Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 22

Hikima Mai-Fitowa Daga Bisa” Tana Aiki Kuwa a Rayuwarka?

Hikima Mai-Fitowa Daga Bisa” Tana Aiki Kuwa a Rayuwarka?

1-3. (a) Ta yaya Sulemanu ya nuna hikima mai yawa wajen warware jayayyar mata game da jariri? (b) Me Jehovah ya yi alkawari zai ba mu, kuma wadanne tambayoyi ne suka taso?

AL’AMARI ne mai wuya—mata biyu suna jayayya a kan jariri. Matan suna zama a gida daya, kowacce ta haifi da, kwanaki ne kawai suka raba su. Yaro dayan ya mutu, amma yanzu kowacce tana da’awar ita ce mamar yaron da yake raye. * Babu shaida game da abin da ya faru. Watakila an kai al’amarin gaban alkali a karamin kotu amma abin ya faskara. A karshe, aka kai wannan al’amarin gaban Sulemanu, sarkin Isra’ila. Zai iya ya bayyana gaskiyar al’amarin kuwa?

2 Bayan ya saurara na dan lokaci sa’ad da matan suke jayayya, Sulemanu ya aika a kawo takobi. Sai, da tabbaci, ya ba da umurni a raba yaron gida biyu, a ba kowacce mace bari guda. A take, uwar ta ainihi ta roki sarki ya ba da yaron—dan da take kauna—ga mace dayar. Amma dayar macen ta nace a raba jaririn gida biyu. Sulemanu yanzu ya san gaskiyar. Ya san kaunar uwa ga dan cikinta, kuma ya yi amfani da wannan ilimin ya warware jayayyar. Ka yi tunanin kwanciyar ran uwar sa’ad da Sulemanu ya ba ta jaririn, ya ce: “Ita ce uwar.”—1 Sarakuna 3:16-27.

3 Hikima mai yawa, ko ba haka ba? Sa’ad da mutane suka ji yadda Sulemanu ya warware al’amarin, Sai suka cika da tsoro, “gama sun gane hikimar Allah tana cikinsa.” Hakika, hikimar Sulemanu kyauta ce daga Allah. Jehovah ya ba shi “zuciya mai-hikima, mai-ganewa.” (1 Sarakuna 3:12, 28) To, mu kuma fa? Mu ma za mu iya samun hikima ta ibada? I, an hure Sulemanu ya rubuta: “Ubangiji yana bada hikima.” (Misalai 2:6) Jehovah ya yi alkawari ya ba da hikima—iya yin amfani kwarai da ilimi, fahimta, da fahimi—ga wadanda suke nema da gaske. Ta yaya za mu samu hikima da take zuwa daga sama? Kuma ta yaya za mu yi amfani da ita a rayuwarmu?

“Ka Sami Hikima”—Ta Yaya?

4-7. Wadanne abubuwa hudu ake bukata domin samun hikima?

4 Dole ne sai muna da fahimi ko kuma muna da ilimi mai yawa kafin mu samu hikima ta Allah? A’a. Jehovah yana shirye ya ba mu hikima ko daga ina muka fito kuma ko yaya iliminmu. (1 Korinthiyawa 1:26-29) Amma dole ne mu dauki matakin samu, domin Littafi Mai Tsarki ya aririce mu mu “sami hikima.” (Misalai 4:7) Ta yaya za mu yi haka?

5 Na farko, muna bukatar mu ji tsoron Allah. “Tsoron Ubangiji mafarin hikima ne [“takun farko ga hikima,” The New English Bible],” in ji Misalai 9:10. Tsoron Allah shi ne tushen hikima ta gaskiya. Me ya sa? Ka tuna cewa hikima ta kunshi iya amfani da ilimi daidai. Tsoron Allah, ba a yi rawar jiki ba ne a gabansa domin razana, amma a yi sujjada a gabansa da ban girma, daraja, da kuma dogara. Irin wannan tsoron yana da kyau kuma yana motsawa. Yana motsa mu mu sa rayuwarmu ta jitu da ilimi na Allah da kuma hanyoyinsa. Babu wani tafarki da ya fi hikima da za mu bi, domin mizanan Jehovah koyaushe suna kawo amfani mafi girma ga dukan wadanda suka bi su.

6 Na biyu, dole ne mu kasance da tawali’u da kuma filako. Hikimar Allah ba za ta kasance ba ba tare da tawali’u ba da kuma filako. (Misalai 11:2) Menene wannan? Idan muna da tawali’u da kuma filako, za mu yarda da son rai cewa ba mu san dukan abu ba, da cewa ra’ayinmu ba kullum ba ne yake daidai, saboda haka, muna bukatar mu san ra’ayin Jehovah bisa batun. Jehovah yana “tsayayya da masu-girman kai,” amma yana farin ciki da kuma ba da hikima ga masu tawali’u a zuciya.—Yakub 4:6.

Domin mu samu hikima ta Allah, dole ne mu yi kokari mu neme ta

7 Abu na uku mai muhimmanci shi ne nazarin rubutacciyar Kalmar Allah. An bayyana hikimar Jehovah a cikin Kalmarsa. Domin mu sami wannan hikima, dole ne mu yi kokari mu neme ta. (Misalai 2:1-5) Farilla ta hudu ita ce addu’a. Idan da gaske mun roki hikima daga wurin Allah, zai ba mu hannu sake. (Yakub 1:5) Addu’o’inmu domin taimakon ruhunsa ba zai fadi banza ba. Kuma ruhunsa zai taimake mu mu samu arziki a cikin Kalmarsa da za ta taimake mu magance matsaloli, mu guje wa masifa, kuma mu yanke shawara cikin hikima.—Luka 11:13.

8. Idan da gaske mun samu hikima ta Allah, ta yaya za ta bayyana?

8 Kamar yadda aka lura a Babi na 17, hikimar Jehovah tana da amfani. Saboda haka, idan da gaske mun samu hikima ta Allah, za ta bayyana a halayenmu. Almajiri Yakub ya kwatanta ’ya’yan hikima ta Allah sa’ad da ya rubuta: “Hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce dafari, bayan wannan mai-salama ce, mai-saukin hali, mai-siyasa, cike da jinkai da kyawawan ’ya’ya, mara-kokanto, mara-riya ce.” (Yakub 3:17) Yayin da muke tattauna kowanne cikin wadannan bangarorin hikima ta Allah, za mu iya tambayar kanmu, ‘Shin hikima mai fitowa daga bisa tana aiki kuwa a rayuwata?’

“Tsatsarka Ce . . . , Bayan Wannan Mai-Salama Ce”

9. Menene yake nufi a kasance da tsatsarka, kuma me ya sa ya dace cewa tsatsarka ita ce hali na farko na hikima da aka rubuta?

9 “Tsatsarka ce dafari.” Kasancewa tsatsarka yana nufin kasancewa mai tsabta marar kazanta, ba kawai a waje ba amma a ciki. Littafi Mai Tsarki ya danganta hikima da zuciya, amma hikima mai zuwa daga bisa ba za ta shiga zuciyar da ta kazantu da mugun tunani, da sha’awa, da kuma nufi ba. (Misalai 2:10; Matta 15:19, 20) Amma, idan zuciyarmu tsatsarka ce—watau, iyakan yadda ta yiwu ga mutane ajizai—za mu “rabu da mugunta, [mu] yi nagarta.” (Zabura 37:27; Misalai 3:7) Bai dace ba ne cewa tsatsarka ita ce hali na farko na hikima da aka rubuta? Ban da haka ma, idan ba mu da tsabta a dabi’a ko kuma a ruhaniya, ta yaya za mu nufi wasu halaye na hikima da take zuwa daga bisa?

10, 11. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance masu neman salama? (b) Idan ka ji ka yi wa dan’uwa mai bi laifi, ta yaya za ka tabbatar da cewa kai mai yin salama ne? (Ka duba hasiya.)

10 “Bayan wannan mai-salama ce.” Hikima ta Allah tana motsa mu mu nemi salama, wanda diyar ruhun Allah ce. (Galatiyawa 5:22) Muna kokari mu guje wa bata “daurin salama” da ya hada kan mutanen Jehovah. (Afisawa 4:3) Muna kuma iyakacin kokarinmu mu mai da salama sa’ad da an yi tashin hankali. Me ya sa wannan yake da muhimmanci? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zama cikin salama: Allah kuwa na kauna da na salama za ya zauna tare da ku.” (2 Korinthiyawa 13:11) Idan muka ci gaba da zama da salama, Allah na salama zai kasance tare da mu. Yadda muke bi da ’yan’uwa masu bi yana shafar dangantakarmu da Jehovah kai tsaye. Ta yaya za mu tabbatar da kanmu mu masu neman salama ne? Ga wani misali.

11 Menene za ka yi idan ka ji ka yi wa dan’uwa mai bi laifi? Yesu ya ce: “Idan fa kana cikin mika baiwarka a wurin bagadi, can ka tuna dan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baiwarka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da dan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka mika baiwarka.” (Matta 5:23, 24) Za ka yi amfani da wannan gargadi ta wajen daukan zarafi ka je wajen dan’uwanka. Da wane nufi? Don ka “sulhunta” da shi. * Domin ka yi haka, kana bukatar ka fahimci, kar ka musanci, fushinsa ba. Idan ka dumfare shi da nufin sulhuntawa kuma ka rike wannan hali, hakika dukan wani rashin fahimta za a warware shi, ba da hakuri yadda ya dace, kuma a yi gafara. Sa’ad da ka dauki zarafin ka sulhunta, kana nuna cewa hikima ta Allah ce take ja-gorarka.

“Mai-Saukin Hali, Mai-Siyasa”

12, 13. (a) Mecece ma’anar furcin da aka fassara “mai-saukin hali” a Yakub 3:17? (b) Ta yaya za mu nuna cewa muna nuna yin la’akari?

12 “Mai-saukin hali.” Me yake nufi a kasance da saukin hali? In ji wani manazarci, kalmar Helenanci ta asali da aka fassara ta, “mai-saukin hali” a Yakub 3:17 tana da wuyar fassara. Masu fassara sun yi amfani da kalmomi kamar su “mai kamewa,” “mai hakuri,” da kuma “mai la’akari.” Hasiya a New World Translation ta nuna cewa ma’anarta ta zahiri “mai yarda” ne. Ta yaya za mu nuna cewa wannan bangaren hikima daga bisa tana aiki a cikinmu?

13 “Ku bari jimrewarku ta sanu ga dukan mutane,” in ji Filibbiyawa 4:5. Wata fassara ta ce: “Ku kasance a san ku da yin la’akari.” (The New Testament in Modern English, na J. B. Phillips) Ka lura cewa ba batun yaya muke ganin kanmu ba ne; amma batun yaya wasu suke ganinmu, da yadda aka san mu ne. Mutum mai la’akari ba ya nace wa kalmomin doka ko da yaushe ko kuma ga nasa ra’ayi. Maimakon haka, yana shirye ya saurari wasu, sa’ad da haka ta dace, ya yarda da muradinsu. Kuma yana da kamewa, ba mai tsanantawa ba, a sha’aninsa da wasu. Ko da yake wannan yana da muhimmanci ga dukan Kiristoci, yana da muhimmanci musamman ga dattawa. Kamewa yana jawo mutane, kuma ya sa dattawa su kasance a iya zuwa gare su. (1 Tassalunikawa 2:7, 8) Dukanmu ya kamata mu tambayi kanmu, ‘An san ni da yin la’akari, mai yarda, kuma mai kamewa kuwa?’

14. Ta yaya za mu nuna cewa mu ‘masu biyayya’ ne?

14 “Mai-siyasa.” Kalmar Helenanci da aka fassara “mai-siyasa” ta bayyana a wani wuri a cikin Nassosin Helenanci na Kiristoci. In ji wani manazarci, wannan kalmar “sau da yawa ana amfani da ita a horon soja.” Tana dauke da ma’anar “saukin rinjaya” da kuma “mika kai.” Wanda hikima daga bisa take ja-gorarsa zai mika kai ga abin da Nassosi suka ce babu jayayya. Ba za a san shi ba cewa ba ya canja shawararsa ko gaskiya ta rinjaye shi. Maimako, zai yi canji da sauri sa’ad da aka nuna masa tabbaci daga Nassosi cewa ya yi kuskure ko kuma ya tsai da shawarar da ba daidai ba. Haka ne wasu suka san ka?

“Cike da Jinkai da Kyawawan ’Ya’ya”

15. Menene jinkai, kuma me ya sa ya dace da aka yi amfani da “jinkai” da kuma “kyawawan ’ya’ya” tare a Yakub 3:17?

15 “Cike da jinkai da kyawawan ’ya’ya.” * Jinkai bangare ne mai muhimmanci na hikima daga bisa, domin iri wannan hikima an ce tana “cike da jinkai.” Ka lura cewa “jinkai” da “kyawawan ’ya’ya” an fade su tare. Wannan ya dace domin a Littafi Mai Tsarki, jinkai sau da yawa yana nufin damuwa da wasu, tausayi da yake ba da ’ya’ya da yawa na ayyukan kirki. Wani littafin neman bayani ya ba da ma’anar jinkai da cewa “jin zafin mummunan yanayi na wani ne, kuma da yin kokari a yi wani abu a kai.” Saboda haka, hikima ta Allah ba marar dadada rai ba ce, marar tausayi, ko kuma cike kawai da ilimi. Maimakon haka, tana dadada rai, tana da tausayi, kuma tana da saurin damuwa. Ta yaya za mu nuna muna cike da jinkai?

16, 17. (a) Kari ga kaunar Allah, menene yake motsa mu mu yi wa wasu wa’azi, kuma me ya sa? (b) A wadanne hanyoyi ne za mu nuna cewa muna cike da jinkai?

16 Hakika hanya mafi kyau ita ce ta wajen gaya wa wasu bisharar Mulkin Allah. Menene yake motsa mu mu yi wannan aiki? Ainihi, kaunar Allah ce. Jinkai ko kuma tausayin wasu ma yakan motsa mu. (Matta 22:37-39) Da yawa a yau “suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Matta 9:36) Makiyaya na addinin karya sun yasar da su kuma sun makantar da su a ruhaniya. Saboda haka, ba su da ja-gora ta hikima da take cikin Kalmar Allah ko kuma albarkar da Mulkin zai kawo ba da dadewa. Sa’ad da muke yin bimbini bisa bukatu na ruhaniya na wadanda suka kewaye mu, tausayinmu daga zuciya sai ya motsa mu mu yi dukan abin da za mu iya mu gaya musu game da nufi na kauna na Jehovah.

Sa’ad da muka nuna jinkai, ko tausayi ga wasu, muna nuna “hikima da take fitowa daga bisa”

17 A wadanne hanyoyi ne kuma za mu nuna cewa muna cike da jinkai? Ka tuna misali na Yesu na Basamariye wanda ya iske matafiyi yana kwance a gefen hanya, an yi masa fashi kuma an buge shi. Tausayi ta motsa shi, Basamariyen ya ‘nuna masa jinkai,’ ya daddaure raunuka na mutumin. (Luka 10:29-37) Wannan bai nuna cewa jinkai ya kunshi ba da taimako ba, ga wadanda suke da bukata? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana “mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba wadanda suke cikin iyalin imani ba.” (Galatiyawa 6:10) Ka bincika wasu yanayi masu yiwuwa. Wani dan’uwa da ya tsufa zai bukaci taimako na zuwa da dawowa daga taro na Kirista. Watakila gwauruwa a cikin ikilisiya za ta bukaci taimako na wasu gyara a gidanta. (Yakub 1:27) Wanda ya karaya zai bukaci ‘magana mai dadi’ don ya wartsake shi. (Misalai 12:25) Sa’ad da muka nuna jinkai a irin wadannan hanyoyi, muna ba da tabbacin cewa hikima daga bisa tana aiki a cikinmu.

“Mara-Kokanto, Mara-Riya Ce”

18. Idan hikima daga bisa take yi mana ja-gora, menene dole mu kawar daga zuciyarmu, kuma me ya sa?

18 “Mara-kokanto, mara-riya ce.” Hikima ta Allah ta wuce kokanto da kuma fahariya ta kasa. Idan wannan hikima tana yi mana ja-gora, mu yi kokari mu kawar da son zuciya daga zuciyarmu. (Yakub 2:9) Ba za mu daukaka wasu ba domin iliminsu, arzikinsu, ko kuma hakkinsu cikin ikilisiya; ko kuma mu raina wani cikin ’yan’uwanmu masu bi, ko yaya kaskantar su ya kasance. Idan Jehovah ya ba wadannan kaunarsa, ya kamata mu ga sun cancanci kaunarmu.

19, 20. (a) Menene tushen kalmar Helenanci na “riya”? (b) Ta yaya za mu nuna “sahihiyar kauna,” kuma me ya sa wannan yake da muhimmanci?

19 “Mara-riya ce.” Kalmar Helenanci ta “riya” tana iya nufin “mai wasan kwaikwayo wanda yake wasa.” A zamanin dā, masu wasan kwaikwayo na Helenawa da Romawa suna saka abin rufe fuska sa’an da suke wasa. Saboda haka, kalmar Helenanci “riya” ana amfani da ita ga wanda yake ayyukan karya. Wannan bangaren hikima ta Allah ya kamata ya rinjayi ba kawai yadda za mu bi da ’yan’uwa masu bi ba amma kuma yadda muke ji game da su.

20 Manzo Bitrus ya lura cewa ‘biyayyarmu ga gaskiya’ ya kamata ta kasance a “sahihiyar kauna ta ’yan’uwa.” (1 Bitrus 1:22) Hakika, kaunarmu ga ’yan’uwanmu dole ne ta kasance ba sama sama ba kawai. Kada mu zama abin rufe fuska ko kuma mu yi abubuwa kawai domin mu rudi wasu. Kaunarmu dole ta zama sahihiya, daga zuciya. Idan haka take, ’yan’uwanmu masu bi za su yarda da mu, domin sun sani cewa muna nan yadda muke. Irin wannan gaskiya tana shirya hanyar dangantaka ta gaskiya tsakanin Kiristoci kuma tana taimakawa wajen kawo yarda a cikin ikilisiya.

“Ka Kiyaye Sahihiyar hikima”

21, 22. (a) Ta yaya Sulemanu ya kasa kiyaye hikima? (b) Ta yaya za mu kiyaye hikima, kuma ta yaya za mu amfana daga yin haka?

21 Hikima ta Allah kyauta ce daga wajen Jehovah, wadda ya kamata mu kiyaye. Sulemanu ya ce: “Dana, . . . ka kiyaye sahihiyar hikima da hankali kuma.” (Misalai 3:21) Abin bakin ciki, Sulemanu kansa bai yi haka ba. Zai kasance mai hikima muddin ya ci gaba da zuciya mai biyayya. Amma a karshe, matansa baki da yawa suka juya zuciyarsa daga bautar Jehovah. (1 Sarakuna 11:1-8) Karshen Sulemanu ya nuna cewa ilimi amfaninsa kadan ne idan ba mu yi amfani da kyau da shi ba.

22 Ta yaya za mu kiyaye sahihiyar hikima? Ba kawai ya kamata mu karanta Littafi Mai Tsarki ba a kai a kai da kuma littattafai na Littafi Mai Tsarki da “bawan nan, mai-aminci, mai-hikima” yake tanadinsa, amma kuma dole ne mu yi kokarin yin amfani da abin da muka koya. (Matta 24:45) Muna da dalili da yawa na yin amfani da hikima ta Allah. Tana nufin rayuwa mafi kyau a yanzu. Tana taimakonmu mu “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai”—rayuwa a sabuwar duniya ta Allah. (1 Timothawus 6:19) Kuma mafi muhimmanci ma, koyon hikima da take fitowa daga bisa za ta matso da mu kusa da tushen dukan hikima, Jehovah Allah.

^ sakin layi na 1 In ji 1 Sarakuna 3:16, mata biyun karuwai ne. Insight on the Scriptures ya ce: “Wadannan matan karuwai ne, ba kamar kilakawa ba, amma mata ne da suka yi fasikanci, ko matan Yahudawa, ko kuma watakila, mata baki.”—Shaidun Jehovah ne suka buga.

^ sakin layi na 11 Furcin Helenanci da aka fassara “ku sulhuntu” ya zo ne daga kalmar aikatau da take nufin “ ‘gyara abin da ya lalace, a canja,’ saboda haka, ‘a sulhunta.’ ” Domin burinka ka kawo canji ne, ka cire, idan zai yiwu, fushi daga zuciyar da aka yi wa laifi.—Romawa 12:18.

^ sakin layi na 15 Wata fassara ta fassara wadannan kalmomi “cike da tausayi da kuma nagarin ayyuka.”—A Translation in the Language of the People, na Charles B. Williams.