Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 21

Yesu Ya Bayyana ‘Hikima Daga Allah’

Yesu Ya Bayyana ‘Hikima Daga Allah’

1-3. Yaya makwabtan Yesu na dā suka dauki koyarwarsa, kuma menene suka kasa ganewa game da shi?

MASU sauraron suka yi mamaki. Saurayin, Yesu yana tsaye a gabansu a majami’a yana koyarwa. Ba bako ba ne a gare su—ya yi girma a birninsu, kuma ya yi aikin sassaka na shekaru da yawa a tsakaninsu. Watakila wasu sun zauna a gidaje da Yesu ya taimaka aka gina, ko kuma sun yi aiki a gonarsu da karkiyar da shi ya sassaka da hannunsa. * Amma yanzu yaya za su bi koyarwar wannan masassaki a dā?

2 Yawancin wadanda suke sauraro sun yi mamaki, suna tambaya: “Daga ina mutumin nan ya sami wannan hikima?” Amma sun kuma ce: “Wannan ba shi ne masassakin nan ba, dan Maryamu.” (Matta 13:54-58; Markus 6:1-3) Abin nadama, wadanda suka taba zama makwabtan Yesu suka ce, ‘Wannan masassakin, mutum ne kawai kamar mu.’ Duk da hikima da take daga maganarsa, suka ki shi. Ba su sani ba cewa hikima da ya bayar ba tasa ba ce.

3 A ina Yesu ya sami wannan hikimar? “Abin da ni ke koyarwa ba nawa ba ne,” in ji shi, “amma nasa ne wanda ya aiko ni.” (Yohanna 7:16) Manzo Bulus ya yi bayani cewa Yesu ya zama “hikima garemu daga wurin Allah.” (1 Korinthiyawa 1:30) Hikimar Jehovah aka bayyana ta wajen Dansa, Yesu. Hakika, gaskiya ne da Yesu ya ce: “Da ni da Ubana daya ne.” (Yohanna 10:30) Bari mu bincika wajaje uku da Yesu ya nuna ‘hikima daga Allah.’

Abin da Ya Koyar

4. (a) Menene jigon sakon Yesu, kuma me ya sa wannan yake da muhimmanci kwarai? (b) Me ya sa shawarar Yesu koyaushe mai amfani ce kuma domin amfanin masu sauraronsa?

4 Da farko, ka yi la’akari da abin da Yesu ya koyar. Jigon sakonsa shi ne “bishara ta mulkin.” (Luka 4:43) Wannan yana da muhimmanci kwarai domin aikin da Mulkin zai yi wajen kunita ikon mallaka na Jehovah kuma ya kawo albarka ta dindindin ga ’yan Adam. A koyarwarsa, Yesu kuma ya ba da shawara mai hikima domin rayuwa ta yau da kullum. Ya tabbatar da kansa cewa shi ne “Mai-shawara” da aka annabta. (Ishaya 9:6) Hakika, me ya sa shawararsa ba za ta zama abin ban mamaki ba? Yana da ilimi kwarai na Kalmar Allah da kuma nufinsa, ya kuma fahimci kwarai yanayin mutane, da kuma kauna mai zurfi ga mutane. Saboda haka, shawararsa koyaushe mai amfani ce kuma domin amfanin masu sauraronsa. Yesu ya furta “maganar rai na har abada.” Hakika, idan aka bi shawararsa tana kai wa zuwa ceto.—Yohanna 6:68.

5. Menene wasu batutuwa da Yesu ya taba a Huduba a kan Dutse?

5 Huduba a kan Dutse fitaccen misali ne na hikima marar kama da aka gani a cikin koyarwar Yesu. Hudubarsa, da aka rubuta a Matta 5:3–7:27, watakila za ta dauki minti 20 ne kawai ya yi ta. Amma gargadinta ba ta da lokaci—tana da muhimmanci daidai kamar ranar da aka yi ta. Yesu ya taba batutuwa da yawa, har da yadda za a gyara dangantaka da wasu. (5:23-26, 38-42; 7:1-5, 12), yadda za a kasance da tsabta ta dabi’a (5:27-32), da kuma yadda za a yi rayuwa mai ma’ana (6:19-24; 7:24-27). Amma Yesu ya yi fiye da gaya wa masu sauraronsa tafarkin hikima; ya nuna musu ta wajen bayani, koyarwa, da kuma ba da tabbaci.

6-8. (a) Wadanne dalilai ne masu kyau Yesu ya bayar domin guje wa alhini? (b) Menene ya nuna cewa shawarar Yesu ta nuna hikima daga sama?

6 Alal misali, ka lura da shawara ta hikima game da yadda za a bi da damuwa game da abin duniya, kamar yadda aka fada a Matta sura 6. “Kada ku yi alhini saboda ranku, abin da za ku ci, ko kuwa abin da za ku sha; ko saboda jikinku, abin da za ku yafa,” Yesu ya ba mu shawara. (Aya ta 25) Abinci da tufafi wajibi ne don rayuwa, kuma daidai ne a damu game da samun wadannan. Amma Yesu ya gaya mana ‘kada mu yi alhini’ saboda wadannan abubuwa. * Me ya sa?

7 Ka saurara yayin da Yesu ya yi bayani mai gamsarwa. Tun da Jehovah ya ba mu rai da kuma jiki, ba zai iya ya ba mu abinci ba ne da zai rayar da rai da kuma tufafi da zai rufe jiki? (Aya ta 25) Idan Allah yana bai wa tsuntsaye abinci kuma yana yi wa furanni tufafi kyawawa, yaya kuwa ba zai kula da mutane masu bauta masa ba! (Ayoyi 26, 28-30) Hakika, damuwa da yawa ba ta da amfani. Ba za ta kara rayuwarmu ba ko kadan. * (Aya ta 27) Ta yaya za mu guje wa alhini? Yesu ya ba da shawara: Ku ci gaba da bai wa bautar Allah waje na farko a rayuwarku. Wadanda suka yi haka za su tabbata cewa dukan bukatunsu Ubansu na samaniya zai “kara” musu. (Aya ta 33) A karshe, Yesu ya bayar da shawara mai amfani kwarai—ku dauki kwana daddaya. Me ya sa za ku kara alhinin gobe a kan na yau? (Aya ta 34) Kari ga wannan, me ya sa za ka damu da abin da watakila ba zai faru ba ma? Amfani da irin wannan shawara zai kāre mu daga ciwon zuciya a cikin wannan duniya da ta cika da damuwa.

8 Hakika, shawarar da Yesu ya bayar tana da amfani a yau kamar yadda take sa’ad da ya ba da ita kusan shekaru 2,000 da suka shige. Wannan ba tabbaci ba ne na hikima daga sama? Shawara mai kyau kwarai daga wajen mutane masu ba da shawara tana shudewa kuma a maimaita ta ko kuma a sake ta. Amma duk da lokaci mai yawa da suka shige koyarwar Yesu ta kasance mai amfani. Amma wannan bai kamata ya ba mu mamaki ba, domin wannan Mai-shawara yana fadin “zantattukan Allah ne.”—Yohanna 3:34.

Yadda Yake Koyarwa

9. Menene wasu sojoji suka ce game da koyarwar Yesu, kuma me ya sa wannan ba zugugu ba ne kawai?

9 Waje na biyu da Yesu ya nuna hikima ta Allah yadda yake koyarwa ne. A wani lokaci, wasu sojoji da aka aike su su kama shi suka koma hannu goma, suna cewa: “Babu mutumin da ya taba yin magana haka.” (Yohanna 7:45, 46) Wannan ba zugugu ba ne kawai. Dukan mutane da suka taba rayuwa, Yesu, wanda ya zo daga “bisa,” yana da ilimi mai yawa da kuma fahimi daga inda ya yi magana. (Yohanna 8:23) Hakika ya koyar yadda babu wani mutumin da zai iya. Ka bincike hanyoyi biyu kawai na wannan Malami mai hikima.

‘Jama’a suka yi mamakin koyarwarsa’

10, 11. (a) Me ya sa za mu yi mamaki game da yin amfani da misalai na Yesu? (b) Mecece almara, kuma wadanne misalai ne suka nuna dalilin da ya sa almara ta Yesu tana da kyau wajen koyarwa?

10 Amfani da kyau da misalai. Aka gaya mana, “Yesu ya fada ma taron da misalai; ba ya fada musu kome ba sai game da misali.” (Matta 13:34) Babu abin da za mu yi sai dai mamaki ga irin wannan iyawarsa marar kama na koyar da gaskiya mai muhimmanci ta wajen amfani da abubuwa na yau da kullum. Manoma suna shuki, mata suna shirin gasa gurasa, yara suna wasa a kasuwa, masunta suna zuba taru, makiyaya suna neman tunkiya da ta bata—wadannan abubuwa ne da masu sauraronsa suke gani sau da yawa. Sa’ad da aka hada abubuwa da aka saba da su, irin wadannan gaskiya suna kahuwa da wuri da kuma zurfi cikin zuciya.—Matta 11:16-19; 13:3-8, 33, 47-50; 18:12-14.

11 Yesu sau da yawa ya yi amfani da almara, gajeren labari daga inda ake koyar gaskiya ta dabi’a da kuma ta ruhaniya. Tun da yake labarai sun fi sauki a tuna da su kuma a fahimce su fiye da abubuwa da ba a gani, almarar ta taimaka wajen adana koyarwar Yesu. A cikin almara da yawa, Yesu ya kwatanta Ubansa kwarai yadda ba za a iya manta da shi ba da wuri. Alal misali, waye ba zai fahimci darasin wannan almara na da almubazzari—cewa wanda ya baude idan ya nuna tuba ta gaskiya, Jehovah zai ji tausayinsa kuma ya sake karbansa?—Luka 15:11-32.

12. (a) Ta wace hanya ce Yesu ya yi amfani da tambayoyi a koyarwarsa? (b) Ta yaya Yesu ya rufe bakin wadanda suka tuhumi ikonsa?

12 Kwarewa wajen yin amfani da tambaya. Yesu ya yi amfani da tambayoyi domin ya sa masu sauraro su kai ga nasu kammala, su bincika abin da ke motsa su, da kuma shawarar da suka yanke. (Matta 12:24-30; 17:24-27; 22:41-46) Sa’ad da shugabannan addini suka yi tambaya ko yana da iko daga wurin Allah, Yesu ya amsa: “Baftismar Yohanna, daga sama ta ke, ko kuwa daga wurin mutane ce?” Da tambayar ta ba su mamaki, suka ce tsakaninsu: “Idan mun ce, Daga sama; sai shi ce mana, Don menene fa ba ku bada gaskiya gareshi ba? Amma idan mun ce, Daga wurin mutane ne; muna jin tsoron taron; gama duka sun maida Yohanna annabi ne.” A karshe, suka amsa: “Ba mu sani ba.” (Markus 11:27-33; Matta 21:23-27) Da tambaya mai sauki, Yesu ya rufe bakinsu kuma ya bayyana mugunta da take zukatansu.

13-15. Ta yaya almara ta Basamariye makwabci ta nuna hikimar Yesu?

13 A wani lokaci Yesu yana hada hanyoyin ta wajen saka tambaya mai saka tunani a cikin misalinsa. Sa’ad da wani lauya Bayahude ya tambayi Yesu abin da ake bukata domin a samu rai na har abada, Yesu ya mai da shi ga Dokar Musa, wadda ta umurci kaunar Allah da kuma ta makwabci. Da yake so ya tabbatar da kansa mai adalci ne, mutumin ya yi tambaya: “Wanene makwabcina?” Yesu ya amsa ta wajen ba da wani labari. Wani Bayahude yana tafiya shi kadai sa’ad da ’yan fashi suka fāda masa, suka kyale shi rai a hannun Allah. Sai ga wasu Yahudawa biyu suna wucewa, na farkon firist ne sai kuma Balawi. Duk suka kyale shi. Amma sai wani Basamariye ya zo, tausayi ya motsa shi ya daddaure raunukan mutumin ya kai shi masauki inda zai warke. Da ya kare labarin, sai Yesu ya tambayi mai yi masa tambaya: “Wa ka aza ya zama makwabci ga wanda ya gamu da mafasa?” Mutumin dole ya ba da amsa: “Wannan da ya nuna masa jinkai.”—Luka 10:25-37.

14 Ta yaya almarar ta nuna hikimar Yesu? A zamanin Yesu, Yahudawa suna amfani da kalmar nan “makwabci” ga wadanda suke bin al’adunsu ne kawai—hakika ba ga Samariyawa ba. (Yohanna 4:9) Da Yesu ya fadi labarin cewa Basamariye ne ya ji rauni kuma Bayahude ya yi taimako, da wannan zai juya kiyayyar? Yesu cikin hikima ya kaga labarin cewa Basamariye ne ya taimaki Bayahude. Ka lura kuma da tambayar da Yesu ya yi a karshen labarin. Ya gyara fahimtarsu na kalmar nan “makwabci.” Lauya watau ya yi tambaya ne: ‘Waye ya kamata ya zama abin kaunata?’ Amma Yesu ya yi tambaya: “A cikin wadannan uku fa, wa ka aza ya zama makwabci.” Yesu ya mai da hankali ba ga wanda aka yi wa kirki ba, wanda ya yi raunin, amma ga wanda ya yi kirki, Basamariye din. Makwabci na gaskiya yana daukan zarafi ya nuna kauna ga wasu ko da daga ina suka fito. Yesu ba zai bayyana darasin fiye da haka ba.

15 Abin mamaki ne da mutane suka yi mamakin ‘hanyar koyarwa’ ta Yesu kuma suka matsa wajensa? (Matta 7:28, 29) A wani lokaci “taro mai-yawa” suka kasance kusa da shi na kwana uku, babu abinci ma!—Markus 8:1, 2.

Hanyar Rayuwarsa

16. A wace hanya ce Yesu ya ba da “ainihin tabbacin” cewa hikima ta Allah ce take yi masa ja-gora?

16 Waje na uku da ya nuna hikimar Jehovah shi ne hanyar rayuwarsa. Ayyukan hikima a bayyane suke. “Wanene a cikinku mai-hikima ne?” almajiri Yakubu ya yi tambaya. Sai ya amsa tambayarsa, yana cewa: “Bari dabi’arsa da ta dace ta ba da ainihin tabbacin haka.” (Yakub 3:13, The New English Bible) Yadda Yesu ya bi dabi’a ya ba da “ainihin tabbacin haka” cewa hikima ta Allah ce take ja-gorarsa. Bari mu bincika yadda ya nuna fahimi, a hanyar rayuwarsa da kuma a sha’aninsa da wasu.

17. Wadanne tabbaci ne muke da su cewa Yesu ya kasance da cikakken daidaita a rayuwarsa?

17 Ka lura cewa mutane wadanda ba su da fahimi sau da yawa suna kama gefe daya? Hakika yana bukatar hikima a daidaita. Nuna hikima ta Allah, Yesu yana da daidaita kwarai. Fiye da kome, ya saka abubuwa na ruhaniya farko a rayuwarsa. Ya shagala kwarai a cikin aikin shelar bishara. “Dalilin fitowata ke nan.” (Markus 1:38) Abin duniya, ba su suka fi muhimmanci ba a gare shi; kamar dai ba shi da abin duniya. (Matta 8:20) Duk da haka, ba marar farin ciki ba ne. Kamar Ubansa, ‘Allah mai farin ciki,’ Yesu mutum ne mai farin ciki, kuma ya kara ga farin cikin wasu. (1 Timothawus 1:11; 6:15) Sa’ad da ya halarci wani bikin aure—ainihi abin da ake kade-kade, wake-wake, da kuma farin ciki—bai je ba ne don ya bata sha’ani. Sa’ad da giya ta kare, ya mai da ruwa ta zama giya, aba da take “sa zuciyar mutum ta wartsake.” (Zabura 104:15; Yohanna 2:1-11) Yesu ya amsa gayyata da yawa zuwa dina, kuma sau da yawa ya yi amfani da irin wannan zarafin wajen koyarwa.—Luka 10:38-42; 14:1-6.

18. Ta yaya Yesu ya nuna fahimi marar kure a sha’aninsa da almajiransa?

18 Yesu ya nuna fahimi marar kure a sha’aninsa da wasu. Fahiminsa game da yadda mutane suke ya sa ya fahimci almajiransa kwarai. Ya tabbata cewa ba kamilai ba ne. Duk da haka, ya fahimci gano halayensu masu kyau. Ya ga wadannan mutane da Jehovah ya jawo za su kasance na kirki. (Yohanna 6:44) Duk da kurakuransu, Yesu ya nuna ya yarda da su da son rai. Ya nuna wannan yardar, ya ba da hakki mai girma ga almajiransa. Ya umarce su su yi wa’azin bishara, kuma ya tabbata za su iya su cika wannan umurnin. (Matta 28:19, 20) Littafin Ayukan Manzanni ya tabbatar da cewa sun yi aikin da aka umarce su cikin aminci. (Ayukan Manzanni 2:41, 42; 4:33; 5:27-32) A bayyane yake, Yesu ya yi hikima da ya yarda da su.

19. Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi mutum “mai-tawali’u ne, mai-kaskantar zuciya”?

19 Kamar yadda muka lura a Babi na 20, Littafi Mai Tsarki ya danganta tawali’u da kuma rashin tsanantawa da hikima. Hakika, Jehovah ne ya kafa misali mafi kyau a wannan batun. Amma Yesu kuma fa? Yana dadada rai mu ga yadda Yesu ya nuna tawali’u a sha’aninsa da almajiransa. Tun da mutum ne kamili, ya fi su. Duk da haka, bai raina almajiransa ba. Ko kuma ya nemi ya nuna su ba kome ba ne. Akasarin haka, ya yi la’akari da kasawarsu kuma ya yi hakuri da kurakuransu. (Markus 14:34-38; Yohanna 16:12) Ba shi da muhimmanci ne da yara ma suka sake a wajen Yesu? Babu shakka suna matsa wajensa domin sun fahimci cewa shi mutum “mai-tawali’u ne, mai-kaskantar zuciya.”—Matta 11:29; Markus 10:13-16.

20. Ta yaya Yesu ya nuna la’akari a sha’aninsa da mace ta Al’umma wadda ’yarta take da aljan?

20 Yesu ya nuna tawali’u na Allah har yanzu a wata hanya. Yana da la’akari, sa’ad da jinkai ya sa wannan ya dace. Alal misali, ka tuna da lokacin da mace daga Al’ummai ta roke shi ya warkar da ’yarta da take da aljan. A hanyoyi uku dabam dabam Yesu ya nuna da farko cewa ba zai taimake ta ba—na fari, ya ki ya yi mata magana; na biyu, ya fada kai tsaye cewa an aiko shi, ba domin na Al’ummai ba ne, amma domin Yahudawa; kuma na uku, ta wajen ba da misali da ya nuna haka. Duk da haka, matar ta nace, wannan ya ba da tabbacin bangaskiya mai karfi kwarai. Yin la’akari da wannan yanayi, menene Yesu ya yi? Ya yi abin da ya ce ba zai yi ba. Ya warkar da ’yar matar. (Matta 15:21-28) Yana da tawali’u na ban mamaki, ko ba haka ba? Ka tuna, tawali’u ne tushen hikima ta gaske.

21. Me ya sa za mu yi kokari mu yi koyi da mutuntaka, furci, da kuma hanyoyin Yesu?

21 Za mu yi godiya cewa Linjila ta bayyana mana kalmomi da kuma ayyukan mutum mafi hikima da ya taba rayuwa! Bari mu tuna cewa Yesu kamilin kamani ne na Ubansa. Ta wajen bin mutuntaka, furci, da kuma hanyoyin Yesu, za mu koyi hikima da take zuwa daga bisa. A cikin babi na gaba za mu ga yadda za mu yi amfani da hikima ta Allah a rayuwarmu.

^ sakin layi na 1 A lokacin Littafi Mai Tsarki, ana kiran masassaka wajen gina gidaje, gyara kujeru, da kuma kayan aikin gona. Justin Martyr, na karni na biyu A.Z., ya rubuta game da Yesu: “Yana aikin sassaka sa’ad da yake tsakanin mutane, yana gyara kotoci da karkiya.”

^ sakin layi na 6 Aikatau na Helenanci da aka fassara “yi alhini” yana nufin “a janye hankalin zuciya.” Kamar yadda aka yi amfani da shi a Matta 6:25, tana nufin damuwa kwarai da take janye ko kuma raba zuciya, ta dauke murna daga rayuwa.

^ sakin layi na 7 Babu shakka, nazarin kimiyya ya nuna cewa damuwa da yawa za ta iya sa mu cikin hadarin kamuwa da ciwon zuciya da kuma wasu cututtuka masu yawa da za su rage tsawon rai.