Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Babi Na 19

“Hikima ta Allah Cikin Asiri

“Hikima ta Allah Cikin Asiri

1, 2. Wane “asiri” ne ya kamata mu so, kuma me ya sa?

ASIRAI! Domin suna ta da hankali, sau da yawa yana yi wa mutane wuya su rike. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Darajar Allah ne a rufe al’amari.” (Misalai 25:2) Hakika, tun da shi ne Mamallakin Duka kuma Mahalicci, Jehovah yana rufe wasu abubuwa daga mutane har sai lokaci ya kai ya bayyana su.

2 Amma, da akwai asiri mai ban mamaki da Jehovah ya bayyana a cikin Kalmarsa. An kira shi “asirin nufin [Allah].” (Afisawa 1:9) Sani game da shi zai yi fiye da cika burinka na son saninsa. Sani na wannan asirin zai kai ka ga ceto kuma zai ba ka fahimi cikin hikimar Jehovah marar iyaka.

An Bayyana Shi da Kadan Kadan

3, 4. Ta yaya annabci da aka rubuta a cikin Farawa 3:15 ya ba da bege, wane “asiri” ya kunsa?

3 Sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, kamar dai nufin Jehovah na cewa kamiltattun mutane su zauna cikin aljanna ta duniya ya wargaje. Amma babu bata lokaci Allah ya warware matsalar. Ya ce: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi za ya kuje kanka, kai kuma za ka kuje duddugensa.”—Farawa 3:15.

4 Wadannan kalmomin suna da wuyar fahimtawa. Wacece wannan mace? Wanene macijin? Wanene “zuriyar” da zai kuje kan macijin? Adamu da Hauwa’u sai dai su yi zato. Duk da haka, kalmar Allah ta ba da bege ga dukan wani amintaccen dan wadannan marasa aminci. Nagarta za ta yi nasara. Nufin Jehovah zai cika. Amma ta yaya? To, wannan ai shi ne asirin! Littafi Mai Tsarki ya kira shi “hikima ta Allah cikin asiri; watau hikima wadda take boye.”—1 Korinthiyawa 2:7.

5. Ka ba da misalin abin da ya sa Jehovah yake bayyana asirinsa da kadan kadan.

5 Tun da “Mai Tone asiri” ne, Jehovah a karshe zai ba da bayani dalla-dalla game da cika asirinsa. (Daniel 2:28) Amma zai yi haka a hankali, da kadan kadan. Alal misali, za mu iya tunanin yadda uba mai kauna yake amsawa sa’ad da dansa ya yi tambaya, “Baba, ta yaya aka haife ni?” Uba mai hikima zai yi masa bayani iyakacin yadda yaron zai iya fahimta. Yayin da yaron ya kara girma, baban sai ya ba shi karin bayani. Hakanan, Jehovah ne ya san lokacin da mutanensa ya kamata ya ba su bayani game da nufinsa.—Misalai 4:18; Daniel 12:4.

6. (a) Menene muhimmancin alkawari? (b) Me ya sa abin mamaki ne cewa Jehovah yana yin alkawari da mutane?

6 Ta yaya Jehovah yake ba da irin wannan bayanin? Ya yi amfani da jerin alkawura, ya bayyana da yawansu. Watakila, ka taba sa hannu cikin wata yarjejeniya—kila don ka sayi gida ko kuma ka ari kudi ko kuma ka ba da bashi. Irin wannan alkawarin yana dauke da tabbaci cewa abin da aka yi dawajewa a kai za a cika. Amma me ya sa Jehovah yake bukatar ya yi alkawari da mutane? Hakika, kalmarsa ta isa tabbaci na alkawarinsa. Hakan gaskiya ne, duk da haka, sau da yawa Allah ya tabbatar da maganarsa da alkawari. Irin wannan alkawari mai karfi yana ba mu mu mutane ajizai dalili mai karfi na dogara ga alkawarin Jehovah.—Ibraniyawa 6:16-18.

Alkawari da Ibrahim

7, 8. (a) Wane alkawari Jehovah ya yi da Ibrahim, kuma wane bayani ya bayar game da asirin? (b) Ta yaya Jehovah da kadan kadan ya bayyana zuriyar Da na alkawarin?

7 Fiye da shekaru dubu biyu bayan an kori mutum daga cikin Aljanna, Jehovah ya gaya wa bawansa mai aminci Ibrahim: “Zan ribanbanya tsatsonka kamar taurarin sama, . . . cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka; domin ka yi biyayya da maganata.” (Farawa 22:17, 18) Wannan ba alkawari ba ne kawai; Jehovah ya yi dawajewa ne kuma ya tokare shi da rantsuwa. (Farawa 17:1, 2; Ibraniyawa 6:13-15) Lallai abin mamaki ne Mamallakin Dukan Halitta ya yi alkawarin zai albarkaci mutane!

“Zan ribanbanya tsatsonka kamar taurarin sama”

8 Alkawarin da ya yi da Ibrahim ya bayyana cewa Dan alkawarin zai kasance mutum, domin zai zama daga zuriyar Ibrahim. Amma zai kasance wanene? Da shigewar lokaci, Jehovah ya bayyana cewa dan Ibrahim Ishaku ne zai kasance kakan Dan. A tsakanin ’ya’yan Ishaku biyu, an zabi Yakubu. (Farawa 21:12; 28:13, 14) Daga baya, Yakubu ya furta wannan kalmomi na annabci bisa daya cikin ’ya’yansa goma sha biyun: “Kandirin ba za ya rabu da Yahuda ba, Sandar mai-mulki kuma daga tsakanin sawayensa, har Shiloh [“Wanda Ya Kasance a Gare Shi Ne”] ya zo; zuwa gare shi kuma biyayyar al’ummai za ta nufa.” (Farawa 49:10) Yanzu an sani cewa Dan zai zama sarki, wanda zai fito daga Yahuda!

Alkawari da Isra’ila

9, 10. (a) Wane alkawari Jehovah ya yi da al’umma ta Isra’ila, kuma wace kāriya wannan alkawari ya yi? (b) Ta yaya Dokar ta nuna bukatar fansa ta mutane ?

9 A shekara ta 1513 K.Z., Jehovah ya yi tanadin da ya gyara hanya domin karin bayani game da asirin. Ya yi alkawari da zuriyar Ibrahim, al’ummar Isra’ila. Ko da yake a yanzu bai kasance ba, wannan Alkawari na Dokar Musa bangare ne mai muhimmanci na nufin Jehovah don kawo Da na alkawarin. Ta yaya? Ka yi la’akari da hanyoyi uku. Na farko, Dokar tana kama da ganuwa ce ta kāriya. (Afisawa 2:14) Umurnanta na adalci sun kasance kamar katanga ne tsakanin Yahudawa da Mutanen wasu Al’ummai. Ta haka Dokar ta taimaka wajen tsare zuriyar Da na alkawarin. Godiya ta tabbata ga wannan kāriyar, al’ummar ta kasance sa’ad da lokacin Allah ya yi da za a haifi Almasihu a kabilar Yahuda.

10 Na biyu, Dokar ta nuna bukatar da mutane suke da ita na fansa. Kamiltacciyar Doka, ta nuna kasawar mutane masu zunubi su bi ta daidai. Saboda haka, ta bayyana “ketaren doka, har wannan zuriya ta zo wadda an yi alkawari da ita.” (Galatiyawa 3:19) Ta wajen hadayar dabbobi, Dokar ta yi tanadin kafarar zunubai. Amma tun da, kamar yadda Bulus ya rubuta, “ba shi yiwuwa jinin bajimai da na awakai shi kawarda zunubai,” wadannan hadayu suna alamta hadayar fansa ce ta Kristi. (Ibraniyawa 10:1-4) Ga Yahudawa masu aminci, wannan alkawarin ya kasance “mai-tsaronmu shi kai mu ga Kristi.”—Galatiyawa 3:24.

11. Wane bege Dokar alkawari ta bai wa Isra’ila, amma me ya sa wannan al’ummar gabaki dayanta ta yi hasara?

11 Na uku, wannan alkawarin ya ba wa al’ummar Isra’ila bege mai girma. Jehovah ya gaya musu idan suka kasance amintattu ga alkawarin, za su zama ‘mulki na firistoci kuma, al’umma mai tsarki.’ (Fitowa 19:5, 6) Isra’ila ta jiki a karshe ta yi tanadin mutane na farko wadanda suke cikin mulkin firistoci na sama. Duk da haka, gabaki dayanta, Isra’ila ta yi wa Dokar alkawarin tawaye, ta ki Da Almasihun, ta yi hasarar wannan begen. To, su waye za su cika wannan mulkin firistoci? Kuma ta yaya wannan al’umma mai albarka za ta kasance da nasaba da Da na alkawarin? Wannan bangaren asirin za a bayyana shi a nan gaba a lokaci na Allah.

Alkawarin Mulki da Dauda

12. Wane alkawari Jehovah ya yi da Dauda, kuma wane bayani ya kara yi game da asirin Allah?

12 A karni na 11 K.Z., Jehovah ya kara ba da bayani game da asirin sa’ad da ya yi wani alkawari. Ya yi wa Sarki Dauda mai aminci alkawari: “Zan kafa zuriyarka daga bayanka, . . . zan kuma kafa mulkinsa. . . . ni kuma zan tabbatadda kursiyin mulkinsa har abada.” (2 Samu’ila 7:12, 13; Zabura 89:3) Yanzu an nuna cewa Da na alkawarin zai fito ne daga gidan Dauda. Amma mulkin dan Adam zai iya kasance “har abada”? (Zabura 89:20, 29, 34-36) Kuma irin wannan sarki dan Adam zai iya ya ceci mutane daga zunubi da mutuwa?

13, 14. (a) In ji Zabura ta 110, wane alkawari Jehovah ya yi wa Sarkinsa da ya nada? (b) Wane karin bayani game da Dan mai zuwa aka yi ta wajen annabawan Jehovah?

13 An hure Dauda ya rubuta: “Ubangiji ya ce ma ubangijina, Ka zauna ga hannun damana, har in maida makiyanka matashin sawunka. Ubangiji ya yi rantsuwa, ba kuwa za shi tuba ba, Kai [Firist ]ne har abada bisa tabi’ar Melchizedek.” (Zabura 110:1, 4) Kalmomin Dauda ya shafi Da na alkawarin kai tsaye, ko kuma Almasihu. (Ayukan Manzanni 2:35, 36) Wannan Sarkin zai yi sarauta, ba a Urushalima ba amma daga sama a “hannun damana” Jehovah. Wannan zai ba shi iko ba bisa kasar Isra’ila ba kawai, amma bisa dukan duniya. (Zabura 2:6-8) A nan an bayyana karin abu. Ka lura cewa Jehovah ya rantse cewa Almasihun zai zama “[firist] . . . bisa tabi’ar Melchizedek.” Kamar Melchizedek, wanda ya yi hidima na sarki da firist a zamanin Ibrahim, Dan mai zuwa, Allah ne zai nada shi ya yi hidima ta Sarki da Firist!—Farawa 14:17-20.

14 A cikin shekaru da yawa, Jehovah ya yi amfani da annabawansa su ba da karin bayani game da asirinsa. Alal misali, Ishaya ya bayyana cewa Dan zai mutu mutuwar hadaya. (Ishaya 53:3-12) Mikah ya fadi wurin da za a haifi Almasihun. (Mikah 5:2) Daniel ya annabta daidai lokacin da Dan zai bayyana da kuma mutuwarsa.—Daniel 9:24-27.

An Bayyana Asirin!

15, 16. (a) Ta yaya Dan Jehovah ya zo ya kasance ta wurin “mace”? (b) Menene Yesu ya gāda daga wajen iyayensa mutane, kuma yaushe Dan alkawarin ya zo?

15 Yadda wadannan annabce-annabce za su cika ya kasance asiri har sai da Dan ya bayyana. Galatiyawa 4:4 ta ce: “Amma sa’anda cikar kwanaki ta zo, Allah ya aiko Dansa, haifaffe daga mace.” A shekara ta 2 K.Z., mala’ika ya gaya wa budurwa Bayahudiya mai suna Maryamu: “Ga shi kuwa, za ki yi ciki, za ki haifi da, za ki ba shi suna Yesu. Shi za ya zama mai-girma, za a ce da shi Dan Madaukaki: Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dauda: . . . Ruhu Mai-tsarki za ya auko miki, ikon Madaukaki kuma za ya inuwantadda ke: domin wannan kuwa abin nan da za a haifa, za a ce da shi mai-tsarki, Dan Allah.”—Luka 1:31, 32, 35.

16 Daga baya, Jehovah ya kaurar da ran Dansa daga sama zuwa cikin Maryamu, sai ya zamanto mace ta haife shi. Maryamu mace ce ajiza. Duk da haka, Yesu bai gaji ajizanci ba daga wajenta, domin “Dan Allah” ne shi. Amma duk da haka, iyayen Yesu na jiki, da yake suna daga zuriyar Dauda ne sun ba shi ikon magājin Dauda. (Ayukan Manzanni 13:22, 23) A lokacin baftismar Yesu a shekara ta 29 A.Z., Jehovah ya nada shi da ruhu mai tsarki kuma ya ce: “Wannan Dana ne, kaunatacena.” (Matta 3:16, 17) A karshe, Dan ya zo! (Galatiyawa 3:16) Lokaci ya yi domin bayyana abubuwa da yawa game da asirin.—2 Timothawus 1:10.

17. Ta yaya aka ba da bayani game da ma’anar Farawa 3:15?

17 A lokacin hidimarsa, Yesu ya bayyana macijin Farawa 3:15 cewa Shaidan ne kuma zuriyar macijin, mabiyan Shaidan ne. (Matta 23:33; Yohanna 8:44) Daga baya, an bayyana yadda dukan wadannan za a kuje su har abada. (Ru’ya ta Yohanna 20:1-3, 10, 15) Kuma an bayyana macen cewa “Urushalima wadda take sama” ce, kungiyar Jehovah ta halittun ruhu wadda take sama kamar matarsa. *Galatiyawa 4:26; Ru’ya ta Yohanna 12:1-6.

Sabon Alkawari

18. Menene dalilin “sabon alkawarin”?

18 Watakila bayyana mafi ban mamaki duka ta zo ne a daren mutuwar Yesu sa’ad da ya gaya wa mabiyansa masu aminci game da “sabon alkawari.” (Luka 22:20) Kamar wanda ya shige, alkawarin Dokar Musa, wannan sabon alkawari domin ya ba da “mulki na firistoci” ne. (Fitowa 19:6; 1 Bitrus 2:9) Amma, wannan alkawarin zai tabbatar da al’umma ce ta ruhaniya ba ta jiki ba, “Isra’ila ta Allah,” da ta kunshi kawai mabiya Kristi masu aminci. (Galatiyawa 6:16) Wadanda suke cikin wannan sabon alkawari za su yi aiki tare da Yesu wajen kawo albarka ga zuriyar ’yan Adam!

19. (a) Me ya sa sabon alkawari ya yi nasara wajen ba da “mulki na firistoci”? (b) Me ya sa aka kira shafaffu Kiristoci “sabon halitta,” kuma nawa ne za su yi hidima a sama da Kristi?

19 Amma me ya sa sabon alkawarin ya yi nasara wajen ba da “mulki na firistoci” su albarkaci ’yan Adam? Domin maimakon hukunta almajiran Kristi cewa masu zunubi ne, ya yi tanadin gafara ga zunubansu ta wajen hadayarsa. (Irmiya 31:31-34) Da zarar sun kasance da tsabta a gaban Jehovah, zai dauke su zuwa iyalinsa na samaniya kuma ya shafe su da ruhu mai tsarki. (Romawa 8:15-17; 2 Korinthiyawa 1:21) Saboda da haka suna shaida ‘sake haihuwa . . . zuwa ga bege mai-rai . . . da aka ajiye a sama.’ (1 Bitrus 1:3, 4) Domin wannan matsayi mai girma sabo ne ga mutane, shafaffu Kiristoci da aka nada ana kirar su “sabon halitta.” (2 Korinthiyawa 5:17) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa a karshe mutane 144,000 ne za su saka hannu wajen sarauta a sama bisa ’yan Adam da aka cece su.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1-4.

20. (a) Wane bayani ne aka yi game da asirin a shekara ta 36 A.Z.? (b) Su waye za su more alkawarin albarka da aka yi wa Ibrahim?

20 Tare da Yesu, wadannan shafaffu suka zama “zuriyar Ibrahim.” * (Galatiyawa 3:29) Wadanda aka zaba da farko Yahudawa ne na jiki. Amma a shekara ta 36 A.Z., wani bangaren asirin ya bayyana: Mutanen Al’ummai, ko kuma wadanda ba Yahudawa ba, su ma za su samu begen zuwa sama. (Romawa 9:6-8; 11:25, 26; Afisawa 3:5, 6) Shafaffu Kiristoci ne kawai za su more albarkar da aka yi wa Ibrahim alkawarinsa? A’a, domin hadayar Yesu za ta amfani dukan duniya. (1 Yohanna 2:2) Da shigewar lokaci, Jehovah ya bayyana cewa “taro mai-girma” marar iyaka zai tsira a karshen zamanin Shaidan. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14) Da yawa kuma za a ta da su daga matattu da begen rayuwa har abada a Aljanna!—Luka 23:43; Yohanna 5:28, 29; Ru’ya ta Yohanna 20:11-15; 21:3, 4.

Hikimar Allah da Kuma Asirin

21, 22. A wadanne hanyoyi ne asirin Jehovah ya bayyana hikimarsa?

21 Asirin nuna “hikima iri iri ta Allah” ce mai ban mamaki. (Afisawa 3:8-10) Lallai Jehovah ya nuna hikima wajen fito da wannan asirin, sai kuma a bayyana shi kadan kadan! Ya yi la’akari da iyakar ’yan Adam, yana kyale su su nuna ainihin zuciyarsu.—Zabura 103:14.

22 Jehovah har ila ya nuna hikima marar kama wajen zaban Yesu ya zama Sarki. Dan Jehovah ya fi dukan wata halitta tabbaci. Da yake raye da jini da tsoka, Yesu ya fuskanci masifu iri iri da yawa. Ya fahimci matsalolin mutane kwarai. (Ibraniyawa 5:7-9) Wadanda suke sarauta tare da Yesu fa? A cikin karnuka, maza da mata—da aka zaba daga dukan launin fata, harsuna, da kuma wurare dabam dabam—an nada su. Babu wata matsala da wani cikinsu bai fuskanta ba kuma ya yi nasara. (Afisawa 4:22-24) Rayuwa karkashin wadannan sarakuna firistoci masu jinkai zai zama da dadi!

23. Wace gata Kiristoci suke da ita game da asirin Jehovah?

23 Manzo Bulus ya rubuta: “Asirin ke nan da ke boye tun daga dukan zamanu da tsararaki: . . . an bayyana shi ga tsarkakansa.” (Kolossiyawa 1:26) Hakika, shafaffu masu tsarki na Jehovah sun zo ga fahimtar asirin sosai, kuma sun koya wa miliyoyi wannan ilimin. Lallai gata ce da dukanmu muke da ita! Jehovah “ya sanashe mu asirin nufinsa.” (Afisawa 1:9) Bari mu gaya wa wasu wannan asiri mai ban mamaki, mu taimake su su fahimci hikimar Jehovah Allah mai wuyar fahimta!

^ sakin layi na 17 “Asirin ibada” ya bayyana a kan Yesu. (1 Timothawus 3:16) Ya dade yana asiri, cewa ko wani zai iya kasance da cikakken aminci ga Jehovah. Yesu ya bayyana amsar. Ya kasance da amincinsa a cikin dukan wani gwaji da Shaidan ya kawo masa.—Matta 4:1-11; 27:26-50.

^ sakin layi na 20 Yesu ma ya yi “alkawarin . . . mulki” da wannan rukunin. (Luka 22:29, 30) Watau, Yesu ya yi alkawari da “karamin garke” cewa za su yi sarauta tare da shi a sama, suna matsayi na biyun na zuriyar Ibrahim.— Luka 12:32.