Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 23

“Ya Fara Kaunace Mu”

“Ya Fara Kaunace Mu”

1-3. Waɗanne yanayi ne suka mai da mutuwar Yesu ba kamar wasu ba a tarihi?

A WATA rana a kaka kusan shekara 2,000 da ta shige, an yi wa wani mutum marar laifi hukunci, aka kama shi da laifin da bai yi ba, sai kuma aka gana masa azaba har ya mutu. Ba shi ne mugun kisa na rashin gaskiya na farko ba a tarihi; kuma abin baƙin ciki, ba shi ne zai kasance na ƙarshe ba. Amma, mutuwarsa ba kamar ta wasu ba ce.

2 Yayin da mutumin ya wahala cikin awoyin azaba na ƙarshe, sama kanta ta nuna cewa wannan aukuwar tana da muhimmanci. Ko da yake da tsakar rana ce, farat ɗaya duhu ya rufe ƙasar. In ji wani ɗan tarihi, “an ɗauke rana.” (Luka 23:44, 45) Kafin ya numfasa numfashinsa na ƙarshe, ya faɗi waɗannan kalmomi da ba za a taɓa manta da su ba: “Ya ƙare”! Hakika, ta wajen ba da ransa, ya cika wani abu mai ban mamaki. Hadayarsa ita ce nuna ƙauna mafi girma da mutum ya taɓa yi.—Yohanna 15:13; 19:30.

3 Wannan mutumin, hakika, Yesu Kristi ne. Azabarsa da kuma mutuwa a wannan rana mai duhu, ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z., sananniya ce ƙwarai. Amma, sau da yawa ana ƙyale wata gaskiya mai muhimmanci. Ko da yake Yesu ya wahala ƙwarai, wani ya wahala ma fiye da haka. Hakika, wani ya ba da hadaya wadda ta fi ma a wannan ranar—nuna ƙauna mafi girma da aka taɓa yi a cikin dukan sararin samaniya. Wane hali ke nan wannan? Amsar ta ba da gabatarwa ga batu mafi muhimmanci: ƙaunar Jehovah.

Nuna Ƙauna Mafi Girma

4. Ta yaya wani sojan Roma ya ga cewa Yesu ba mutum ba ne kawai, kuma menene wannan sojan ya ce?

4 Wani sojan Roma da ya ja-goranci kashe Yesu ya yi mamaki domin duhu da kuma girgizar ƙasa da suka biyo bayan mutuwar Yesu. “Hakika wannan Ɗan Allah ne,” in ji shi. (Matta 27:54) Babu shakka, Yesu ba mutum ba ne kawai. Sojan ya taimaka a kashe Ɗa makaɗaici na Allah Maɗaukaki! Yaya tamanin wannan Ɗa wurin Ubansa?

5. Ta yaya za a iya kwatanta yawan lokaci da Jehovah da Ɗansa suke a sama tare?

5 Littafi Mai Tsarki ya kira Yesu “ɗan fari ne gaban dukan halitta.” (Kolossiyawa 1:15) Ka yi tunani—Ɗan Jehovah yana raye kafin a halicci duniya ta zahiri. To, tun yaushe Uba da Ɗan suke tare? Wasu masana kimiyya suka kimanta cewa sararin samaniya tana da shekaru biliyan 13. Kana iya ma nuna yawan wannan lokacin? Don a taimaki mutane su fahimci shekarun sararin samaniya yadda ’yan kimiyya suka kimanta, wata na’ura ta zana taswirar lokaci mai tsawon ƙafa 360. Yayin da baƙi suke tafiya a wajen wannan taswira, dukan taku da suka yi yana wakiltan shekaru miliyan 75 na rayuwar sararin samaniya. A ƙarshen taswirar ta lokaci, maki guda ne mai ƙibar gashi ƙwaya ɗaya take wakiltar dukan tarihin ’yan Adam! Duk da haka, ko idan wannan kimantawar daidai ce, dukan taswirar lokacin ba za ta iya wakiltan tsawon rayuwar Ɗan Jehovah ba! Wane aiki yake yi a dukan tsawon wannan lokaci?

6. (a) Menene Ɗan Jehovah yake yi a lokacin rayuwarsa kafin ya zo duniya? (b) Wace irin nasaba ce ta kasance tsakanin Jehovah da Ɗansa?

6 Ɗan ya yi farin cikin zama “gwanin mai-aiki” na Ubansa. (Misalai 8:30) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba a yi kome ba cikin abin da an yi, sai ta wurin [Ɗan].” (Yohanna 1:3) Saboda haka, Jehovah da Ɗansa suka yi aiki tare suka halicci dukan wasu abubuwa. Hakika sun kasance tare cikin farin ciki! Babu shakka, mutane da yawa za su yarda cewa ƙauna tsakanin iyaye da yara tana da ƙarfi ƙwarai. Kuma ƙauna “ita ce magamin kamilta.” (Kolossiyawa 3:14) Saboda haka, waye a tsakaninmu zai fara gwada ƙarfin gami da ya kasance tsakaninsu a cikin wannan lokaci mai yawa sosai? Babu shakka, Jehovah Allah da Ɗansa sun nasabtu cikin gami mafi ƙarfi da ya taɓa faruwa.

7. Sa’ad da Yesu ya yi baftisma, yaya Jehovah ya furta yadda yake ji game da Ɗansa?

7 Duk da haka, Uban ya aiko Ɗansa zuwa duniya a haife shi jariri ɗan mutum. Yin haka na wasu shekaru yana nufin Jehovah dole ya mance da hulɗa ta kurkusa da Ɗansa da yake ƙauna a sama. Da ƙauna mai yawa, Ya lura daga sama yayin da Yesu yake girma ya zama cikakken mutum. Sa’ad da yake kimanin shekara 30 da haihuwa, Yesu ya yi baftisma. Ba sai mun yi zaton yadda Jehovah ya ji ba. Uban ya yi magana da kansa daga sama: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai.” (Matta 3:17) Tun da Yesu ya yi dukan abin da aka riga aka annabta, dukan abin da aka umurce shi, Ubansa ya yi farin ciki sosai!—Yohanna 5:36; 17:4.

8, 9. (a) Menene aka yi wa Yesu a ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z., kuma yaya wannan ya shafi Ubansa a samaniya? (b) Me ya sa Jehovah ya ƙyale Ɗansa ya wahala kuma ya mutu?

8 Amma, yadda Jehovah ya ji a ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z. fa? Yaya ya ji sa’ad da aka ci amanar Yesu kuma taron mutane suka kama shi daddare? Abokanan Yesu suka guje shi kuma aka yi masa hukunci marar gaskiya? Da aka yi masa ba’a, aka tufa masa yawu, kuma aka naushe shi? Da aka yi masa bulala, bayansa ya tsatsage? Da aka buga masa ƙusa hannu da ƙafa, bisa dogon gungume aka rataye shi sa’ilin da mutane suke zaginsa? Yaya Uban ya ji yayin da Ɗansa da yake ƙauna ya yi kuka domin ƙunar azaba? Yaya Jehovah ya ji yayin da Yesu ya numfasa numfashi na ƙarshe, kuma lokaci na farko tun daga farkon halitta da Ɗan ba ya raye?—Matta 26:14-16, 46, 47, 56, 59, 67; 27:38-44, 46; Yohanna 19:1.

“Allah . . . ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai”

9 Ba magana. Tun da Jehovah yana da motsin rai, azaba da ya sha domin mutuwar Ɗansa ta fi ƙarfin kalma ta bayyana. Abin da za a iya yin bayani a kai shi ne dalilin da ya sa Jehovah ya ƙyale hakan ya faru. Me ya sa Uban ya ƙyale kansa ya sha irin wannan azabar? Dalilin yana rubuce cikin aya ta Littafi Mai Tsarki da aka kira ƙaramar Linjila. Yohanna 3:16 ta ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” Saboda haka, dalilin Jehovah shi ne: ƙauna. Kyauta ta Jehovah—aiko da Ɗansa ya wahala kuma ya mutu dominmu—shi ne nuni na ƙauna mafi girma da aka taɓa yi.

Ma’anar Ƙaunar Allah

10. Ɗan Adam yana da wace bukata, kuma menene ya faru da ma’anar kalmar nan “ƙauna”?

10 Mecece ma’anar wannan kalmar “ƙauna”? An ce ƙauna ita ce bukata mafi girma da ’yan Adam suke da ita. A dukan rayuwar mutum, mutane suna neman ƙauna, suna rayu saboda ita, su galabaita su mutu saboda rashinta. Abin mamaki, tana da wuyar ma’ana. Hakika, mutane suna yawan magana a kanta. Da akwai littattafai, waƙoƙi rubutattu da na baƙa game da ita a kai a kai. Sakamakon ba ko yaushe yake bayyana ma’anar ƙauna ba. Hakika, kalmar an fiye amfani da ita har ma’anarta ta kasance da wuya.

11, 12. (a) A ina za mu koyi abubuwa da yawa game da ƙauna, kuma me ya sa a nan ne? (b) Waɗanne irin ƙauna ne aka bayyana a cikin harshe na dā na Helenanci, kuma wace kalma ce ta ƙauna aka yi amfani da ita sau da yawa a cikin Nassosin Helenanci na Kirista? (Ka kuma ga hasiya.) (c) Mecece a·gaʹpe?

11 Amma, Littafi Mai Tsarki ya koyar da bayani game da ƙauna. Expository Dictionary of New Testament Words na Vine ya lura: “Za a san ƙauna daga aikin da ta motsa ne kawai.” Tarihin Littafi Mai Tsarki game da ayyukan Jehovah ya koyar da mu sosai game da ƙaunarsa—nagarin so da yake da shi ga halittunsa. Alal misali, menene zai bayyana game da wannan halin sosai idan ba nuna ƙauna mai zurfi na Jehovah ba da aka kwatanta a baya? A babobi da za su biyo baya, za mu ga wasu misalai masu yawa na ƙaunar Jehovah. Bugu da ƙari, za mu samu fahimi daga asalin kalma ta “ƙauna” da aka yi amfani da ita cikin Littafi Mai Tsarki. A harshen dā na Helenanci, da akwai kalmomi huɗu na “ƙauna.” * Tsakanin waɗannan, wadda aka fi amfani da ita a cikin Nassosin Helenanci na Kiristoci ita ce a·gaʹpe. Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya kira ta “kalma mafi ƙarfi na ƙauna da za a taɓa tunaninta.” Me ya sa?

12 A·gaʹpe tana nufin ƙauna da mizani yake yi mata ja-gora. Saboda haka, ta fice sakamako na motsin rai ga abin da wani ya ce ko ya yi. Ta fi faɗi a ma’anarta, ta fi tunani da sani a tushenta. Fiye da kome, a·gaʹpe ba ta da son kai. Alal misali, ka sake duba Yohanna 3:16. Wacce ce “duniya” da Allah yake ƙauna sarai da har ya ba da Ɗansa makaɗaici? Duniya ce ta mutane da za a iya cetonsu. Wannan ya haɗa da mutane da yawa da suke bin tafarkin zunubi. Jehovah yana ƙaunar kowanne kamar abokinsa, kamar yadda ya ƙaunaci mai aminci Ibrahim? (Yaƙub 2:23) A’a, amma cikin ƙauna Jehovah ya yi wa duka kirki, babban hasara ga kansa. Yana son kowa ya tuba kuma ya canja tafarkinsa. (2 Bitrus 3:9) Mutane da yawa sun yi haka. Waɗannan ya karɓe su da farin ciki a matsayin abokansa.

13, 14. Menene ya nuna cewa a·gaʹpe sau da yawa tana haɗe da soyayya?

13 Duk da haka, wasu suna da mummunan ra’ayi game da a·gaʹpe. Suna tunanin cewa tana nufin ƙauna ce marar himma, irinta ilimi. Amma a hakikanin gaskiya a·gaʹpe sau da yawa ta haɗa da soyayya mai kyau. Alal misali, sa’ad da Yesu ya ce, “Uban yana ƙaunar Ɗan,” an yi amfani da wata irin kalmar a·gaʹpe. Wannan ƙaunar ba ta da soyayya ce? Ka lura cewa Yesu kuma ya ce, “Uban yana ƙaunar Ɗan,” an yi amfani da wata irin kalmar phi·leʹo. (Yohanna 3:35; 5:20) Ƙaunar Jehovah sau da yawa tana haɗe da soyayya. Duk da haka, ƙauna motsin rai ba ya taɓa rinjayarta. Ko da yaushe mizaninsa na hikima da adalci ne yake yi mata ja-gora.

14 Kamar yadda muka gani, dukan halayen Jehovah masu kyau ne, kamilai, masu ban sha’awa. Amma ƙauna ta fi duka ban sha’awa. Babu abin da yake sa mu matsa kusa da Jehovah haka. Abin farin ciki, ƙauna ita ce halinsa mafi yawa. Ta yaya muka san da haka?

“Allah Ƙauna Ne”

15. Wane furci Littafi Mai Tsarki ya yi game da halin Jehovah na ƙauna, kuma a wace hanya ce wannan furci ya kasance farda? (Duba kuma hasiya.)

15 Littafi Mai tsarki ya faɗi wani abu game da ƙauna da ba a taɓa faɗa ba game da wasu shahararrun halaye na Jehovah. Nassosi ba su ce Allah iko ba ne ko kuma cewa Allah shari’a ko kuma ma su ce Allah hikima ne. Yana da waɗannan halaye, shi ne tushen waɗannan, kuma ba shi da na biyu a dukan waɗannan uku. Amma game da hali na huɗun, an faɗi wani abu mafi zurfi: “Allah ƙauna ne.” * (1 Yohanna 4:8) Menene wannan yake nufi?

16-18. (a) Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ƙauna ne”? (b) A dukan halittun da suke duniya me ya sa mutum ne alama da ta dace na halin Jehovah na ƙauna?

16 “Allah ƙauna ne” ba abu ba ne mai sauƙi, kamar a ce, “Allah ya yi daidai da ƙauna.” Ba zai dace ba kuma mu juya furcin mu ce “ƙauna Allah ne.” Jehovah ya wuce hali da ba a gani. Shi wani ne mai motsin rai dabam dabam da kuma halaye ƙari ga ƙauna. Ƙauna ce ta cika Jehovah. Saboda haka wani littafin neman bayani ya ce game da ayar: “Ainihin Allah ko kuma yanayinsa ƙauna ne.” Za mu iya tunaninsa a wannan hanyar: Ikon Jehovah yana sa shi ya yi abu. Shari’arsa da hikima suna ja-gorarsa a hanyar da yake aikata abubuwa. Amma ƙaunar Jehovah take motsa shi ya yi abu. Kuma ƙaunarsa tana kasancewa a cikin dukan hanyar da ya yi amfani da wasu halayensa.

17 Sau da yawa ana cewa Jehovah shi ne ƙauna aini. Saboda haka, idan muna so mu koyi game da ƙauna ta ƙa’ida, dole ne mu koyi game da Jehovah. Hakika, za mu ga wannan kyakkyawan hali a mutane ma. Amma me ya sa akwai shi? A lokacin halitta, Jehovah ya yi wannan maganar, a bayyane, ga Ɗansa ne: “Bari mu yi mutum a cikin surarmu, bisa ga kamaninmu.” (Farawa 1:26) A dukan halittu da suke cikin duniya, maza ne da mata kawai za su iya zaɓa su ƙaunaci Ubansu na samaniya kuma su yi koyi da shi. Ka tuna cewa Jehovah ya yi amfani da halittu dabam dabam ya alamta halayensa na musamman. Duk da haka, Jehovah ya zaɓi wannan halitta mafi matsayi na duniya, mutum, ya alamta Halinsa mafi girma, ƙauna.—Ezekiel 1:10.

18 Sa’ad da muka yi ƙauna a hanya marar son kai, na ƙa’ida, muna nuna hali mafi girma na Jehovah ne. Kamar yadda manzo Yohanna ya rubuta ne: “Muna ƙauna, domin ya fara ƙaunace mu.” (1 Yohanna 4:19) Amma a waɗanne hanyoyi ne Jehovah ya ƙaunace mu da farko?

Jehovah Ya Ɗauki Mataki

19. Me ya sa za a ce ƙauna muhimmiya ce a aikin halitta na Jehovah?

19 Ƙauna ba sabuwar aba ba ce. To, menene ya motsa Jehovah ya fara halitta? Ba domin kewa ba ne saboda haka ya nemi abokin zama ba. Jehovah cikakke ne kuma mai wadatar zuci, bai rasa kome ba da wani zai ba shi. Amma ƙaunarsa, hali mai ƙarfi, ya motsa shi ya so ya more rayuwa da halittu masu hankali waɗanda za su yi godiya ga irin wannan kyautar. “Farkon halittar Allah,” shi ne Ɗansa makaɗaici. (Ru’ya ta Yohanna 3:14) Sai Jehovah ya yi amfani da gwanin aikinsa ya sa wasu abubuwa suka wanzu, na farko mala’iku. (Ayuba 38:4, 7; Kolossiyawa 1:16) An albarkace su da ’yanci, fahimi, da kuma motsin rai, waɗannan manyan ruhohi suna da zarafin kafa dangantaka tasu da junansu—da wasu, fiye da haka kuma, da Jehovah Allah. (2 Korinthiyawa 3:17) Saboda haka, sun yi ƙauna domin an ƙaunace su ne da farko.

20, 21. Adamu da Hauwa’u suna da wane tabbaci cewa Jehovah yana ƙaunarsu, duk da haka, menene suka yi?

20 Haka yake da ’yan Adam ma. Da farko, Adamu da Hauwa’u suna cike da ƙauna. Dukan inda suka juya a cikin gidansu Aljanna a Adnin, suna ganin tabbacin ƙaunar Ubansu. Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji Allah kuma ya dasa gona daga wajen gabas, a cikin Adnin; can kuwa ya sanya mutumin da ya sifanta.” (Farawa 2:8) Ka taɓa zuwa lambu wanda yake da kyaun gaske? Menene ya faranta maka rai ƙwarai? Haske da yake zuwa daga bayan ganyaye? Launi dabam dabam na furanni? Kukan tsuntsaye da kuma ƙarar ƙwari? Yaya kuma ƙamshin itatuwa, ’ya’yan itatuwa, da kuma furanni? Ko yaya dai, babu wani lambu da za a gwada da na Adnin. Me ya sa?

21 Wancan lambun Jehovah ne kansa ya kafa shi! Dole ne ya kasance marar kwatanci domin kyaunsa. Dukan itace mai ban sha’awa don kyau ko kuma mai ɗanɗano ya kasance a wurin. Lambun yana samun ban ruwa da kyau, yana da fili, kuma yana cike da dabbobi iri dabam dabam. Adamu da Hauwa’u suna da dukan abin da zai sa rayuwarsu ta kasance da farin ciki da kuma gamsuwa, haɗe da aiki mai gamsarwa da kuma abokin zama kamiltacciya. Jehovah ya ƙaunace su da farko, kuma suna da dalilai masu yawa su yi ƙaunarsa. Amma sun kasa yin haka. Maimakon su yi biyayya da Ubansa na samaniya cikin ƙauna, suka yi masa tawaye domin son kai.—Farawa, sura 2.

22. Ta yaya yadda Jehovah ya aikata ga tawaye na Adnin ya ba da tabbacin cewa ‘ƙaunarsa ba ta ƙarewa’?

22 Lalle wannan zai yi wa Jehovah ciwo! Amma wannan tawayen ya ɓata zuciyarsa mai ƙauna ne? A’a! “Jinƙansa [ko kuma “ƙauna ta aminci,” hasiya] har abada ne.” (Zabura 136:1) Saboda haka, babu ɓata lokaci ya ƙudura ya yi tanadi cikin ƙauna ya ceci ’ya’yan Adamu da Hauwa’u masu zuciyar kirki. Kamar yadda muka gani, waɗannan tanadin sun haɗa da hadaya ta fansa na Ɗansa wanda yake ƙauna, wanda ya shafi Ubansa ƙwarai.—1 Yohanna 4:10.

23. Menene dalili ɗaya da ya sa Jehovah ‘Allah ne mai farin ciki,’ kuma wace tambaya ce mai muhimmanci za a bincika a babi na gaba?

23 Hakika, daga farko Jehovah ya ɗauki mataki ya nuna ƙauna ga mutane. A hanyoyi marasa iyaka, ‘ya ƙaunace mu da farko.’ Ƙauna tana ɗaukaka jituwa da farin ciki, saboda haka ba abin mamaki ba ne da aka kwatanta Jehovah da cewa ‘Allah mai farin ciki.’ (1 Timothawus 1:11) Amma, tambaya mai muhimmanci ta taso. Jehovah yana ƙaunar kowannenmu ne? Babi na gaba zai bincika wannan batun.

^ sakin layi na 11 Kalmar aikatau phi·leʹo, mai nufin “ka so wani, ka yi muradin wani, ka so (kamar yadda wani zai ji game da aboki na kud da kud ko kuma ɗan’uwa),” an yi amfani da ita sau da yawa a cikin Nassosin Helenanci na Kiristoci. ’Yar’uwar kalmar stor·geʹ, ko kuma ƙauna ta iyali, an yi amfani da ita a 2 Timothawus 3:3 na nuna cewa irin wannan ƙaunar ba za ta kasance ba a kwanaki na ƙarshe. Eʹros, ƙauna ta soyayya tsakanin jinsi, ba a yi amfani da ita ba cikin Nassosin Helenanci na Kirista, ko da yake irin wannan ƙauna an yi maganar ta cikin Littafi Mai tsarki.—Misalai 5:15-20.

^ sakin layi na 15 Furci biyu na Nassi suna da irin tsari ɗaya: “Allah haske ne” da “Allah . . . wuta ne.” (1 Yohanna 1:5; Ibraniyawa 12:29) Amma waɗannan dole ne a fahimce su kwalliya ce ta magana, domin sun kamanta Jehovah da abubuwa na zahiri. Jehovah kamar haske yake, domin shi mai tsarki ne kuma mai adalci. Babu “duhu,” ko ƙazanta, a gare shi. Kuma za a kwatanta shi da wuta domin amfani da ikonsa na halaka.