Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 18

Hikima Cikin “Maganar Allah”

Hikima Cikin “Maganar Allah”

1, 2. Wace “wasika” Jehovah ya rubuto mana, kuma me ya sa?

KA TUNA sa’ad da ka samu wasika daga wanda kake kauna da ke da zama da nesa? Abubuwa kadan ne suke ba mu farin ciki kamar wasika daga wajen wanda muke kauna. Muna farin ciki mu san yadda yake, abin da ya fuskanta da kuma abin da yake shirin yi. Irin wannan sadarwa tana kawo kaunatattu kusa da juna, ko suna nesa da juna a zahiri.

2 To, menene zai kawo mana farin ciki fiye da samun rubutaccen sako daga Allahn da muke kauna? Watau, kamar Jehovah ya rubuto mana wasika ne—Maganarsa, Littafi Mai Tsarki. A ciki ya gaya mana wanda yake, abin da ya yi, abin da yake da niyyar yi, da kuma abubuwa da yawa. Jehovah ya ba mu Kalmarsa domin yana so mu kusace shi. Allahnmu mafi hikima ya zabi hanya da ta fi kyau ya yi magana da mu. Da hikima marar iyaka a hanyar da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da kuma abin da ya kunsa.

Me Ya Sa Rubutacciyar Kalma?

3. Ta wace hanya ce Jehovah ya bayar da Doka ga Musa?

3 Wasu suna iya mamaki, ‘Me ya sa Jehovah bai yi amfani da hanya mafi ban al’ajabi ba—kamar a ce, murya daga sama—ta yi magana da mutane?’ Hakika, a wasu lokatai Jehovah ya yi magana daga sama ta wajen wakilansa mala’iku. Alal misali ya yi hakan, sa’ad da yake ba da Doka ga Isra’ila. (Galatiyawa 3:19) Muryar daga sama tana da ban tsoro—saboda haka Isra’ilawa da suka razana suka roki Jehovah kada ya yi magana da su ta wannan hanyar amma ya yi hakan ta wajen Musa. (Fitowa 20:18-20) Saboda haka, aka bai wa Musa Doka da take dauke da umurnai 600, baki da baki.

4. Ka bayyana abin da ya sa sanarwa ta maganar baki ba za ta kasance hanya ba ce matabbaciya ta bi da dokokin Allah.

4 To, inda ba a rubuta Dokar ba fa? Da Musa zai iya tuna daidai kalmomin dokar kuma ya gaya wa sauran al’ummar ba tare da kuskure ba? Tsara da suke zuwa a nan gaba fa? Da dole ne su dogara gabaki daya a kan maganar baka? Da wannan ba za ta kasance hanya ce matabbaciya ta bi da dokokin Allah ba. Ka yi tunanin abin da zai faru idan an sanar da labari ga dogon layin mutane a gaya wa mutum na farko sai shi kuma ya gaya wa na biye da shi a bi haka har karshen layin. Abin da mutumin da yake karshen layin zai ji watakila zai bambanta kwarai da na farkon. Kalmomin Dokar Allah, a nan ba ta cikin irin wannan hadarin.

5, 6. Menene Jehovah ya umurci Musa ya yi da Maganarsa, kuma me ya sa albarka ce a gare mu mu samu rubutacciyar Kalmar Jehovah?

5 Cikin hikima Jehovah ya zabi a rubuta maganarsa. Ya umurci Musa: “Ka rubuta wadannan zantattuka: gama bisa ga azancin wadannan zantattuka na yi alkawari tare da kai da Isra’ila kuma.” (Fitowa 34:27) Haka zamanin rubuta Littafi Mai Tsarki ya fara, a shekara ta 1513 K.Z. A cikin shekaru 1,610 da suka biyo baya, Jehovah ya yi “magana a zamanin dā ta . . . hanya dabam dabam,” da mutane marubuta 40 wadanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki. (Ibraniyawa 1:1) Daga baya, marubuta da suka ba da kai suka mai da hankali suka rubuta wasu domin su adana Nassosin.—Ezra 7:6; Zabura 45:1.

6 Babu shakka Jehovah ya albarkace mu da ya yi magana da mu ta rubutu. Ka taba samun wasikar da kake kaunarta kwarai—watakila domin tana da ban karfafa—da ka adana kana karatunta sau da yawa? Haka “wasikar” Jehovah take a gare mu. Domin Jehovah ya sa an rubuta maganarsa, muna iya karatunta a kai a kai kuma mu yi bimbini bisa abin da ta ce. (Zabura 1:2) Za mu iya samun “ta’aziyyar littattafai” duk lokacin da muke bukatarta.—Romawa 15:4.

Me Ya Sa Marubuta Mutane Ne?

7. Ta yaya aka ga hikimar Jehovah a wajen yin amfani da marubuta mutane?

7 Cikin hikimarsa, Jehovah ya yi amfani da mutane su rubuta Kalmarsa. Ka yi la’akari da wannan: Da Jehovah ya yi amfani da mala’iku su rubuta Littafi Mai Tsarki, da zai kasance iri daya ne? Hakika, da mala’iku za su iya kwatanta Jehovah a nasu mizanai masu girma, su furta nasu ibada a gare shi, kuma su rubuta labari game da bayin Allah masu aminci. Da kuwa za mu iya fahimtar ra’ayin wadannan kamiltattun halittu na ruhu, wadanda iliminsu, fahimi, da kuma ikonsu sun dara namu?—Ibraniyawa 2:6, 7.

“Kowane nassi hurare daga wurin Allah”

8. A wace hanya ce aka kyale marubutan Littafi Mai Tsarki su yi amfani da na su fahimi? (Duba hasiya.)

8 Ta wajen amfani da marubuta mutane, Jehovah ya ba mu daidai abin da muke bukata—rubutu da ke “hurare daga wurin Allah” amma kuma yana ga mutane. (2 Timothawus 3:16) Ta yaya ya cim ma wannan? A bayyane yake cewa ya kyale marubutan su yi amfani da nasu fahimi wajen zaban kalmomi “masu-dadin ji, da abin da aka rubuta daidai, kalmomin gaskiya ke nan.” (Mai-Wa’azi 12:10, 11) Wannan ya ba da dalilin salo iri-iri na Littafi Mai Tsarki; rubutun ya bayyana tarbiyya da kuma mutuntakar kowanne marubuci. * Duk da haka, wadannan mutane “suka yi magana daga wurin Allah, Ruhu Mai-tsarki ne yana motsa su.” (2 Bitrus 1:21) Saboda haka, aba da aka samu a karshe da gaske “maganar Allah” ce.—1 Tassalunikawa 2:13.

9, 10. Me ya sa yin amfani da marubuta mutane ya kara armashi ga Littafi Mai Tsarki?

9 Yin amfani da marubuta mutane ya bai wa Littafi Mai Tsarki armashi kwarai. Marubutansa mutane ne masu motsin zuciya kamar namu. Tun da ajizai ne, sun fuskanci gwaji da kuma matsi kamar namu. A wasu lokatai, ruhun Jehovah yana hure su su rubuta game da tasu motsawar zuciya da kuma kokawa. (2 Korinthiyawa 12:7-10) Saboda haka sun yi rubutu na mai maganar, kalmomi da babu mala’ikan da zai iya furta su.

10 Ka dauki Sarki Dauda na Isra’ila ga misali. Bayan ya yi zunubi mai tsanani, Dauda ya rubuta zabura da a ciki ya furta zuciyarsa, yana rokon gafarar Allah. Ya rubuta: “Ka tsarkake ni daga zunubina. Gama ina sane da laifofina: zunubina yana gabana tuttur. Ga shi, cikin mugunta aka sifanta ni; cikin zunubi kuma uwata ta dauki cikina. Kada ka yashe ni daga gabanka; kada kuma ka dauke mini ruhunka mai-tsarki. Hadayu na Allah karyayyen ruhu ne: karyayyar zuciya mai-tuba ba za ka rena ta ba, ya Allah.” (Zabura 51:2, 3, 5, 11, 17) Ka ga bakin cikin marubucin? Waye in ba mutum ajizi ba zai iya furta irin wannan sosuwar zuci?

Me Ya Sa Littafi ne Game da Mutane?

11. Wadanne misalai ne na rayuwa ta gaskiya aka hada cikin Littafi Mai Tsarki ‘domin koyonmu’?

11 Har ila da wani abu kuma da ya kara ga armashin Littafi Mai Tsarki. Galibi, littafi ne game da mutane—mutane na zahiri—wadanda suke bauta wa Allah da kuma wadanda ba sa bauta masa. Mun karanta game da abubuwa da suka fuskanta, wahalarsu, da kuma farin ciki. Mun ga sakamakon abin da suka zaba a rayuwa. An rubuta irin wadannan labaran ‘domin koyonmu.’ (Romawa 15:4) Ta wajen wannan misali na rayuwa ta gaskiya, Jehovah ya koyar a hanyoyi da suke taba zukatanmu. Ga wasu misalai.

12. Tarihin Littafi Mai Tsarki game da mutane marasa aminci ya taimake mu a wace hanya?

12 Littafi Mai Tsarki ya fadi game da mutane marasa aminci, har ma miyagu, da kuma abin da ya faru da su. A cikin wadannan tarihin, ayyukan sun nuna halaye da ba a so, sun kasance da sauki mu fahimci hakan. Alal misali, wace doka ce game da rashin aminci za ta fi wannan nunin halin Yahuda wanda ya shirya ya ci amanar Yesu? (Matta 26:14-16, 46-50; 27:3-10) Irin wannan tarihin yana taba zuciyarmu kwarai, yana taimakonmu mu fahimci kuma mu ki kazaman halaye.

13. A wadanne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki ya taimake mu mu fahimci halaye masu kyau?

13 Littafi Mai Tsarki kuma ya kwatanta bayin Allah da yawa masu aminci. Mun karanta game da ibadarsu da kuma aminci. Mun ga misalan halayen da ya kamata mu koya domin mu kusaci Allah. Ka dauki bangaskiya ga misali. Littafi Mai Tsarki ya bayyana ma’anar bangaskiya kuma ya gaya mana yadda take da muhimmanci idan muna so mu faranta wa Allah rai. (Ibraniyawa 11:1, 6) Amma kuma Littafi Mai Tsarki yana dauke da misalai na bangaskiya kwarai. Ka yi tunanin bangaskiya da Ibrahim ya nuna sa’ad da ya yi kokarin ya mika Ishaku. (Farawa, sura 22; Ibraniyawa 11:17-19) Ta wajen irin wannan tarihi, kalmar nan “bangaskiya” tana ba da bayani kuma takan kasance da saukin fahimta. Kai, hikima ce da Jehovah ba kawai ya shawarce mu mu koyi halaye masu kyau ba, amma kuma ya yi tanadin misalai game da su!

14, 15. Menene Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da wata mace da ta zo haikali, kuma menene muka koya game da Jehovah daga wannan labarin?

14 Tarihin rayuwa ta gaske da suke cikin Littafi Mai Tsarki sau da yawa suna koya mana wani abu game da yadda Jehovah yake. Ka yi la’akari da abin da muka karanta game da matar da Yesu ya lura da ita a cikin haikali. Yayin da yake zaune kusa da ma’aji, Yesu yana kallo sa’ad da mutane suke jefa kyautarsu. Mutane masu arziki da yawa suka zo, suna ta zubawa daga “cikin falalarsu.” Amma Yesu ya kafa wa wata gwauruwa matalauciya ido. Kyautar ta kunshi “anini biyu.” * Shi ne iyakar kudi da take da su. Yesu, wanda yake nuna irin ra’ayin Jehovah game da batutuwa ya ce: “Abin da wannan gwauruwa matalauciya ta zuba sun fi nasu duka da suka zuba cikin ma’aji.” Bisa ga wadannan kalmomi, ta zuba fiye da dukan abin da suka zuba idan aka hada.—Markus 12:41-44; Luka 21:1-4; Yohanna 8:28.

15 Ba shi da muhimmanci ne cewa a cikin dukan mutane da suka zo haikalin a wannan ranar, aka ware wannan gwauruwar kuma aka ambace ta a cikin Littafi Mai Tsarki? Ta wajen wannan misalin, Jehovah ya koya mana cewa shi Allah ne mai godiya. Yana farin ciki ya karbi kyautarmu ta zuciya daya, ko yaya suke idan aka gwada su da abin da wasu suka bayar. Jehovah ya yi amfani da hanya mafi kyau ya koyar da mu wannan gaskiya mai taba zuciya!

Abin da Ba Ya Cikin Littafi Mai Tsarki

16, 17. Ta yaya ake ganin hikimar Jehovah har a cikin abin da ya zabi ba zai hada cikin Kalmarsa ba?

16 Idan ka rubuta wasika ga wadda kake kauna, wasikar za ta kasance tana da iyaka. Saboda haka, za ka zabi abin da za ka rubuta. Hakanan, Jehovah ya zabi ya fadi game da wasu mutane da kuma wasu aukuwa cikin Kalmarsa. Amma a wadannan labaran na kwatanci, Littafi Mai Tsarki bai fadi kome dalla-dalla ba. (Yohanna 21:25) Alal misali, sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya fadi game da zartar da hukuncin Allah, bayanin ba zai amsa dukan tambayoyinmu ba. Hikimar Jehovah ta bayyana har a cikin abin da ya zaba ba zai hada cikin Kalmarsa ba. Ta yaya?

17 Hanyar da aka rubuta Littafi Mai Tsarki tana gwada abin da yake zuciyarmu. Ibraniyawa 4:12 ta ce: “Maganar [ko kuma, sakon] Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa rarraban rai da ruhu, . . . tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” Sakon Littafi Mai Tsarki yana hudawa da zurfi, yana bayyana tunaninmu na gaske da kuma nufe-nufenmu. Wadanda suke karatunsa da ra’ayin sukā sau da yawa suna tuntube domin labaran da ba sa dauke da cikakken bayani ba za su gamsar da su ba. Irin wadannan mutanen har suna tambaya ko Jehovah da gaske yana da kauna, da hikima, kuma mai gaskiya.

18, 19. (a) Me ya sa bai kamata mu damu ba idan wani labari na Littafi Mai Tsarki ya jawo tambayoyi da ba za mu iya samun amsarsu nan take ba? (b) Me ake bukata domin a fahimci Kalmar Allah, kuma ta yaya wannan tabbaci ne na hikima mai girma ta Jehovah?

18 Akasarin haka, sa’ad da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau da zuciyar kirki, za mu koya game da Jehovah a matani da Littafi Mai Tsarki gaba dayansa ya bayyana shi. Saboda haka, ba ya ta da mana hankali idan a wani labari ya jawo tambayoyi da ba za mu iya samun amsarsu ba a take. Alal misali: Sa’ad da muke wasan wasa kwakwalwa, watakila da farko ba mu ga wani bangare ba ko kuma ba mu fahimci yadda wani bangare yake da nasaba da wasu ba. Duk da haka, watakila mun tare bangarori da suka isa mu fahimci yadda hoton gabaki dayansa yake. Hakazalika, sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki, da kadan kadan za mu koyi game da irin Allah da Jehovah yake, sai cikakken hoton ya bayyana. Ko idan da farko ba mu fahimci wasu labarai ba ko kuma mu ga yadda ya jitu da mutuntakar Allah, nazarinmu na Littafi Mai Tsarki ya riga ya koya mana kwarai game da Jehovah da zai iya sa mu ga cewa shi babu shakka mai kauna ne, Allah mai gaskiya.

19 To, domin mu fahimci Kalmar Allah, dole ne mu karanta kuma mu yi nazarinsa da zuciyar kirki da kuma rashin son zuciya. Wannan ba tabbaci ba ne na hikima mai girma na Jehovah? Mutane masu basira suna iya rubuta littafi da sai “masu hikima da fahimi” za su iya fahimta. Amma a rubuta littafi da sai masu zuciyar kirki za su fahimta—yana bukatar hikima ta Allah!—Matta 11:25.

Littafin “Sahihiyar Hikima”

20. Me ya sa Jehovah ne kadai zai gaya mana hanya mafi kyau na rayuwa, kuma menene Littafi Mai Tsarki ya kunsa da zai taimake mu?

20 A cikin Kalmarsa, Jehovah ya gaya mana hanya mafi kyau da za mu rayu. Tun da Mahaliccinmu ne, ya san abin da muke bukata fiye da yadda muka sani. Bukatun mutane—hade da muradin kauna, farin ciki, da kuma nasara wajen nasaba—ya kasance duk daya. Littafi Mai Tsarki yana dauke da arziki na “sahihiyar hikima” da za ta taimake mu mu yi rayuwa mai ma’ana. (Misalai 2:7) Kowanne sashe na wannan littafin nazari yana dauke da babi da yake nuna yadda za mu yi amfani da gargadi na hikima ta Littafi Mai Tsarki, amma bari mu bincika daya kawai.

21-23. Wane gargadi na hikima zai taimake mu mu guje wa fushi da kiyayya?

21 Ka taba lura cewa mutane da suke da kiyayya da kuma gāba sau da yawa suna ji wa kansu ne? Gāba kaya ce mai nauyin dauka a rayuwa. Sa’ad da muke rike da ita, tana cika tunaninmu, tana dauke mana salama, kuma ta kashe mana farin ciki. Nazari na kimiyya ya nuna cewa yin gāba za ta iya kara mana hadarin ciwon zuciya da kuma wasu cututtuka masu tsanani. Shekaru aru-aru kafin wadannan nazarin kimiyya, Littafi Mai Tsarki da hikima ya ce: “Ka daina yin fushi, ka rabu da hasala.” (Zabura 37:8) Amma ta yaya za mu yi wannan?

22 Kalmar Allah ta ba da wannan gargadi cikin hikima: “Hankalin mutum ya kan sa fushinsa shi yi jinkiri: daraja ne kuwa a gareshi shi kyale laifi.” (Misalai 19:11) Fahimi iya hangar nesa ce, ganin fiye da zahiri. Fahimi yana dauke da fahimta, domin zai taimake mu mu fahimci abin da ya sa wani ya yi magana ko kuma ya yi abu a wata hanya. Da kokarin mu fahimci ainihin abin da ya motsa shi, yadda yake ji, da kuma yanayin zai iya taimakonmu wajen korar miyagun tunani da kuma zuci game da shi.

23 Littafi Mai Tsarki yana dauke da wannan karin shawarwari: “Kuna hakuri da juna, kuna gafarta ma juna.” (Kolossiyawa 3:13) Furcin nan “kuna hakuri da juna” yana nufin jimiri da wasu, kyale halayensu da ba ma so. Irin wannan jimirin zai taimaka wajen guje wa kananan kiyayya. “Gafarta” tana dauke da ma’anar a kyale kiyayya ta wuce. Allah mai hikima ya sani cewa muna bukatar mu gafarta wa wasu sa’ad da akwai dalilin yin haka. Wannan ba domin a kyautata musu ba ne kawai amma kuma domin namu kwanciyar rai da kuma zuciya. (Luka 17:3, 4) Hikima tana kunshe cikin Kalmar Allah!

24. Me ke faruwa idan muka sa rayuwarmu ta jitu da hikima ta Allah?

24 Domin kaunarsa marar iyaka ta motsa shi, Jehovah yana so ya yi magana da mu. Ya zabi hanya mafi kyau—rubutacciyar “wasika” da mutane suka rubuta sa’ilin da ruhu mai tsarki yake yi musu ja-gora. Domin haka, hikimar Jehovah ce take cikin shafuffukansa. Wannan hikima ‘tabbatacciya ce kwarai.’ (Zabura 93:5) Sa’ad da muka sa rayuwarmu ta jitu da ita, da kuma sa’ad da muka gaya wa wasu, ta haka muna kusantar Allahnmu da ya fi hikima. A babi na gaba, za mu tattauna wani misali fitacce na hikima mai hangar nesa na Jehovah: iyawarsa ya fadi abin da zai kasance a nan gaba kuma ya cika nufinsa.

^ sakin layi na 8 Alal misali, Dauda, wanda makiyayi ne, ya yi amfani da misalai daga rayuwar makiyayi. (Zabura ta 23) Matta, wanda dā mai karban haraji ne, ya yi magana sau da yawa bisa kudi da kuma muhimmancinsu. (Matta 17:27; 26:15; 27:3) Luka, wanda likita ne, ya yi amfani da kalmomi da suka nuna wannan.—Luka 4:38; 14:2; 16:20.

^ sakin layi na 14 Kowacce wannan saba drachma dari ce, mafi kankantar tsaba ta Yahudawa da ake amfani da shi a lokacin. Dari biyu sun yi daidai da kashi daya cikin sattin da hudu na kudin aikin yini. Wadannan tsaba biyu ba za su iya ma su sayi gwara guda ba, tsuntsu mai araha da matalauta suke amfani da shi wajen abinci.