya riga ya ce da ita tsarkakkiya, kuma a karshe zai ga dukan duniya ta zama aljanna tana cike da kamiltacciyar iyalin ’yan Adam. (Farawa 1:28; 2:3) Amma bayan tawaye na bala’i, ta yaya irin wannan abu zai faru? Menene Allah zai yi? A nan an gwada hikimar Jehovah kwarai—watakila gwaji mafi girma.

3, 4. (a) Me ya sa martanin Jehovah ga tawaye a Adnin misali ne mai ban tsoro na hikimarsa? (b) Tawali’u zai motsa mu mu tuna da wace gaskiya sa’ad da muke nazarin hikimar Jehovah?

3 Jehovah ya mai da martani babu bata lokaci. Ya yanke hukunci ga ’yan tawayen na Adnin, kuma a wannan lokacin, ya ba da dan bayani game da wani abu mai ban mamaki: nufinsa ya gyara aibi da suka jawo. (Farawa 3:15) Nufin Jehovah mai hangar nesa ya mike daga Adnin cikin dukan shekaru dubbai na tarihin mutane zuwa gaba, gaba can da nisa. Ga shi mafi kyau ne kwarai marar wuya, duk da haka yana cike da hikima da mai karanta Littafi Mai Tsarki zai yi amfani da yawancin rayuwarsa a yin nazari da kuma yin bimbini a kansa. Bugu da kari, nufin Jehovah yana da cikakken tabbacin yin nasara. Zai kawo karshen dukan mugunta, zunubi, da kuma mutuwa. Zai kai amintattun mutane zuwa kamilci. Dukan wannan zai faru kafin rana ta bakwan ta kare, saboda, duk abin da ya faru, Jehovah zai cika nufinsa ga duniya da kuma ’yan Adam a kan lokaci daya rak!

4 Irin wannan hikimar tana da ban tsoro, ko ba haka ba? Manzo Bulus ya motsa ya rubuta: “Ya zurfin . . . hikimar Allah!” (Romawa 11:33) Sa’ad da muke nazarin fasaloli dabam dabam na wannan hikimar Allah, ya kamata tawali’u ya motsa mu mu tuna wata muhimmiyar gaskiya—cewa, dukan kokarinmu, sama saman wannan hikima ne mai yawa na Jehovah za mu iya tonewa. (Ayuba 26:14) Da farko, bari mu ba da ma’anar wannan hali mai ban tsoro.

Mecece Hikima ta Allah

5, 6. Wace nasaba ce take tsakanin ilimi da hikima, kuma yaya yawar ilimin Jehovah yake?

5 Hikima ba daidai take da ilimi ba. Kwamfuta ta iya rike ilimi mai yawa, amma zai yi wuya a ce wani ya kira wannan inji cewa mai hikima ne. Duk da haka, ilimi da hikima suna da nasaba. (Misalai 10:14) Alal misali, idan kana bukatar shawara mai kyau game da magance ciwo mai tsanani, za ka je ne wajen wanda ba shi da ilimi sosai game da magani? Da kyar! Saboda haka, ilimi wajibi ne ga hikima ta gaskiya.

6 Jehovah yana da ilimi marar iyaka. Tun da shi ne “Sarkin zamanai,” shi ne kadai yake raye har abada. (Ru’ya ta Yohanna 15:3) Kuma a dukan wadannan shekaru aru-aru, yana sane da kome. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu wani abu mai-rai kuma da ba a bayyane a gabansa ba: amma abubuwa duka a tsiraice su ke, budadu kuma gaban idanun wannan wanda mu ke gareshi.” (Ibraniyawa 4:13; Misalai 15:3) Tun da shi ne Mahalicci, Jehovah yana da cikakken ilimin abin da ya halitta, kuma ya lura da dukan ayyukan ’yan Adam tun daga farko. Yana bincika zuciyar kowane mutum, baya ketare ko daya. (1 Labarbaru 28:9) Tun da ya halicce mu da ’yancin zaban abin da muke so, yana yin farin ciki sa’ad da ya ga muna zaban abin da yake da kyau a rayuwa. Tun da “Mai-jin addu’a” ne, yana sauraron addu’o’i masu yawa a lokaci daya! (Zabura 65:2) Ba sai an fada ba, Jehovah ba ya mantuwa.

7, 8. Ta yaya Jehovah ya nuna fahimta, fahimi, da kuma hikima?

7 Jehovah yana da fiye da ilimi. Yana ganin yadda gaskiya take da nasaba kuma ya gano dukan batun ta wajen bayani masu yawa. Zai bincika kuma ya hukunta, ya bambance tsakanin mai kyau da marar kyau, mai muhimmanci da marar muhimmanci. Bugu da kari, yana gani fiye da sama sama kawai, yana ganin cikin zuciya. (1 Samu’ila 16:7) Saboda haka, Jehovah yana da fahimta da fahimin abubuwa da suka fi ilimi. Amma duk da haka hikima ta fi su duka.

8 Hikima tana nufin yin amfani da ilimi, fahimi, da kuma fahimta domin a samu sakamakon da ake bukata. Wasu kalmomi na asali da aka fassara su “hikima” a zahiri suna nufin “ainihin aiki” ko “hikima wajen aiki.” Saboda haka, hikimar Jehovah ba maganar baki ba ce kawai. Tana aiki, kuma tana nasara. Yin amfani da zurfin iliminsa da kuma fahimtarsa, ko da yaushe Jehovah yana yanke shawara mafi kyau, yana yin su ta hanya mafi kyau da za a yi tunaninta. Wannan ita ce hikima ta gaskiya! Jehovah ya nuna gaskiyar maganar Yesu: “Hikima kuwa ta barata bisa ga ayyukanta.” (Matta 11:19) Ayyukansa a dukan sararin samaniya suna ba da shaida mai karfi game da hikimarsa.

Tabbacin Hikima ta Allah

9, 10. (a) Jehovah ya nuna wace irin hikima, kuma ta yaya ya nuna wannan? (b) Ta yaya kwai na naman jiki ya ba da tabbacin hikima ta Jehovah?

9 Ka taba mamakin hikimar mai aikin hannu da ya yi wani abu mai kyau da yake aiki daidai? Irin wannan hikima ce mai ban sha’awa. (Fitowa 31:1-3) Jehovah da kansa shi ne tushen hikima kuma shi ne mafi girma wajen hikima. Sarki Dauda ya ce game da Jehovah: “Zan yi godiya gareka; gama kirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce kuwa: ayyukanka suna da ban al’ajabi; wannan ma raina ya sani sarai.” (Zabura 139:14) Hakika, yayin da mun koyi game da jikin mutum, hakanan za mu ga mun tsorata da hikima ta Jehovah.

10 Alal misali: Rayuwarka ta fara da kwaya daya na kwai na naman jiki—kwan maniyyi daga mamarka, ya hadu da na maniyyin babanka. Ba da dadewa ba, wannan kwan ya fara rarrabuwa. Kai, da ka fito a karshe, kwayaye tiriliyan 100 suka yi ka. Kanana ne ’yan mitsitsi. Kan allura zai dauki kusan 10,000 masu matsakaicin girma. Duk da haka, kai halitta ce na ban mamaki. Kwan ya fi dukan wani inji da mutum ya gina ko kuma masana’anta. ’Yan kimiyya sun ce kwan kamar birni ne mai ganuwa—mai kofa da mafita, tsarin sifiri, tsarin sadarwa, tushen lantarki, masana’anta, tsarin zubar da juji, ’yan tsaro, har ma da gwamnatin tarayya a cikin cibiyarsa. Bugu da kari, kwan zai iya yin wani kamarsa a cikin ’yan awoyi kadan!

11, 12. (a) Menene yake saka kwai daga dan tayi su bambanta, kuma ta yaya wannan ya jitu da Zabura 139:16? (b) A wace hanya ce kwakwalwar mutum ta nuna cewa yadda ‘aka yi mu abin mamaki ne’?

11 Hakika, ba dukan kwan naman jiki ba ne suke daidai da juna. Sa’ad da kwan dan-tayi ya ci gaba da rarrabuwa, suna daukan matsayi dabam dabam. Wasu za su zama kwai masu gina jijiyoyi; wasu na kashi, tsoka, jini, ko kuma na ido. Dukan wadannan bambancin an tsara su cikin “laburare” na kwan, wato DNA. Abin farin ciki, an hure Dauda ya ce game da Jehovah: “Idanunka sun ga gababuwan jikina tun ba su cika ba, a cikin littafinka an rubuta dukansu.”—Zabura 139:16.

12 Wadansu gabobin jiki suna da wuyar ganewa kwarai. Alal misali, ka yi la’akari da kwakwalwar mutum. Wasu sun kira ta, abin da ta fi wuya da aka gano a dukan sararin samaniya. Tana dauke da kwayayen jijiyoyi wajen biliyan 100—da yawa suna kamar taurari a damin taurari namu. Kowanne cikin wadannan kwayayen yana yin saiwa mai dubban nasaba da wasu kwayayen. ’Yan kimiyya sun ce kwakwalwar mutum za ta iya daukan dukan bayani da suke cikin dukan laburare na duniya, suka ce wajen ajiyarta, da gaske, babu magwaji. Duk da shekaru da yawa na nazari a kan wannan abin da ‘aka yi mai ban mamaki,’ ’yan kimiyya sun yarda cewa ba za su taba fahimtar yadda take aiki sosai ba.

13, 14. (a) Ta yaya tururuwa da kuma wasu halittu suka nuna cewa suna da “azanci,” kuma menene wannan ya koya mana game da Mahalicci? (b) Me ya sa za mu ce irin halitta kamar su sakar gizo an yi su “cikin hikima”?

13 Duk da haka, mutane misali ne daya kawai na hikimar Jehovah ta halitta. Zabura 104:24 ta ce: “Ya Ubangiji, ayyukanka ina misalin yawansu! Da hikima ka yi su duka: duniya cike ta ke da wadatarka.” Hikimar Jehovah tana bayyane a dukan halitta da suka kewaye mu. Alal misali, tururuwa, tana da “azanci.” (Misalai 30:24) Hakika, makauratar tururuwa an tsara su kwarai. Wasu makauratar tururuwa suna gadi, wasu suna yin gida, wasu kuma suna samun abinci daga wasu kananan kwari da ke shan furanni kamar wadannan garke ne. Wasu tururuwa suna ayyuka kamar manoma, suna shuki kuma suna girbe “iri” na naman kwari. Halittu da yawa an tsara su su yi abubuwa masu ban mamaki ta azancinsu. Kuda yana iya jujjuyawa yadda jirgin da mutum ya yi ba zai iya ba. Tsuntsaye masu kaura suna tafiya ta wajen bin taurari, ta wajen maganadiso na duniya, ko kuma ta wajen wasu irin taswira ta cikin duniya. Masana kwayoyin rai sun yi shekaru suna nazari a kan wadannan halaye masu ban mamaki da aka tsara a cikin wadannan halittun. Hakika kuwa Allah Mai Tsara wadannan abubuwa yana da hikima!

14 ’Yan kimiyya sun koyi abubuwa da yawa daga hikimar halitta ta Jehovah. Har ma da sashen injiniyoyi da ake kira kimiyyar kwaikwayo, da take neman ta yi kwaikwayon dukan abin da suke gani a halitta. Alal misali, watakila za ka zuba wa sakar gizo-gizo idanu kana mamakin kyanta. Amma injiniya yana gani abin ban mamaki ne kawai na zane-zane. Wasu zare da kamar ba su da karfi sun fi karfe karfi, sun fi ma zaren da ake rigar kāre harsashi da shi. Yaya karfinsu? Ka yi tunani an fadada sakar gizo har sai da ta kai girman taru. Irin wannan tarun zai iya kama jirgin sama na fasinja da yake cikin gudu! Hakika, Jehovah ya yi dukan wadannan abubuwa ‘cikin hikima.’

Wa ya tsara halittun duniya su kasance da “azanci”?

Hikima da ta Gabaci Duniya

15, 16. (a) Damin taurari suna ba da wane tabbaci ne na hikimar Jehovah? (b) Ta yaya matsayin Jehovah na Kwamanda Mafi Girma bisa mala’iku babu iyaka ya ba da tabbacin hikimar wannan Mai Gudanarwa?

15 Hikimar Jehovah ta bayyana a cikin dukan ayyukansa a dukan sararin samaniya. Samaniya mai taurari da muka tattauna da dan dama a Babi na 5 ba kawai suna watse ba ne a samaniya. Godiya ta tabbata ga hikimar “ka’idodin sammai” na Jehovah, taurarin an tsara su dami dami, kuma damin aka tara su cikin manyan dami, kuma aka tara manyan a cikin dami mafiya girma. (Ayuba 38:33) Babu mamaki da Jehovah ya kira wadannan halittun “runduna”! (Ishaya 40:26) Har yanzu da wata runduna kuma da ta bayyana hikimar Jehovah sosai.

16 Kamar yadda muka lura a Babi na 4, an kira Allah ‘Jehovah mai runduna’ domin matsayinsa na Kwamanda Mafi Girma na rundunar miliyoyin halittu na ruhu. Wannan tabbaci ne na ikon Jehovah. Amma ta yaya wannan ya shafi hikimarsa? Ka lura: Jehovah da Yesu ba sa zaman banza. (Yohanna 5:17) Daidai ne da ya nuna cewa, mala’iku masu yi wa Mai Girma Duka hidima suna aiki kullum. Kuma ka tuna cewa sun fi mutane, sun fi mutane fahimi da kuma iko. (Ibraniyawa 1:7; 2:7) Duk da haka, Jehovah ya saka dukan wadannan mala’iku aiki, suna aiki mai gamsarwa da farin ciki—suna “iyar da sakonsa” kuma suna “aika yardarsa”—na biliyoyin shekaru. (Zabura 103:20, 21) Lallai hikimar Mai Gudanar da wannan yana da ban tsoro!

Jehovah ne “Kadai Mai-Hikima”

17, 18. Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Jehovah ne “kadai mai-hikima,” kuma me ya sa hikimarsa za ta tsoratar da mu?

17 Bisa ga wadannan tabbacin, abin mamaki ne da Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa hikimar Jehovah babu na biyunta? Alal misali, ya ce Jehovah ne “kadai mai-hikima.” (Romawa 16:27) Jehovah ne kadai yake da hikima a cikakkiyar ma’anarta. Shi ne tushen dukan hikima ta gaskiya. (Misalai 2:6) Abin da ya sa ke nan Yesu ko da yake shi ne mafi hikima a dukan halittun Jehovah, bai dogara ga tasa hikimar ba amma ya yi magana kamar yadda Ubansa ya yi masa ja-gora.—Yohanna 12:48-50.

18 Ka lura da yadda manzo Bulus ya furta fardanci na hikimar Jehovah: “Ya zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin wuyan binciken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bi sawu!” (Romawa 11:33) Ta wajen fara ayar da “Ya,” Bulus ya nuna motsin rai sosai—a wannan batun, daukaka ce kwarai. Kalmar Helenanci da ya zaba wa “zurfin” tana da nasaba ta kusa da kalmar “rami mara matuka.” Saboda haka, kalmominsa sun kawo hoton zuci. Sa’ad da muka yi tunani bisa hikimar Jehovah, kamar dai a ce muna leka wani rami ne marar iyaka marar karshe, rami mai zurfi da fadi da ba za mu iya ma fahimtar girmansa ba, balle ma a ce mu yi bayani ko kuma mu zana shi dalla-dalla. (Zabura 92:5) Wannan ba abin da zai sa mutum saukin kai ba?

19, 20. (a) Me ya sa gaggafa alama ce da ta dace ta hikimar Allah? (b) Ta yaya Jehovah ya nuna iyawarsa ya ga abin da zai faru a nan gaba?

19 Jehovah ne “kadai mai-hikima” a wata hanya kuma: Shi kadai ne kawai zai iya ganin abin da ke zuwa a nan gaba. Ka tuna cewa, Jehovah ya yi amfani da gaggafa mai ganin nesa ya alamta hikimarsa. Babbar gaggafa watakila nauyin ta awu goma ne, amma idanunta sun fi na cikakken mutum girma. Idanun gaggafa suna gani na ban mamaki, suna sa tsuntsuwar ta hangi abinci daga nisan dubban kafafu daga sama, watakila ma nisan miloli! Jehovah ya taba cewa game da gaggafa: “Daga nesa idanunta su kan tsinkayo ta.” (Ayuba 39:29) Hakazalika, Jehovah yana iya hangar “nesa” game da lokaci—nan gaba!

20 Littafi Mai Tsarki yana cike da tabbaci cewa wannan gaskiya ce. Yana dauke da darurruwan annabce-annabce, ko kuma tarihi da aka rubuta kafin abin ya auku. Sakamakon yake-yake, tashi da faduwar masu mallakar duniya, da kuma wasu dabarar yaki na wasu kwamandojin soja duka an fade su a cikin Littafi Mai Tsarki—a wasu batun, darurruwan shekaru kafin su faru.—Ishaya 44:25–45:4; Daniel 8:2-8, 20-22.

21, 22. (a) Me ya sa babu tushen cewa Jehovah ya riga ya ga dukan abin da za ka zaba a rayuwa? Ka ba da misali. (b) Ta yaya muka sani cewa hikimar Jehovah ba cewa, ba ta da juyayi da kuma motsin rai ba ne?

21 Wannan yana nufi ne cewa, Allah ya riga ya ga abin da za ka zaba a rayuwarka? Wasu da suke koyar da koyarwar kaddara sun nace cewa wai amsar E ce. Amma, wannan ra’ayin yana kaskantar da hikimar Jehovah, domin yana nufin cewa ba zai iya ya sarrafa iyawarsa na ganin abin da yake zuwa a nan gaba ba. Alal misali: Idan kana da muryar waka kyakkyawa, ba ka da zabe ke nan, sai dai ka rika waka a koyaushe? Ra’ayin ba shi da kan gado! Hakanan, Jehovah yana iya ganin abin da zai faru a nan gaba, amma ba ya amfani da ita a kowane lokaci. Yin haka zai take mana namu son rai, kyauta mai kyau da Jehovah ba zai taba kwacewa ba.—Kubawar Shari’a 30:19, 20.

22 Mafi muni ma, tunanin kaddara yana nuna cewa hikimar Jehovah ba ta da juyayi, ba ta da kauna, ko kuma tausayi. Amma babu abin da ya wuce gaskiya! Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Jehovah yana da “hikima a zuciya.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Ayuba 9:4) Ba wai yana da zuciya ta zahiri ba, amma Littafi Mai Tsarki sau da yawa yana amfani da wannan kalmar wajen maganar abin da ke cikin mutum, wanda ya hada da motsin rai da kuma yadda mutum yake ji, kamar kauna. Saboda haka, hikimar Jehovah, kamar wasu halayensa, kauna ce take mata ja-gora.—1 Yohanna 4:8.

23. Fifitar hikimar Jehovah ya kamata ta motsa mu mu yi menene?

23 Yadda take, hikimar Jehovah abin dogara ce cikakkiya. Domin ta dara hikimarmu kwarai shi ya sa Kalmar Allah ya aririce mu cikin kauna: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: a cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” (Misalai 3:5, 6) Bari yanzu mu shiga binciken hikimar Jehovah saboda mu matso kusa da Allahnmu kadai mai hikima.